← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 82

Sashe 81

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarsa ta yi ringing ya ciro wayar ya duba farincikinsa ce take kira wato Noor, ya amsa wayar ya kara a kunne shi ma dai sound din kiransa a karshe yake kamar yadda na mutane da yawa yake a manyan wayoyin yanzu.

“Kareem ka yi magana da Baba? Me ya fada maka?”

Sai da yayi iya yadda zai ya danne yakin dake zuciyarsa ya amsawa Noor da murya mai sanyi.

“Na yi magana da shi be yarda ba, amman zan sake samun shi gida mu yi magana karki daga hankalinki”

“Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...”

Safeena ta fada da karfi, Kareem yayi hanzarin kashe wayar, fuska a hade ya jefawa Safeena mugun kallo da idanuwansa da suka gama canjawa. Wani marin ya sake kai wata, ya saka kafarsa ya kwashe nata kafafuwan sai da ta fadi kasa, ya daga kafarsa ya daki bayanta sai da ya amsa, sannan ya cire belt din jikinsa ya fara zuba mata ba ji ba gani...
Duka yayi mata sosai kamar wani ubanta sannan ya fice ya barta a gurin tana ihu tana kuka. Motarsa ya shiga ya kama hanyar tafiya ganin yarsa domin ya san a yanzu su kadai suke rage masa, aikin ma baya jin zai iya tafiya a yau tun tashinsa baya jin lafiya balle kuma yanzu da abubuwa suke juye masa. Sai da ya shiga unguwa ya ji ba zai iya karasa family house dinsu ba, nesa da gidan ya faka mota ya kwantar da kujerarsa ya jinke hannunsa ya rufe ido yana nadamar dukan da yayi ma Safeena, domin be tana kai hannunsa yayi ma mace duka irin wanda yayi mata a yau.

Yana cikin motar ya aka kira sallah azahar sannan yaja motar daker yana jin kansa na ciwo kamar zai tsage gida biyu ya isa masallacin unguwar yayi sallah ya sake komawa motarsa, sannan ya karasa gidansu. A harabar gidan ya faka motar ya kashe yana kallon flowers din da suke gabansa amman zuciyarsa tana can wata duniyar. Wayarsa ya ciro ya duba number Noor ya sauke ajiya zuciya ya kai sau takwas sannan ya danna na aika mata kira cikin tsoro jikinsa har rawa yake.

Shiru yayi bayan ta daga kiran, sai kuma ya rasa me zai fada mata, ya zai fara mata bayanin komai ya zai wanke kansa, ta ina zai fara fahimtar da ita, be ma yi tsammanin zata amsa kiran ba.

“Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!”

“Noor”

Zai yi magana ta yanke kiran, runtse ido yayi sosai, ne bude ba sai da ya ji an bude gate din gidan, direban dake dauko yaransa daga makaranta ne ya dauko su ya faka a inda ya saba faka motar. A yake Kareem ya nemo kwarin guiwa da juriya ya sakawa zuciyarsa ya bude motar ya fito cikin karfi hali yake takawa yana murmushi ya nufi yaransa da suka nufo shi suna.

“Oyoyo Dady Dady Dady”

Kamin ya karasa gurinsu su ma su karaso gurinsa ya yanke jiki ya fadi kasa ribbbb.

“Dady.....!”

Tine ta saka ihu ta saki bag dinta da lunch box din dake hannunta ta kama mahaifinta tana kiran.

“Momy Hajiya... Anty Khadija... Yaya Aaryam... Dady na ya fadi... Dady...”

NOOR POV.

Sai da na zabura a lokacin da yayi hanzarin yanke wayar, kenan yana tare da Safeena har yanzu? Kuma yake fadar yana so na? Yake fadar ya tuba? Yake fadar yayi nadama? Me ya kai shi gurinta? Me yasa ma zai amsa wayata a gabanta.

“Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...”

Maganar Safeena ta sake nanata kanta a kunnena, zai iya zama gaskiya shiyasa dazun ya daure ni da kalamansa, namiji zai iya aikata komai domin ya samu biyan bukatar kansa. Na mike tsaye zuciyata na raya min Safeena ce matar da Baba yace ta same shi da maganar, ita kuma ta ji ne ta gurin Kareem.
Ya fada mata sirrina kamar yadda ya fada min nata, me yasa yake haka? So yake ta jefa ni a matsala ta yadda zan rasa kowa sai shi kadai shiyasa yake taimako na a ko da yaushe? So yake na rasa kowa na zama tare da shi shi kadai, shi kuma sai ya juya ni a yadda yake so? Yanzu na gane dalilin duka taimakonsa na gane manufarsa, na gane buri da bukatunsa.

