← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 63

Sashe 1

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal


Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 1 part 1
ZURFIN CIKI book 1 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 02:16
UUmmi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu
hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata
tafiya a hankali.daga can gefe ta hango wata
yarinya wadda bazata wuce sa'arta ba.
tace,"yauwa,ga firdausin data tsokane ni" ta nufi
wurinta ,tasha gabanta ta rike kugu.

"fiddausi wa
kike tsokana? fiddausi tace "ban tsokane ki ba
fa".cikin tsoro tayi maganar .ummi ta shako mata
wuya. ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga.ban
ce ba inji fiddausi .ummi ta hankada ta tare da
cewa "Allah yaso ki." nikan garin da fiddausin tayi
ya tarwatse a kasa tace "kin gani ko? wallahi sai
kin biyani"ta soma kuka,ummi ta sheka da
gudu,sai gida. tana ajiye man gyadan data siyo ta
nufi ba daki don fitsari ya matse ta .umma dake
zaune tana fadin.

"da mutum!da mutum!!" saida
ummi ta bude .

Ganin yaya Abba tayi,da gudu ta
juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi
bol da dakakken yajin da umma ta daka zata
soya mai don cin abincin rana. sai kuma ta tuna
cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai binciko ta.ta
fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa. tsohuwar tana
sallar azahar.ummi ta tsallake ta ta kutsa kasan
gado.nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson
sha da zarar ta idar da sallah.

Alhaji babba tasa
ya aiko mata da furar daga kasuwa.don tasha da
rana.

Abba ya fito wanka ranshi a bace.dakin
umma ya nufa yana fadin "ummi ke ummi zonan"
Ya samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta
zubar, tana fada.

Ya ce, "Umma ban san irin
dukan da zan wa Ummi ba yau.

Ta ce,"Abba ka
mata dukan mutuwa, na gaji da halin Ummi.

Yarinya sai ka ce 'yar fata?

Ka dubata ta tafi
dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a dake ta."
Ya ce,"Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta,
amma ba zan barta ba.

Ya juya zai tafi, suka ji
muryar Tsohuwa tana fadin.

Ba zan yi fada ba, ka
kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka
barta da rai.

Ta dubi Umma" ke kuma Suwaiba
dama kin san ba za ki daraja sunana ba ki ka sa
a ka sa miki don kiji dadin ci min fuska?" Umma
ta ce," Ba haka ba ne Tsohuwa, Ummi ba ta yo
halinki ba.

Ita fa rashin hankali ne da ita.

Yayanta
fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta
zubar min da barkono.

Abba ya ce, "Umma don
Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta
6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta
hana a yi mata fada.

Uhm duk fadanki yau sai na
dake ta, ba sunan ki ba in ma kece,"Tsohuwa
tasa kuka gami da salati.

"Yanzu mai sunan
Malam ni ka ke fadawa haka?" ya ce, "An fada
miki." Umma ta ce, "kai Abba zan sa6a maka
jeka." Ta juyo wurin Tsohuwa, Don Allah kiyi
hakuri...............

Maman Fiddausi ce tayi sallama
tare da Fiddausin suka shigo.

Ran Maman
Fiddausin a 6ace, ta tsaya rike da gari a
hannunta ta dubi Umma.

Ta ce, Umman Abba
dubi abn da Umminki tayi min don Allah, yarinyar
nan tayo nika da kyar," tun safe sai yanzu na
samu, amma ta zubar min." Abba ya ce, Kinga
halinta ko?" Tsohuwa ta ce, "Wannan ba matar
Bala ba ce?" Maman Fiddausi ta ce, "Ni ce." Ta
ce," To kije kije ki nemi wanda ya zubar da
garinki, Ummi ko fita ba tayi ba.

Umma ta ce, "
Ta fita Tsohuwa, na aike ta siyan mai." Tsohuwa
ta ce," Tsokanarta a ka yi to.

