← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 82

Sashe 66

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Okay ta kwashe karya da gaskiya ta fada miki kin zo kina zargina da abun da ban aikata ba ko? Saboda tsaurin ido har ki kalleni kina kirana da suna kala kala ko? Ni fa mijinki Noor”

Na tofa masa yawu a fuska.

“Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye yanzu kam, da can amman ban da yanzu”

“Okay rashin kunya zaki nuna min ko? To sai na ga idan akwai uban da ya isa ya saka na sake ki, kuma kika sake fada min wata maganar banza sai na ci ubanki yanzu nan”

“Ubana yayi maka yawa, kuma babu wanda zai saka kaka kai zaka sake ni dan kanka, wato kai da yake namiji mai karfin hali dan duniya har kana da bakin yakata ko? Taya zaka ba ni maganin bachi ka tafi ko wane dare ka kwanta da yar'uwata sai asuba ka dawo ku ci amanata a tare kuma ka ce ba zaka sake ni ba? Wallahi karya kake Abdullahi”

Ya nuna kansa yana murje ido kamar da gaske be aikata ba.

“Ni nake saka miki maganin bachi?”

“Aa ni nake sakawa kaina, wanda ka ba ni jiya ya zube ban sha ba, ina kallon lokacin da ka tashi daga dakin nan ka tafi dakin Hana, na labe na ji abun da kuke magana a kai, har ciki za ku zubar”

Na fashe da kuka domin ba ni da wani abun yi a yanzu kamar shi.

“Ba laifinka ba ne, laifin yar'uwata ne ita da ta ci amanata, dama kum jira wata kila gurin haihu zan mutu ai sai ka aureta ku zauna”

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Ya sassauta muryarsa.

“Noor Wallahi aikin sheidan ne, kuskure ne aka samu, me Hana ta fada miki?”

“Ban saurareta ba, kamar yadda ba zan saurareka ba, saki kawai nake so ka sake ni”

“Ni ba zan sake ki ba Ina son ki Noor shedan ne Wallahi”

Kalmar ina son ki ta saka na ji kamar da wuka a kusa na daka masa a sautin zuciya. Ya matso kusa da ni

“Abu ne da zamu tsaya mu rufawa juna asiri, ita yar'uwarki ce ni kuma mijinki ne, kuma ga cikina a jikinki Noor, Wallahi na miki alkawari ba zan sake ba”

“Gobe zan tafi na bar muku gidan, ku cigaba da aikata abun da kuke har mahadi ya bayyana, ni dai ka sake ni”

“Ba zan sake ki ba Noor ni ba zan sake ki ba, ni ban taba aikata komai ba sai a wannan karon da Allah ya kawo tsautsayi”

“Karya kake, ba wannan ne karon farko ba Wallahi kawai dai ban gane ba sai yanzu, shiyasa tun kamin ka aure ni kake ta taba ni, da na yi magana ka ce gwada ni kake yi, ashe gwadawa kake ka gani idan ni yar iska ce na amince maka a waje, ka gama da ni ka tafi, da hakan be samu sai ka bijiro da maganar aure, da na samu ciki kuma sai na daina burge ka saboda ba auren Allah ba ne, auren sha'awa ka yi min. Sai kuma sha'awarka ta koma gurin kanwata jinina, ita kuma bata duba alaka ba ta yarda kuka taru kuka ci amanata”

Na dafe zuciyata ina bakincin da ban fahimci wannan red flag din ba tun farko, ga kuma Safeena ma ai izina ce.
Ya dafe kansa ya juya ya juyo ya fara safa da marwa kamin ya samu tsayawa gabana a rikece har da fashe min da kuka.

“Dan Allah ki kwantar da hankalinki mu yi magana ta fahimta, sakinki zai bata abubuwa ne kawai, ina zaki je da ciki? Abun nan aikin shaidan ne Noor zai iya fadawa kan kowa, zan tafi na bar miki gidan har hankalinki ya kwanta amman ni ba zan sake ki ba”

A take kukan ya yanke min.

“Ba zaka sake ni ba saboda kana tsoron kar a tambayi dalilin mutuwar na fadi cewar kai da yar'uwata kuka ci amanata?”

Yayi kamar be ji ba dauki wayarsa yana kuka zai fice dakin.

“Ba zaka sake ni ba, sai na hada maka cewar dan da Safeena ta haifa maka yanzu ba jininka ba ne, ďan falkanta ne, ex-boyfriend dinta? Sai na fada maka dalilin da ya saka Safeena ta daina daga maka hankali akan aurena? Sai na fada maka na san Safeena irin wanin da baka yi mata ba? Sai na fada maka a duk lokacin da ka bar Kano tana tarayya da Ex dinta ne har sai ka dawo? Sai na fada maka Safeena ta taba ji min ciwo a hannu saboda ta yi tunanin Ex dinta kuma falkamta so na yake, saboda kishinsa?”

Ya juyo ya kalleni kukan da yake ya tsaya.

