← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 82

Sashe 3

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya ya fita daga dakin, ni ma na bi bayansa, yana shiga dakina ya dauki makullinsa ya fice daga gidan. Ni kuma na kife kan gado ina wani irin kuka sosai mai ban tausayi, Kareem kawai nake hangowa irin halin da zai shiga, ni kaina da na yi rashin uwa a kusa da ni ya kasani wani kalar hali na kunci da kewarta balle kuma ace ta tafi kenan har abada, ga shi ba dadin matarsa yake ji ba, Allah kadai ya san halin da zai shiga a yanzu.

Ban wuce minti talatin da shiga dakin ba, macen dake fadar jiri na daukarta bata iya bandaki sai gashi ta kawo kanta a bangare kamar ba ita ba.

“Amarya har yanzu kukan ne? Ayi hakuri mana duk mai rai a mamaci ne”

Ta zauna kusa da ni tana fadar haka har da kai hannu ta shafa bayana alamar rarrashi.

“Hmmm ina mamakinki a haka ma kina tausayin Kareem, ina ga ace kin san abun da aka boye miki?”

Na tashi zaune ido da hawaye na kalleta.

“Kamar ya? Bata mutu ba kenan ko kuma me?”

“Aa ta rasu fa, ba akanta nake magana ba akam Kareem din kansa”

“Me kike nufi?”

“Sannu a hankali zaki san abubuwa da yawa kanwata, matukar idan muka yi sirri zamu haka rame mu bunne babu wanda ya ji, yanzu ma din ma zuwa na yi na roki wata alfarma a gurinki”

Na goge hancina ina kallonta.

“Ta me?”

“Dan Allah ko da yan'uwanki ko yan'uwan Barrister sun shigo karki fadawa kowa cewar ba ni da lafiya, irin wannan rashin lafiyar ta aljannu ba abar yayata ba ce, kuma ba kowa zai fahimta ba, duk abun da aka yi a gidan nan ko tsakanina da ke ko da mijinmu karki bari kowa ya ji, ko a musulumcin ana son rike sirri, shi ne yarda kuma namiji yana son mace mai tsanannin rikon sirri, tsakaninki da shi dabam, haka kuma sirrin dake tsakanina da ke dabam”

Na daga mata kai cike da gamsuwa.

“In Shaa Allah Madam ba zan fadawa kowa sirrina dake ba, kuma ba zan fadawa kowa baki da lafiya ba”

Ta yi murmushi

“Madan kuma?”

“Haka na ji Barrister yana fada, ban san sunanki ba”

“Sunana Aisha, sunan Madam suna ne da Barrister ya saba min da shi, ni kuma nake masa lakani da Barrister, amman ke zaki iya kiransa da sunansa kai tsaye daman ba son shi kike ba balle na ce ki yi masa sunan soyayya, ni kuma ki kira ni da Sunana Aisha bana son wani Anty ko Yaya ko Maman wani balle Madam”

Me yasa Hafiz ya fada mata bana sonsa? Gashi sai yawan nanatawa take ina jin wani iri, ko da yake gaskiya ta fada bana son sa dole ce aka yi da kuma kaddarowar Ubangiji.

“Tohm In Shaa Allah”

“Yauwa, bari na shiga ciki na yi wanka na ji jikina ya dan saki”

“OK”

Ta tashi ta fice daga dakin, ni kuma na shiga bandaki na wanke fuskata ina jin cikina na kukan yuwan.
Misalin Goma mutane suka fara shigowa yan ganin amarya daga yan'uwansa daga bisani kuma nawa yan'uwa suka fara zuwa. Babu wanda na jidadin zuwansa irin Hana domin jiya ba da ita aka zo ba, a yau kuma ita kadai ce zan iya fadawa damuwa. Domin na kasa sakewa kowa ya kalli fuskata ya san na sha kuka sosai idona ya nuna haka. Wata kila wasu daga yan'uwa mahaifina da suka san bana maraba da auren za su yi zaton wannan kukan na kiyayyar auren ne na yi, yan'uwan Barrister ma sai na ga jikinsu yayi sanyi sosai sai kallona suke kasa kasa ba su wani dade ba suka tafi bayan Zainab da Yar Fulani da Hana sun girka abincin rana. Haka Aisha ta shigo aka yi ta hira da ita sai kusan karfe hudu sannan Hafiz ya dawo gidan ba tare da ya shigo bangarena ba ya dauketa suka tafi gidan mutuwar.
Sai da mutane suka fara ragewa sannan Hana ta saka ni a daki muka zauna ta ce.

“Noor ina dalilinka na kuka uwar abokin mijinki ya mutu? Uwar mijinki ce balle hakan ya dame ki? Ina ruwanki?”

“Hana akwai tausayi fa, Wallahi Kareem yana da kirki kawai dai raba ni da Zafeer da zama sila ne nake jin na tsane shi, kuma ki duba yadda muka ji da Mama ta tafi balle kuma ace uwarta ta mutu fa”

“Akwai tausayi amman be kamata ki rika kuka haka ba, ke dai kina kukan auren ne ko? In ba haka ba ban ga ta inda mutuwar uwar wani ta shafe ki ba, Noor ki natsu dan Allah kin ga auren nan an riga an daura ki yi hakuri ki zauna ki bar wa marar da kunya, gashi kin samu kishiya ta kwai inda har ba munafurci take ba to tana da halin kirki, yanzu idan wani abu ya faru kin san Baba ke zai dorawa laifi, kuma Mama zata shiga tashin hankali, gidanki yayi kyau sosai, kowa sai magana yake, kuma mutumen yayi miki hallacci sosai be kamata ki bijiro masa da wani abun na rashin dadi ba, ki duba yadda kika bar gidanmu yanzu ke mai yanci ce sai abun da kike so kike dafawa, ko ki ci haba Noor dan Allah ki natsu”