Umma ta amshe
abin garin ta zuba musu, sannan ta ce, "Don
Allah Tine kiyi hkr." Abba ya nufi daki.

Sai da ya
shirya tsaf, sannan ya dauki belt ya nufi cikin
gida, dakin Tsohuwa ya shiga kai-tsaye kasan
gado ya nufa.

Ya jawo ta, ta soma kurma ihu.

Daya ya lafta mata amma ta dane shi tare da
cukwikuye belt din tana ihu.

Tsohuwa ta iso tana
dukanshi a baya, fadi take "Za ka kasheta ne?

Jama"a kuyo dauki.

Haushin hakan yasa shi
damko kanta ya shiga zuba mata kola, ya
sirmiyota ya shiga lafta da takalminshi, tunda ta
hana belt din.

Sai da ya mata tas, sannan ya fita
ya bar su, Tsohuwa na kuka Ummi na kuka. , Sai
da komai ya natsa ta leka ta jawo furarta don
tasha, sai ta ganta a zube.

Ta ce, A" a ke ki ka
zubar min da fura?" Ummi ta ce, To ba shi ne
janyo ni ba Yaa Abban.

Tsohuwa ta ce, "Ai ko sai
ya siyo min furata.

Ta mike ta wuce Umma tana
rabon abinci, ta nufi soro in da dakin Abba yake
(Zaure) Ya fito yana rufe kofa, ta ce "Au za ka
fita ba?

To ka sawo min furata da ka zubar.

Ko
kallonta bai yi ba ya rufe kofarshi ya wuce.

Ta ce
mishi "Aikin bana, in ba siyo min ba ubanka ai ya
dawo ko min dare ya sito min.

Abba ya ce, Ku ku
ka sani.

Ra ce, kaima ka sani, dan jakar uba.

Ta
dawo ciki tana mitar ya cika bakin rai.

Umma ta
ce, "Ina Abban?

Tsohuwa ta ce, "Ya tafi, in bai
sai min furata ba ranshi zai 6aci yau a gidannan.

Umma ta ce "Ni bai ma ci abinci ba ya fita, ke
Ummi zo ki kira min shi, yunwa fa yake ji.

Tsohuwa ta ce, "Ba za ta kira shi ba, ya dake ta
sannan ta kira shi?

Tunda bai barta taci da dadin
rai ba, shi ma ba ya ci ba.,, Umma tayi shiry,sai
haushin Ummi da take ji kamar ta shake ta ta
mutu.

Ummi tayi wanka ta zura kayan Mkrnt,
tana saka sandal Umma ta ce, "Ina Ummi?

Zo
nan." Ummi ta tafi tana cewa a ranta.

"ALLAH
YASA DAKIN YAYA ABBA ZA TA AIKE NI, SAI NA
RAMA DUKAN DA YA YI MIN JIYA, DON YANZUN
DUK ME YA MIN SAI NA RAMA.........." Umma ta
katse mata tunani da cewa,"dauki shayin Abba ki
kai masa kada yayi latti,kai shayin ki dawo ki
dauki dankalin,yau shi kadai ma nayiwa dankalin."
Tace,"nifa?"umma tace "ke kina cin dumame
Abba ko ba ya ci,dan haka dan wanda ya rage
shi nayi wa." Ummi ta figi kayan tea din ta nufi
dakin Abba tana tura baki.tare da sallama bata
jira amsa ba,ta daga labule ta fada.

Dabi'ar da
yake mata fada akai kullum,ya gama saka
singiletinshi kenan yana kokarin saka riga.

Yace,
"wai ke wace irin majanuniya ce?ban ce miki in
kinyi sallama sallama sai na amsa za ki shigo
ba? sai kawai ta saki tiren,ruwan zafin ya zube
masa a kafa,dankalin ya watse kan rigar da zai
saka. tayo waje da gudu,sai dakin tsohuwa.ya
fito da sauri yana cewa,"umma ta kona ni! ta
kona ni!!" da sauri umma ta fito daga dakin Alhaji
babba,shima Alhajin na biye da ita yana fadin
"wacece ta kona ka?" Yace "ummi ce! ummi
ce!!."nan take Alhaji babba ya rike kafar yana tofa
mishi addu'a.