“Kina cikin bachin rai ne, zaki iya fadar komai Noor na sani”

“Ina cikin bacin rai, amman ba cikin gushewar hankali ba, idan baka yarda ba ka dauki yaron ka gwada jininsa da naka mana, ka cancanci haka ai, daman shege sai dan iska, a da har mamakin dalilin Safeena nake na aikata haka, ashe ta yi daidaita kai din tsohon shege ne”

Ya daka min tsawa.

“Ya ishe ki haka yanzu kam ya ishe ki haka? Mace nawa take kama mijinta yana abun da be dace ba amman ta rufa masa asiri a zaune, balle ni da kaddara ce kuma ba ni kadai ba har da yar'uwarki, kusan ma ita ta ja ra'ayi a komai”

“Wallahi ko kai ne dan autan maza na gama zaman aure da kai Abdull, ko ka sake ni ko na daga na kira uwarka a yanzu na fada mata abun da ka aikata da kanwata kuma na tabbatar mata cewar ďan da Safeena take shayarwa a yanzu ba jikanta ba ne? Domin ba jininka ba ne, na yarda idan aka bincika aka tararda tsabanin haka a kai ni kotu, ko dai so kake na kira kanenka da mahaifiyata ma fada musu? Kwanciyar hankalinka ka sake ni, Ba zan fadawa kowa abun da kuka aikata ba ni na bar ku da Allah”

A fusace ya nufi takardar ya dauka yayi rubutu a kai ya jefa min a fuska.

“Ke ce da bakinciki ba ni ba...”

Ya nufi kofa.

“Allah ya raba ni da bakinciki tun da ya raba ni da kai”

Na fashe da kuka mai karfi. Na yi kuka kuka sosai kuka irin na macen da rauni ya mamayeta ta rasa makoma, saki nake so kuma na samu yanzu idan na koma gida me zan fadawa iyayenmu? Na fada cikina ina bakinciki da ban zaba masa uba na gari ba. A dakin na kwana, sai dai bachi be dauke ni ba, bayan ruwa bana shan komai ba, shi kuma tun da ya fita be dawo ba, har garin Allah ya waye.

Cikin kuka da bakinciki na yi sallah Asuba, na roki Allah ya sanyaya min zuciyata ya sanya min saka min kana'a domin har lokacin ban ji zan iya yi ma yar'uwata wata bakar addu'a ba, har gobe ita din jini na ce idan wani abun ya faru da ita kamar ya faru da ni ne. Ni dai na san na barta da Allah shi ya san abun da ya dace da ita kuma shi ya san sakamakon da zai yi min akanta.

Misalin shida da rabi na fara hada kayana cikin akwaiti sai da na yi nisa da hadawa sai kuma, sai kuma na ji bana bukatar kala ko daya domin Abdull ne ya siya, a yanzu kuma bana sha'awar duk wani abu mai alaka da shi. Cikinsa ma da yake jikina da ace zan iya da cire shi zan yi na aje masa a gidansa na yi tafiyata. Jaka kawai na nufa na dauka na hada yan kudadena na dauki wayata ita ma dan ta zame min dole a yanzu.

Hijabi na saka sannan na dauki takardar sakin da ban iya karantawa ba na saka a jaka na nufi kofar dakin na bude, sai na yi arba da doguwar takardar aje a kofar daki. Na duka na saka hannu na dauka a tunani Abdull ne ya aje min amman da na fara karantawa sai na tararda sabanin haka..

_Yar uwata noor, ban ci amanarki, ba zan taba iya cin amanarki ba, ba ki saurare ni ba, bakinciki be bari kin tuna da halina ba! Yadda kika dauki abun ba haka yake ba, Wallahi mijinki ya nuna min fin karfi ne, ya fara tallata min bukatarsa tun a lokacin da na bukaci tafiya gida kika hanani ne. A lokacin bana son fada miki ne saboda kar na zama silar lalacewar aurenki..._

Na hade yawu na nufi kujera na zauna.

_Da ya fahimci ba zan aminta ba, sai ya shirya min tarko, ranar Monday da muka fita da sunan zai sauke ni a hanya, sai ya biya da ni a wata tsohuwar ma'aikatarsu, yace min zai tafi ya duba wani abun ne, ban yi tunanin zai nuna min karfi ba ne, shiyasa ta yace na shiga wani office na dan jira shi, na jira har na gaji da zama be dawo ba da na fito sai na lura gurin babu mutane sosai, na tsorata da farko na dauka siyar da ni zai yi, ashe kudirinsa dabam ne. Na koma ciki na zauna jiransa har ya dawo, sai ya fara lallaba ni yana min kamfe da abubuwan da yake min na kyautatawa ashe ba dan Allah yayi min ba, da na nuna masa ba haka ya fara kokawa da ni, Wallahi na yi ina yadda zan iya na kare kaina Noor amman hakan be samu ba sai da ya biya bukatarsa, a ranar ban samu tafiya makaranta ba a gurin na wuni, sai da ya dawo aiki ya biyo ya dauke ni aje ni nesa da gidan na tako na iso da kafa sannan ya shigo_

Hawayena sun zuba jikin takardar na juya dayan shafin ina karantawa.
Chapter 66 · 0% Book details