← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 82

Sashe 9

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta bini da kallo har na shiga dakina na taso yaran suka fito, ta kama hannunsu suka fice tare. Dakin na gyara sannan na shiga na yi wanka na fito jikina na ciwo domin ban saba aikin wahala haka ba, mai na shafa na dauki riga da skirt material na saka sannan na shiga kitchen din na dafa shayi da gass na soya kwai biyar na soya dankali na fito na zauna. Ina tsaka da ci Hafiz ya shigo falon rike da biredi ya aje min.

“Good Morning”

Na amsa da murmushi sai ya gutsuri kwain dake gabana ya ci.

“Ashe kin iya soya kwai”

Na yi murmushi, ya mayar min da murmushin sannan ya tashi ya fice. Ina gama karyawa na hau bachin wahala idona cike da kwalla indai haka auren yake ba shi da dadi ni dai a gurin, ba zan fita ba ga aiki kullum ga wahalar kyautatawa miji ko baka so... Na yi wannan tunanin na yi wacan har bachi yayi gaba da ni ban farka sai azahar shi ma saboda Aisha ta shigo har dakina ne ta tashe ni daga bachin.

“Ke bachin rana kin yi sallah ma tashi mu yi hira”

Na tashi ina murza ido, bayan na yi sallah na dawo muka zauna da ita falo tana min hira mafi yawan hallayar Hafiz take fada min marar kyau, tana kara tsorata ni akan mijinta, sai dai abun da ya bani mamaki kuma ya daure min kai shi ne yadda take zaune da shi lafiya babu wani tashin hankali sai soyyayah da kaunar juna. Ba ita ta bar bangaren ba sai biyar na yamma a lokacin ne na shiga kitchen na sarrafa shimkafa da miya da naman kaza na ci, na bar ragowar kamar yadda na kasa cinye kwan da na soya a dazun. Da dare Hafiz ya shigo ya duba ni sannan Yaransa suka shigo muka kwana tare, washe gari ma haka ya na gyara komai na yi wanka na girka shimkafa da wuri, kamin na kwanta bachin kanwarta ta shigo kirana wai yau tana son na shigo bangarenta mu yi hira.

Kwasar fafauwana na yi na shiga bangarenta tana ta bani labarin irin soyayyar da suka yi, ashe aure ta yi bata dace ba ta fito shi kuma ya ganta ya nuna yana sonta iyayensa suka amince kasancewar ba masu matsala ba ne, shi yayi mata komai kamar yadda yayi min a aurena, a lokacin ne take fada min shi ya saka ta makaranta ta yi karatu har take aiki.

“Amman ban taba ganin kin tafi aikin ba?”

Ta yi murmushi.

“Yanzu kin ga ina da ciki wata 6 kuma gaskiya bana sha'awar aiki, na fi sha'awar zama a gida yanzu na kula da mijina da aurena, daman dai babu abun da na rasa kawai ra'ayi ne, yanzu kuma na gane hakan ina son zama a gidana ko ba komai hankalinsa zai fi kwanciya za mu kula da shi tun da ba ni kadai ba ce a yanzu”

“Haka ne, amman aiki yana da sha'awa ina son aiki sosai”

“Amman ke baki gama karatu ba aka miki aure ko? Na ga ke din yarinya ce sosai har yanxu baki gama wayo ba”

Na sauke kaina kasa.

“Haka ma a gidanmu ake cewa wai bana da hankali ba na da wayo, wai kanwata ta fi ni wayo, amman ni bana ganin haka”

Ni da ita muka juya muka kalli kofar falon da aka bude Hafiz ne ya shigo ba a irin lokacin da ya saba dawowa ba, har da yar tsabararsa.

“Welcome Barrister”

“Yan mata na har biyu, me ake tattaunawa?”

“Hira ce kawai ta karatu take fada min tana sha'awar aiki, ni kuma yanzu ya gumshe ni har na aje sai nan gaba kuma idan komai ya daidaita”

Yayi murmushi ya miko min ledar hannunsa sai na saka hannu biyu na karba, sai dai na lura kamar hakan be mata dadi ba domin a take fuskarta ta canja.

“Aiki kike sha'awa Noor, ni yanzu bana sha'awar mace ta yi aiki, ita ma saboda ta dage sai ta yi ne, zan saka ki makaranta ki yi karatu mai zurfi saboda gaba, amman zancen aiki ba yanzu ba”

Na wara ido baki sake kai kace son karatun nake.

“Da gaske zaka bar ni na yi karatu?”

“Me zai hana ni fa dan boko ne, karatu sai kin ture yarinya”

Zan yi magana ta cafke ta nuna masa murnarta a fili na jindadin yadda yace zan yi karatu tana ta yabonsa har da masa godiya.

“Ke gani ko ai na fada miki ki kwantar da hankalinki Barr be da matsala ko kadan, shi mai son kyautata ma iyalinsa ba”

Annashuwa ta suka fuskarsa.

“Wato gulmana kika yi ko? Na kama ki”

Sai ta yi dariya tana kallonsa. Shi kuma ya kalleni.

“Ba zaki bude ledar ki ga miye a ciki ba Noor”

Na bude ledar na ciro gasashiyar kaza da kayan ciki mai Onion and vegetable sai kamshi suke. Leda ta uku kuma faranti ne dauke da yar tsutsar nan da na yi sha'awar ci tun ina zuwa restaurants din Kareem.