Umma ta debo kullun kamu ta zuba
mishi,amma duk da haka sai da yan yatsun
kafarsa suka kumbura. tsohuwa ta fito daga daki
tana fadin,"kai ummi bata ji? wai ni meyasa aka
sa mata sunana?" Abba ya kalli tsohuwa cikin
takaici yace,"duk ba ke kike daure mata gindi ba?"
Umma ta shiga dakin tsohuwa ta janye kayan da
tsohuwa ta jera don kada aga ummi,ta janyota
tun daga dakin take kwallo da ummi har waje.

Alhaji ma yau har dashi aka zane ummi,tsohuwa
dai sai yan mitoci take yi,wai yanxu haka ma
bata sani bane.

Abba dai ranar dai bai je
makaranta ba,haka nan da yamma sai da ya saka
ummi a dakinshi ya bata gwale-gwale sannan ya
zane ta. misalin hudu da rabi na yamma,Ahmad
abokin Abba yayi sallama a kofar gidan,Abba ya
amsa ya fito.

Suna zaune kan dakalin kofar gidan
suna hira,sai ga ummi ta yanko da gudu tana
waiwayen baya.

Ya ce,"zo nan."tazo yace,"kinyo
tsokanar fada ko?" tace,"a'a.yace in har tsokana
ki kayo zaki sani shegiya mummuna kazama.

Ta
murguda baki,yasa takalmi ya jefeta,ta shige gida
sai ko ga wani yaro jiki duk kwata yayyanshi na
biye dashi. ya tambayesu,suka ce "ummi ce ta
jefa shi kwata"ya taso yaron har cikin gida ya
kamota dakin tsohuwa ya tsareta ta wanke ma
yaron jiki,ta kuma wanke kayan. sannan ya
zuzzuba mata kola a kai.tsohuwa tana ta yiwa
yaran fada,wai ita ma su daina tsokanarta Umma
ko lekowa bata yi ba,ya fito ya samu Ahmad yana
cewa "kayi hakuri na barka kai kadai." Ahmad
yace,"ba komai" sai Abba ya zauna sannan
Ahmad ya dube shi.

Abba wannan kanwar taka
kuwa bata da Aljanu?

Abba yace,"ba kowa
akanta,sai iskanci." Ahmad yace."a'a,kai dai ku
kaita ayi mata rukiyya." Abba yayi dariya,sannan
yace kasan Allah ba kowa akan ummi,saboda
Alhaji karami ya taba yin wannan tunanin. ya
dauke ta yakai ta rukiya bata da komai."Ahmad
yace tabdi!,gaskiya in ta isa aure duk wanda ya
aureta akwai aiki babba a tare dashi.

Abba ya
ce,"wane mahaukaci ne ma zaya dibar ma kansa
ummi?"Ahmad ya ce,"sai ai muku hadin ggida..."
ya kaima Ahmad naushi a gefen ciki,Ahmad ya
kauce yana masa dariya.

Abba ya ce,"ka cuce
ni,ace in auri ummi ai sai na hada kayana na bar
garin nan. nan.

Ahmad ya s heke da dariya har
da rike ciki.sannan ya ce,"don me?

Abba ya
ce,"to wannan yarinyar ba sai ta hada maka
gobara gida ba?gata kazama ga muni." Ahmad ya
ce,"kama dai kuke yi." Abba ya bata rai,"Ahmad
bana so.in har da gaske ina kamada ummi ba sai
na koma ciki an sake haifana ba.

Don Allah ni
tashi ma ka tafi,don wallahi da don kai bane kake
fada min haka da sai munyi rigima,na tsani
ummi,bana sonta sam!
Chapter 1 · 0% Book details