← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 82

Sashe 36

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin gaskiya ta ba zan karba ba, domin ko na karba ban san miye zan yi da su ba a yanzu. Sai dai na lura hakan be masa dadi ba domin rufe ni yayi da fada a dole na karba na yi masa godiya.

“Tafi bangaren Hajiya ki ce na ce cikin yaran nan duk wanda yake nan ya sauke ki gida”

“Tohm”

Na mike tsaye na yi ma Mama sallama sannan na fice daga falon yana ta kallona. Bangaren Hajiyar na dawo na sanar mata abun da Alhaji ya fada sai mutumen dake tsaye a gabanta yayinda take zaune ya juyo ya kalleni. A nan ma wani mamakin ya kara kama ni, mutumen nan da ya taba yunkurin biya min kudin siyayyar da na yi a wani dare da muka fita tare da Hafiz.

“Kamar na sanki?”

Na bude baki kamar zan yi magana sai kuma na yi shiru, ban san me zan ce ba, ni dai ina da saurin gane mutane shiyasa na gane shi.

“Noor ce Yar wajen Anty Amarya ce, ita ce wadda mijinta ya rasu”

“Ai ban sani ba, Allah ya jikanshi da Rahama”

“Ameen, ku tafi tare sai ka sauke ta ka wuce, Noor bari ga Abdull zai fita yanzu sai sai ya wuce da ke, ki jira shi a waje”

“Okay”

Na juya na fito daga ciki, ban san wacece motarsa a cikin motocin gidan ba dan haka zauna a balcony har ya fito.

“Kika zauna a kasa?”

Bance komai na na mike tsaye na bi bayansa muka isa gurin wata sabuwar mota, sai da ya fara shiga sannan na bude na shiga front seat. Ba tare da yace min komai ba yayi reverse ya fice daga gidan.

“Ina ne unguwarku?”

A lokacin da na dago sai na ga idonsa akaina suke. Na fada masa na sake maida kaina kasa kamar ba ni ba. Na ji lokacin da wayarsa ta yi kara ya amsa.

“Hello Safeena...”

Sai kuma yayi shiru, yana sauraren abun da ake fada masa.

“Yanzu na fito gida, amman zan biya ta can, sai na zo miki da shi, shi kadai kike so ko da wani abun?”

Na yi shiru ina saurarensa kamar wata Munafuka kamin na ji ya ce.

“Okay sai na dawo”

Ya aje wayar ya dago zan kalleshi idona suka fada cikin nasa da sauri na dauke kaina ina jin sautin murmushinsa. Ban sake kallon gefen da yake ba har muka isa unguwar.

“Ka sauke ni a nan unguwar bata da kyau can ciki”

Na fada.

“Karki damu, amanarki aka ba ni sai na kai ki har gida”

Yadda ya fada haka ya aiwatar har kofar gidanmu ya isa da motarsa ya faka, ni kuma na bude na fito zan rufe kofar ya ce.

“Ba godiya”

Ban ce masa komai ba na rufe motar, na gode masa sai ka ce rokonsa na yi ya kawo ni. Sai da na shiga gida sannan na ji motarsa ta bar kofar gidan.

KAREEM POV.

Yana gama sallah asuba ya shiga kitchen hadawa yaransa breakfast. Domin Yusura bata musu komai tun da ta dawo gidan, Kullum shi zai hada musu breakfast ko kuma ya saka aika musu daga restaurant dinsa kamin su tashi break.

And now cooking is one of his favorite things, yana samun nishadi a girkin, musamman idan yaran suka farka suka same shi a kitchen suna hayani yana aikinsa har ya gama, ya karya tare da su wani sa'in kuma ya zuba musu na su, ya tafi da nasa a office ko kuma su su tafi da na su school shi kuma ya ci a gida. Idan ya fita sannan Yusura take saukowa ta gyara ko'ina ta dora na rana. Tun da ta dawo gidan be taba leka dakinta ba, be taba ce mata uffan ba, ita ma kuma bata bari sun hadu ba, da zarar ta ji motarsa ko ta san lokacin dawowarsa sai ta shige dakinta.

Yau ma sai da ya raka su har gurin bus sannan ya dawo ya zauna ya ci nasa breakfast. Bayan ya gama ya mike tsaye ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya ya fito yana rike da lab coat dinsa da wayarsa sai kamshi yake zuba. Yayi kyau sosai ramar da yayi ta kara masa kwarjini da haifa. Sai da ya fice daga falon sannan Yusura ta sauko a zatonta ya fice gaba daya, dinning ta nufa ta tsaya tana kallon kayan karyawar da ya shirya, biredin da ya gasa ta dauka taba tabe baki ta shinshina ta aje.

Sannan ta ja kujera ta zauna ta bude flask din ruwa zafi, a daidai lokacin Kareem ya turo kofar falon ya shigo domin daukar wallet dinsa da ya manta a dakinsa. Kallo daya yayi ma gurin da take zaune ya dauke kai ya haura sama ya dauko wallet dinsa ya sake fice. Yusura bata taba jin kunya irin ranar ba, bayan amincewa da aurensa da ta yi wannan ne abu da na biyu da take bakinciki a rayuwarta, ji ta yi kamar ta fasa komai na gidan dan bakinciki.