Sai bayan Sallah azahar sannan kiran Kareem ya shigo wayata, na sani daman zai kira ko ya zo domin kare kansa, kuma na shiryawa duk wata karyarsa sai na ga iya gudun ruwansa. Na amsa kira sai yayi shiru ba tare da ya ce komai ba.

“Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!”

Na fada masa kai tsaye hawaye na zubo min zuciyata na zafi because this is the most hardest words i had ever said to someone, who's there for me in every Situations, rabuwa ce irin wanda rai be so ba amman dole na yi.

“Noor...”

Zai yi magana na yanke kiran ba tare da na tsaya na saurari abun da zai fada ba. Na dafe zuciyata ina kuka he's someone who's  always been a good friend to me, but the fact that i know yana da manufa na yin haka ya yanke duk wani hanzari, ya ture duk wani uzuri nasa, ba zan iya yarda na lalata rayuwa saboda namiji ba.
Karfin hali na yi na fita na siyowa Hana maganin zazzabi domin jikinta yayi zafi sosai fever ya rufe ta.

Ana gama sallah la'asar ban tsaya cin abincin rana da Umma ta sauke ba na yi mata karya cewar Zainab ta kira waya na kaiwa mahaifiyarta su yi magana saboda wayar mahaifiyarta ta lalace.

“Ki dawo da wuri, domin Babanki tun da ya fita be dawo ba har yanzu kin san kuwa yana hanya a yanzu, idan ya dawo be same ki ba, ke ce a ruwa”

“Ba zan dade ba In Shaa Allahu”

Na saka talkamina ina kara sirranta jakata dake boye a hijab dina na fice daga gidan, kai tsaye titi na nufa daman manufar ta samu dalilin fitar ne. Ina kokarin taron Napep na muka yi ido hudu da Zafeer zai karya kwanar gidanmu da wata kafirar mota mai kyau da kyalli. Wuce ni yayi ya shiga kwanar ni kuma na shiga Napep din na fada masa inda zai kai ni, yana tafe ina mamakin mi ya kawo Zafeer a nan ya domin tuni ya dauke iyayensa daga unguwar saboda likkafa ta yi gaba a wata unguwa mai kyau suke zaune a yanzu.

A kofar gidan Abdull kuma gidan Safeena mai napep din ya sauke ni na bashi kudinsa na shiga gidan bayan mun gaisa da mai gadin, har yake fada min bata dade da shigowa gidan ba. Da manifa biyu na zo gidan an roketa alfarma ta saka mahaifina ya janye ko kuma na yi mata ta karfi.
A bakin kofar falon na tsaya na bude jakata na dauko wayata na sakata a airplane mode sannan na kunna recording na shiga falon ina sallama, wayar na rike a hannuna.

“Wa'alaikumussalam, bakar macijiya me kuma ya kawo ki?”

Ta amsa min tana tsaye rike da maganin da ban san na miye ba a hannunta, fuskarta ta kumbura daga bakin inda yake ina kallo a jikin, fuskarta da kafadarta zuwa kafafuwanta da hannunta sun yi ja, alamar an mata duka.

“Magana na zo mu yi dan Allah ki saurare ni Safeena”

“Ina jinki”

Na matsa kusa da ita na fara mata magiya da raunaniyar murya.

“Idan kina tunanin wani abu ne a tsakanina da Kareem, Wallahi babu dan Allah dan girman Allah ki yi hakuri da abun da na yi miki, ina rokonki alfarma ki saka Baba ya janye shari'ar nan”

“Ashe kin san kin cutar da ni, wato yanzu kina son mu sasanta dan kar auren uwarki ya mutu kuma asirin kawarki ya tonu ku kunyata ko? Amman ke kika son kunyata ni, ki bara ni da abun da nake so, kin yi iya yadda kika iya har sai da kika fitar da ni a zuciyar Kareem, hakan be miki ba sai da kika auri mijina, hankalinki be kwanta ba sai da kika fada masa cewar dan da na haifa ba jininsa ba ne”

“Cikin fushi na fada masa hakan, kuma ba dan ya sake ko ya juya miki baya ba, kawai na fada ne saboda a lokacin raina yana bace ne, na bakinciki abun da yayi ma kanwata”

“Ai kin ci riba idan bibiyar mazan mutane yana da kyau kin gani ai, kin gaji kwadayi gurin ubanki, gaba daya kin firgita min tunani, kin saka Kareem ya tsane ni mijina ya tsane ni, mijina yana garin nan amman ya ki ya zo gidana, yau kuma Kareem yayi min abun da be taba ba, kin saka masa wani banzan hali da ba na shi ba, na tsane ki Noor”

Na risina kasa ina rokonta.

“Dan Allah ki taimaka min Safeena, Wallahi ba zan fadawa kowa cewar kin haihu a waje ba, dan Allah ki fadawa Baba karya kike ya janye shari'ar nan”
Chapter 81 · 0% Book details