“Waya fada maka ina son wannan?”

“Na taba ji gurin Kareem”

“Na gode”

Ina fada ina kallonsa gaba daya ya gana faranta min zuciya a yau.

“Me aka dafa?”

“Ghanian jollof na yi”

“Ku kunci kenan?”

“Har kunci kenan?”

Ta amsa.

“Eh mun ci”

Na mike tsaye rike da leadar.

“Zan tafi bangarena na ci wannan sai na sha tare da tea”

“Okay Amarya aci dadi lafiya”

Ta fada na fice daga bangaren na dawo bangare na, wanke hannuna ne kawai ya same ni dole na wanke hannun na zauna na fara ci ina jin wani shauki saboda mai da take da shi gashi ta yi laka laka kamar kitsen kilishi. Bayan na gama na wanke hannun na yi alwala na yi sallah ina nade carpet ya shigo rike da plate dake dauke da kayan ciki da kazar da ya siyo dazun.

“Kin manta wannan Noor ko ba ki ci.”

“Na ci wannan abun na koshi”

“Ki aje wannan anjima sai ki ci”

Na karba na juya zan fice sai na ji ya rikoni yana kokarin rumgume.

“Kin yi min kyau yau fiye da kullum, ko dan kin dan sake jiki kin sake fuskar nan ne”

Na yi murmushin yake Ina sauraren yadda yake yawo da hancinsa a wuyana. Sallamar Na'ima ce ta katse hanzarinsa a dole ya sake ni da sauri yana amsawa. Ya fice daga dakin da sauri

“Wai Anty tana kiranka”

“Okay”

Na bi bayansa na shiga kitchen na aje naman sannan na fito na dawo falo na zauna ina kallo. Da zai shigo yi min sai da safe ne yake sanar da ni wai an yi gobara a gidan Baba, hankalina ya tashi sosai jin cewar gidan ya kore gaba daya.

“Amman ba a rasa kowa ba?”

“Da an rasa rai da Baba ya fada min, kin san baya boyo, amman dai gobe zamu je mu duba”

“Da dare nan aka yi wutar?”

“Da yamma”

“Dan Allah ko zaka kira min Baba na ji shi?”

Na tambaya tare da fatar zai karba bukata sai dai hakan be samu ba.

“Ki yi hakuri gobe zamu je mu duba”

“Tohm”

Kusan sai da na yi mafarkin wutar saboda na kwanta a abun a zuciyata, washe gari na gyara komai na shirya da wuri ina gama karyawa ya shigo bangarena da shirinsa muka fita, a nan ma na ga rashin jindadin fitar ta mu a tare a fuskar Aisha domin ta kasa saki fuska kamar yadda ta saba sai ce masa take ya dawo ya ci abincin rana.

“Wata kila ba zan samu dawowa ba, ita ma ai zata dawo ta yi girki ko?”

Ya kalleni ina zaune a gidan gaba.

“Eh”

Ta yi mana Allah ya tsare na rufe motar yaja muka kama hanya. Ba mu yi nisa da fara tafiyar ba ya kama hannuna ya rike yana murzawa a hankali.

“A kwana biyun nan fa ina ta jin sonki yana kama ni, kin san ni ban san dadin auren budurwa ba sai yanzu, Allah yasa na same ki fiye da yadda bake tsammani”

Na yi shiru ba dan ba gama fahimtar inda zancensa ya dosa ba. Shi kuma be sake ce min komai ba har muka isa unguwar, ina kallon gidansu Zafeer dai da idona ya cika da kwalla, a nesa da kofar gidanmu ya faka ba tare da ya kashe motar ba ya ce.

“Ki fadawa Baba idan zan zo daukarki xan shigo mu gaisa ina masa jaje”

Na kalleshi kadan na dauke kai, wata kila ya fara gajiya da halin Baba ne, ko kuma dai yana jin abun da yake nema a yanzu ya samu shiyasa yake son kaucewa daga jikin Baba. Ko da yake Baba din ne iya masa sai Allah ba kowa ne zai jure ba. Bude motar na yi na fita sai da na isa kofar gidanmu sannan yayi reverse ni kuma na shiga cikin gidan namu da ya kone tun daga waje har cikin gidan. Da gudu na karasa gurin Hana dake kwance tsakar gidan da konuwa a fuskarta zuwa cinyar hannunta.

“Innalillahi Hana”

Ta fara yunkurin tashi zaune. A lokacin da Baba ya fito bandakin da sauri yaka aje butar ya kalleni yayi murmushi.

“Aha ahhh wa nakd jin muryarta a gidan kamar Nooriyya yar albarka”

Na juya na kalleshi ina hawaye.

“Baba ashe gobara aka yi?”

“Kin gani dai haka Allah ya kawo mana, wutar da dare, ina mijin naki? Baki ce ya shigo ba? Kika bar shi a waje? Ba kara ya shigo ya ga yadda gidan yayi ba”

Ya fara tafiya sai na dakatar da shi.

“Baba ya tafi yace yana maka jaje za ku gaisa idan zai zo daukata”

“Au be tsaya ba? Tohmmm... Toh toh ba matsala ai duk daya ne, kuna dai zaune lafiya ko?”

“lafiya Kalau Baba, Baba me yasa ba a kai Hannatu asibiti ba? Kuna ce fa”

Na fada ina kallon maganin gargajiya da aka shafa mata.
Chapter 9 · 0% Book details