Tuki yake a hankali har ya isa asibitin, ya faka motarsa a gurin da aka rubuta Dr Kareem sannan ya fito ya dauki kayansa ya rufe motar ya shiga cikin Babbar asibiti ana miko masa gaisuwa yana amsawa. Office dinsa ya shiga ya fara duba takardun dake gurin sannan ya fita ya fara duba marar lafiyar da aka aje da ya kamata ya duba su.

After ya gama ya dawo ya zauna a office dinsa patient din dake shigowa suka fara shigowa yana dubata. Third person da ta shigo ita ce Safeena, tana sanye da dogon Hijabinta har kasa sai dai hakan be boye cikin dake jikinta, har ta zauna ita yake kallo. Sai da ta aje jakar dake hannunta sannan ya jingina baya ya kwanta jikin kujerar yana kallonta.

“Wai ke wace irin yarinya ce Safeena?”

“Ni din wata yarinya ce, mai wuyar warke ciwo, wata yarinya ce da ka koyawa soyayyarka kuma kake kokarin guduwa bayan ka yaudareta da farko”

“Gargadin da na yi miki, da kuma tazarar da na baki daga lokacin da muka yi haduwar karshe zuwa yau bata fahimtar dake, na rumgumi kaddarata, ke ma ki rumgumi taki?”

“Ka rumgume kaddara saboda Yusura tana sonka tana kyautata maka a yanzu? Ko kuma daman can karya ka yi min kace bata kula saboda kullum ka rika samun biyan bukatarka da ni? Ka yi breaking heart dina da farko yanzu kuma bayan na saba mu'alama da kai na saba da kwanciya a kirjinka na saba da soyayyar kake tunanin sake guduwa ka bar ni?”

Ya mike tsaye daga zaunen da yake ya nufi windows dinsa ya bata baya.

“Kana da kyau, Kareem kana da kudi amman duk wannan be tabbatar min da ina sonka ba sai da mu'amala ta hada mu, all this while na kyale ka ne saboda ina dauke da cikin nan”

“Me kika zo yi yanzu? Tashi ki fice daga office din nan”

“Baka da wannan damar ba saboda da kai na zo ba, saboda cikin nan ne, na dawo da awon cikin nan a nan ne, a nan zan yi ta zuwa har zuwa lokacin da zan haihu”

Ya dafa Window ya rike kansa.

“Namiji zan haifa suka ce, kuma ina alfahari da haka”

Kareem ya dauki lokaci a haka kamin wani tunanin ya zo masa sai ya juyo da sauri ya kalli cikin na ta sannan ya kalli fuskarta, sai ta yi masa murmushi.

“Fita ki bar office din nan”

Ya nuna mata kofar, zata sake magana da daka mata tsawa har sai da ta zabura.

“Fita ki bar office din nan na ce”

Ta mike tsaye da sauri ta dauki jakarta tana kallon yadda ya hade fuska kamar be taba ganinta ba, ta fice daga Office din. Dawowar yayi ya zauna kan kujerar ya dafe kansa ya runtse ido yana numfashi da karfi, ya girgiza kai kamin ya daga hannunsa ya buga a tebur din yana jin wani irin bakinciki marar misaltuwa...

It could be a joke maybe tana gwada shi ne, if not ai tana da hankali matukar ba wata manufa take da ita akansa ba ba zata taba sha'awar haihuwa da shi alhalin tana da aure ba, ta dauki dawainiyar cikin da ba na mijinta ba ta kai masa yayi komai, ba zata fara ba. Abun da zuciyarsa ta raya masa kenan har ya ji ya samu saussaucin cigaba da aikin da yake. Sai da lokacin tashi aikinsa yayi ya tuna da ba shi da abokin hira ko shawara a yanzu domin Hafiz is no more balle ya fada masa hasashensa ko damuwarsa.Tafiyar Ya Nabil karatu ta zame ta bude min wani gurbi a gidan. Domin ruwan da yake debo mana da safe yanzu nauyin ya koma kaina, ni nake cika gidan da ruwa ga jikin nawa ba mai son wahala ba ne amman haka nake daurewa ina yi saboda gujewa hayaniyar Baba bana son ya jefe ni da wata kalmar marar dadi a yanzu. Haka ma ba fita nake son yi ba, saboda idanuwan mutane yana kaina, idan na hadu da kanen Zafeer har jefa min magana suke kamar ni na so mutuwar auren ko kuma zaman gidan.

A haka dai na daure na danne zuciyata ina cigaba da rayuwa a gidan ubana. Ranar wata labara Anty Larai ta kawo mana ziyara har da tsarabarta domin ta dade rabonta da gidan. Rabon da na saka a ido kuma tun a gurin gaisuwar Hafiz. Na yi murna sosai da ganin tana cikin Gwagganina masu hankali da kamanta adalci daidai gwargwado. Ina zaune kusa da ita nabban danta Ridwan Wanda ya kasance cousin ne a gareni sai tsokana ta yake, ni kam baki ya mutu bana cewa komai, Hana ce take ramawa sai Umma dake dan jefo magana sama sama.

Gwaggo ta shafa kaina zuwa bayana tana murmushi ta ce.

“Ka bi ka saka min yarinya a gaba, saboda yanzu ka samu ta yi lafiya ko? Da ada ne ai ba zaka iya da ita ba”

“In ji waye ko a da ne zan iya, kawai ina daga mata kafa ne”

Anty Larai ta bude jakarta ta dauko goro ta gutsira tana fadin.
Chapter 36 · 0% Book details