A nan kuma sai na ji kewar rayuwar gidanmu ta dawo min sabuwa, sai na ji babu dadi. Ban raina kaina ba sai da za su tafi da magariba, bayan sun gyara min gidan ko'ina fess, suka jera min lefen da suka zo da shi a cikin Wardrobe dina. Har gurin Gate na rakasu na tsaya daga jikin gate din ina kallonsu har na daina hangosu sannan na juyo na dawo cikin gidan kamar wata marainiya, ina ta jin kadaici da kewar gidanmu, gashi an kawo ni a gurin wanda bana so kamar yadda matarsa Aisha take ta yawan fada. Duk yadda ake yawa kyaun falon da dakina ni dai na runtse ido ban ga kyau a makamata ba. Wata kila saboda hankali be kwanta da auren ba ne ko kuma dai saboda kyalkyali duniya baya gabana a yanzu. Na ji kewa na ji kadaici da tsoro kamin Hafiz ya shigo bangarena domin na ji tsayawar motarsa tun bayan da aka gama sallah Isha'i sai dai be samu shigowa bangarena ba sai tara da yan mintuna.
Wike na yi masa da ido ina kallonsa kamar mai jiran ya fada min wani abu, sai yayi murmushi ya tsakali hancina da keys din motar dake hannunsa.

“Wannan idon da aka sakar min fa? Babu sannu da zuwa babu komai”

Na sauke idon kasa ina jin haushi yadda ya taba min hanci.

“Amaryata, kin yi sallah”

Na daga mishi kai ba tare da na kalleshi ba, sai ya cire hular kansa ya aje ya fara kokarin cire tufafinsa, ina ganin haka na tashi na koma falo na zauna na bar masa dakin. Sai kusan goma ya fito daga dakin sanye da wata sabuwar Shadda, yana ta kamshin turare ya zauna kusa da ni.

“Me kika ci?”

Ya taba bakina sai na kauce.

“Na ci abun da aka dafa kadan”

“Ta so mu tafi Wani guri mai kyau mu siye wani abun sai mu dawo, ban samu riko komai ba saboda mun dawo gida jikin Madam sai a hankali yayi zafi sosai, amman dai na kira kanwarta zata so ta taya ta kwana”

“Ni ba sai na je ba, zaka iya tafiya ka siyo ai”

“Idan haka kike so, ba matsala”

Ya kai bakinsa zai sumbanci bakina na kauce da sauri na tashi tsaye na bar gurin na koma dayar kujera na zauna. Murmushi na ji yayi mai sauti ya girgiza kai sannan ya mike tsaye.

“Hafiz”

Na kira sunanshi sai ya juyo ya kalleni.

“Amaryata ba ki ji sunan ya miki girma ba? hafiz kai tsaye”

“Toh ai sunanka ne?”

“Haka ne to amman yanzu ni ai mijinki ne”

“To ya zan ce maka? Mijina?”

Yayi murmushi.

“Fada min abun da kike son na siya miki?”

Na sauke idona kasa ina taba hannuna.

“Daman ina son na tambaya Ya Kareem yake?”

“Da sauki?”

“Yayi kuka?”

“Wanda ya rasa uwa ai dole yayi kuka Noor, uwa ba wasa ba”

A take idona ya cika da kwalla.

“Yayi kuka sosai?”

“Namiji ne shi ai, a boye zai yi”

Na dada noce kaina kasa domin bana son ya ga alamar hawaye a idanuwan nawa. Bw sake ce min komai ba ya shiga dakina be jima ba ya fito ya fice. Misalin Sha daya ya rabi ya shigo bangaren nawa a lokacin ina kwance kan gadona na yi shiruuu ni bana tunani kuma bana kuka, babu damuwa babu kuma farinciki a tare da ni. Not too good not too bad. Ina kallonsa har ya sauke ledadin dake hannunsa sannan ya karaso inda nake kwance ya shafa bayana, hakan ya saka ni hanzarin tashi zaune na buge hannunsa.

“Ka daina taba ni bana so Hafiz”

“Hmmm zaki saba”

Ya fada yana murmushi, ni kuwa gabana sai faduwa yake ina yawan tuna labarin da Aisha ta fada min akansa. A daren mun samu aiwatar da sallah nafila da ba mu samu damar gabatarwa ba a daren da ya gabata wadda shi ne darenmu na farko. Ya cilasta min cin naman kazar da gas meat da ya siyo daga wani restaurant din, duk yadda nake da kwadayi da son dadi sai na kasa sake jiki na ci komai gaba daya komai ya fice min a kai. A gurin kwanciya ne aka fara samuwar drama domin ni ba zan yarda na kwanta gado daya da shi ba, musamman da na lura da yadda yake ta son taba a lokacin da muke cin abinci, baya ko taya abokinsa jimami kirkiri zai taba yar mutune saboda babu kunya a idonsa.

“To yanzu ya kike so ayi?”

Ya tambaye ni yana sanye da kayan bachi kalar nawa da ya saka min a lefe.

“Ka kwanta a kasa ko kuma ni na kwanta a kasan kai ka hau gadon”

“Ba wani abu zan miki ba Noor, ba zan miki komai ba”

Na ga gaskiyar hakan a muryarsa da fuskarta amman tsoro da yawan tunawa da maganar Aisha ya hana ni yarda da shi.
Chapter 3 · 0% Book details