Sashe 29
Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani abun da Kareem be sake yi ba shi ne hawaye. A gaban idonsa ran abokinsa amininsa abokin shawararsa ya fita. Ya saba ganin mutuwa ya saba sanar da ita ya saba jinta but this one is different mutuwar Hafiz ta yi hitting dinsa in a different way, na farko a lokacin da be yi tsammani ba, kuma a gurin wanda be sakawa ba, mutuwar Momy ta zo masa da sauki domin ta yi ciwo kamin ta rasu, and ko da yaushe tana yawan fadar zata mutu zata mutu tana kan tunatar da su idan sun manta. Amman abokinsa da yake lafiya kalau suka yi waya a hanyarsa ta dawowa har yayi masa alkawarin dawowa da Noor, ta yi hitting dinsa so so so bad. A hanyar da be yi tsammani ba, what a lost, this is a great lost to him ya rasa RAI BIYU within a year...
Ya rasa uwa ya rasa babban amininsa.
Har kara ma mutuwar Momy ya samu zubar da hawaye yayi kuka a lokacin da ya kebe kansa amman mutuwar Hafiz ta yi hitting dinsa in a way da ta tare hawayensa ta tare zuciyarsa daga kuka tun daga asibitin da mahaifinsa yake kuka har aka dauko gawarsa aka dawo da ita gida gurin iyayensa yan'uwa da matarsa suka rufe gawar da kuka shi kam ko kadan hawaye be kusanci idonsa ba. Kuma ta hana idanuwansa runtsawa a lokacin da ya kwana tare da gawar abokinsa domin yin masa sallama ta karshe.. Da kansa ya wanke abokinsa yayi masa sutura sannan aka jira wayewar gari domin kai shi gidansa na gaskiya.
Suna fitowa daga sallah azuba ya shiga cikin gidan ya tambayi mahaifiyar Hafiz ko an sanar da Noor.
“Aa ba a fada mata ba, jiya na tambayi Aisha ya ba su zo tare ba sai tace wai tana gidansu ta tafi kusan sati uku bata gidan”
“Ya kamata a sanar da ita, hakki ne a fitar mata da shi...”
“Aisha tace sakinta yayi, amman be fada mana ba, ko ka sani”
“Haka ne, amman tana da hakkin a sanar mata... Mama ki aika a daukota”
“Toh ko zaka tafi tare da Raliya sai ku taho da ita, tun da kai ka san gidan”
Yayi shiru kamar yace a a sai kuma ya amsa mata da kai ya ce Raliya ta tashi su tafi. Karfe 6am daidai suka faka a kofar gidan.
“Shiga ki musu magana”
“Tohm...”
Ta amsa tana kuka sannan ta bude motar ta fita.
NOOR POV.
Muna tsaka da tafiya sai na ga sun yi nisa sun bar ni, yana rike da hannun uwargidansa Aisha ita kuma tana rike da hannun yaranta. Gajiya ta saka na zauna a gurin da suka bar ni mai tsananin turbaya da jar kasa, sai dariya nake sun yi nisa sosai kamin Hafiz ya juyo ya kalleni a lokacin ne ya hankara bana tare da su sai ya rugo a ruje ya nufo inda nake yana rike da hannun Aisha ya karaso kusa da ni yana numfashi daker.
“Noor taso mu tafi...”
Ya miko min hannunsa sai na daga kai na kalleshi sannan na mika masa nawa hannun zai kama kenan kasar da yake tsaye akanta ta bude ta rusga da shi ya fada, sai ya bar mu a gurin ni da Aisha muna kallon ramen da ya fada, ita tana rike da yaransa ni kuma ina daga zaune a gurin domin be kai ga riko ni ba ya fada. Dariyar Aisha ce ta dawo da hankalina zuwa gareta kamin ni ma na fara dariyar sai na mike tsaye. Ban lura ba ashe saman wani tsaye nake tsaye mai tsananin tsawo da saka jiri. Tangal tangal na fara kamar zan fadi sai na ji wani ya rike ni ta dama, yana sakina ya fara tangal tangal wani ya rike ni daga hagu, yana sakina na sake komawa yar gidan jiya, sai kuma na ji an rike ni ta baya, kamin na ji wani dabam kuma ya rumgume ni a kirjinsa, a chest with full of hairy chest har yana shiga min baki.
.....Firrrrrrr gigit na farko daga bachin wahala da kuma mafarkin da na tabbatar ba na kwarai ne, domin mafarkin dariya yana nufin bakinciki ga mai yinsa sai dai ta inda ban fahimta me yasa ni da Aisha muke dariyar? Kuma su waye suke rike ni? Waye wanda na kwanta a kirjinsa. Tashi na yi na alwala na rama sallah sannan na gabatar da sallah asuba ina jin fuskata na min yaji saboda dukan da Yaya yayi min ya ji min ciwo a kumatu da gafen ido har ma da saman bakina. Na jingina kadan ina lazimi da hannuna na ji an buga gidanmu, Yaya ne ya bude bana jin me ake cewa amman tabbas na ji yana fadin.
“Eh tana nan”
Sannan ya kwala min kira na tashi da sauri da kuzari na fita gudun kar na yi laifi. A tsakar gidan na yi arba da kanwar Hafiz, domin Aisha ta gabatar min da su a lokacin da suka zo ina amarya haka ma a burin Walima mun hadu da juna. Hawayen da na gani a idonta ne suke min magana ba bakinta.
“Yaya Kareem yana waje ya ce ki zo mu tafi”
Na nufi kofar babu talkami a kafata na fice daga gidan zuwa kofar waje. Kareem ya na samu jingine jikin wata bakuwar mota ya rumgume hannayena yana kofar gidanmu.
“Hafiz ya rasu...!”
Na fada domin a yanzu na gama fahimtar mafarkina.
“Ban fada mata ba”
Na ji kanwarsa ta fada daga bayana. Juyowa na yi na kalleta.
“Na sani, na gani a mafarkina na gani jiya ya saki hannuna ya zo zai kama ni sai wani rame ya bude ya fada da shi, ya saki hannuna da na Aisha, ya tafi ya bar ni ina tangal tangal, wayyo Allah na, na shiga uku wayyo Hafiz...”
Na ruka zan kai kasa sai kanwarsa ta rike ni ni da ita muka fashe da kuka mai karfi.
“Karfe 8am za ayi masa sallah, you need to be there kamin a tafi da gawarsa”
Kareem ya fada ganin kukan na mu ba mai karewa ba ne. Yaya ya leko yana ganin Kareem ya gaishe shi, sai Kareem ya ce.
“Ka fadawa Baba Allah yayi ma Hafiz rasuwa jiya da dare, sakamakon hatsarin da yayi a hanyarsa ta dawowa daga Kano”
“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”
Yaya ya fada ya juya ya koma cikin gidan, Kareem kuma ya bude mana mota ni da ita muka shiga baya. Yanzu ta ina zan roki gafararsa ya tafi be fahimce ni ba, ina jiran tsammanin zuwa ko aikowa a dauke ni sai labarin mutuwarsa ya riske ni a yanzu.
“Ni ma tawa rayuwar ta kare...!”
Wannan kawai na iya furtawa ina kuka bayan haka ban sake fadar komai ba har muka isa gidan. Gidan ya cika tam da mutane amman ba cikar farinciki ba domin kowa kuka yake da jimami. Haka na fito motar babu talkami a kafata kanwarsa ta ja ni ta shiga da ni har gurin da gawar take. Sai ta ja ta tsaya daga bakin kofa ta ni kuma na kwance, yana kwance cikin kagara an masa sutura amman likkafaninsa yana jike da jini. Ban taba arba da gawa ba sai a ranar domin ban taba rasa kowa ba, ban rasa uwa ba ban rasa uba na ban rasa yaya ko kanwa ba. Ban san ya zafin abun yake ba, ban taba zauna a daki daga ni sai gawa ba sai yau. Ashe mijina ne farkon abun da zan fara rasawa a kananan shekaruna... Ban taba sanin idan mutum ya mutu abubuwan da kake masa marar dadi ne suke zuwa su tsaya maka a rai ba sai yau.
Yadda yayi ta kokarin kaiwa ga jikina ina hana shi da ihu da kokawa ne ya tsaya min a rai, ya saka ni fasa ihu ya saka ni rawar jiki, me yasa ban bari ya kai ga abun da yake halalinsa ba? Me yasa na biyewa Aisha da tsoro har abubuwa suka zo mana a haka? Ashe zaman ba mai tsawo ba ne ko da na zauna a gidansa ne. Wasu matane ne suka shigo suka fitar da ni, ina wani irin kuka da ban san ina yi ba, sai hakuri suke ba ni suna rarrashina amman ji nake kamar suna cewa bude baki ki yi kuka sosai Noor yau ranar kukanki ce.
Ni dai na san bana son Hafiz amman kuma ba kinsa nake ba, amman a ranar na ji tausayinsa kuma na ji tausayin kaina, ban gane haka ba sai da aka fito da gawarsa za a fita da ita domin yi masa sallah. Ban san ya aka yi ba na isa gurin na ratsa cikin maza na rike makara, ina kiran sunansa kamar ance zai iya amsa min. Daker aka banbare hannuna daga jikin makarar su kuka ni kuka ana rike ni aka fita da gawar mijina wanda shi ne duniyata a yanzu.
Ban kara raina kaina ba sai da aka kai shi gidansa na gaskiya aka dawo, maza suka shigo cikin gidan domin yi mana gaisuwa, ashe wata kalar azaba ake ji idan aka yi maka gaisuwar wanda ya rasu. Allah ya jikansa yayi masa rahama ya raya abun da ya bari haka kowa yake ta fada. Cikin taron masu yi mana gaisuwa Mama ta kutso ta shigo ta iso inda nake ta zauna sai ta saka hannunta biyu ta rika fuska.
“Yi hakuri Noor yi hakuri”