← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 82

Sashe 69

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hijabi na saka sannan na dauki takardar sakin da ban iya karantawa ba na saka a jaka na nufi kofar dakin na bude, sai na yi arba da doguwar takardar aje a kofar daki. Na duka na saka hannu na dauka a tunani Abdull ne ya aje min amman da na fara karantawa sai na tararda sabanin haka..

_Yar uwata noor, ban ci amanarki, ba zan taba iya cin amanarki ba, ba ki saurare ni ba, bakinciki be bari kin tuna da halina ba! Yadda kika dauki abun ba haka yake ba, Wallahi mijinki ya nuna min fin karfi ne, ya fara tallata min bukatarsa tun a lokacin da na bukaci tafiya gida kika hanani ne. A lokacin bana son fada miki ne saboda kar na zama silar lalacewar aurenki..._

Na hade yawu na nufi kujera na zauna.

_Da ya fahimci ba zan aminta ba, sai ya shirya min tarko, ranar Monday da muka fita da sunan zai sauke ni a hanya, sai ya biya da ni a wata tsohuwar ma'aikatarsu, yace min zai tafi ya duba wani abun ne, ban yi tunanin zai nuna min karfi ba ne, shiyasa ta yace na shiga wani office na dan jira shi, na jira har na gaji da zama be dawo ba da na fito sai na lura gurin babu mutane sosai, na tsorata da farko na dauka siyar da ni zai yi, ashe kudirinsa dabam ne. Na koma ciki na zauna jiransa har ya dawo, sai ya fara lallaba ni yana min kamfe da abubuwan da yake min na kyautatawa ashe ba dan Allah yayi min ba, da na nuna masa ba haka ya fara kokawa da ni, Wallahi na yi ina yadda zan iya na kare kaina Noor amman hakan be samu ba sai da ya biya bukatarsa, a ranar ban samu tafiya makaranta ba a gurin na wuni, sai da ya dawo aiki ya biyo ya dauke ni aje ni nesa da gidan na tako na iso da kafa sannan ya shigo_

Hawayena sun zuba jikin takardar na juya dayan shafin ina karantawa.

_Daga ranar ne ciki ya shige ni, tun daga lokacin yake bibiyata yana ba ni hakuri kuma yana lallaba ni ko zan amince amman ban amince masa ba, ba zan iya fada miki ba ne, saboda kar na zama silar lalacewar aurenki da na Mama na rumgumi a abun a matsayin kaddara. Shi da kansa ya ba ni abun auna ciki ya ce na auna idan babu ciki saboda kar mu ya bayyana mu ji kunya, kuma da na auna sai na samu akwai ciki amman ban san ko wata nawa ba ne, da na fada masa sai yace za a zubar amman sai na amince masa ya ci gaba da mu'alama da ni, da hakan ya ribance ni na amince saboda ina son a cire cikin kar ki gane, domin ya fada min ya san duk yadda zai yi ya wanke kansa ni ya bar ni a ruwa idan ban aminta ba, kuma gaskiya ya fada ni mace ce bayyanar cikin zai rusa rayuwata, shi kuma namiji ne, wanda ya riga ya gina rayuwarsa kaddarata bata isa ruguza komai ba_

Ya share hawayena ina kuka.

_Ki yi tunani mana Noor yadda dangi da iyaye suke murna da dan halak, haka suke bakinciki da na haram, na san Baba kashe ni zai yi idan ya sani, buri na yadda za a zubar da ciki ne ba tare da kowa ya ji ba. Kullum maganar da nake masa kenan kuma saboda haka nake amincewa da shi, shi kuma yana ga jan lokaci saboda biyan bukatarsa. Amman ni ba zan iya cin amanarki ba Noor zuciyata ba haka take ba, ba a mana wannan tarbiyarba, tsorona na lalacewar aurenki ne da na Mama, ba ki tsaya kin saurare ni ba, ban san ya zan miki bayani ba_

Na mike tsaye da sauri a lokacin da nake karanta sakonta na karshe.

_A lokacin da zaki samu sakon nan ki karanta bana gidanki, na bar gidanki Noor, kuma ba gida zan tafi ba, ba zan kaiwa Mama abun kunya ba, ba zan tafi da cikin shege gidan Baba ba, na san zaki fada musu dukan abun da ya faru a lokacin da zaki koma gida ko kuma aka neme ni aka rasa. Dan Allah ki fada musu gaskiya Wallahi ba da son na aikata ba, kaddara ce ta riga fata, zan tafi inda ban san kowa ba kuma kowa be san ni ba, na bar ku Noor ku yafe ni, musamman ke...!_

Na jefar da takardar na nufi dakinta da sauri ina kiranta.

“Hana Hana Hana...”

Na tura sai na samu dakin babu kowa, na fada bandaki nan ma bata nan, na fito da gudu na nufo gate ina tambayar mai gadi ko ya ga fitarta.

“Hana ai tun jiya da dare ta fita, misalin sha daya na dare”

Na fashe da kuka na bude gate din na fita da gudu kamar ance zan ganta. Na yi dama na kalli karshen Titi da babu mutane na juyo na yi hagu nan ma babu alamar sawunta. A gurin na zube na kwarara wani irin ihu da dukan karfina ina kuka har sai da abun da ke cikina na motsa....

Duk wanda ta karanta min littafi bata biya ba na barta da ALLAH. duk wanda ta yi min sharing paid pages na barta da ALLAH.

It's 500
Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660Na dauki awa hudu ina nakudar da ban san da zuwanta sai da muka tafi asibiti, na wahala iya wahala har na yi zaton rai zai yi bankwana da duniya ne.
Suka can na yi nishi na yunkura ina ta kokarina, amman kamar bana yi, ban yi zaton haka haihuwa take da da wahala da ciwon fa azaba ba sai da na kai matakin.

A lokacin da likitoci suka bada shawarar a shiga ni tiyata domin ceto rayuwata da rayuwar abun da yake ciki ganin na kasa haihuwar, na katse sosai na yi zaton idan ana shiga da ni ba zan fito da rai ba. Sun fada idan ba ayi haka ba zan iya samun matsala ko abun da ke ciki ya samu, domin haihuwar ce ta zo min babu abun da ya isa ya tare, ma'ana dai zan yi haihuwar bakwaini kamar yadda aka haife ni.

Cikin ikon Allah da rahamarsa kamin asuba wani karfin ya zo min, yunkuri daya biyu a uku kan yarinya ya fara fitowa, da na sake yunkurin ta kara fitowa, likitan da ya karbi haihuwata ya yanka gurin ya janyo babyn, azabar sai ta zame min kala biyu, ba ma kamar lokacin da ake dinkewa. Ko ba a fada min na sani yata bata so da rai ba, domin ban ji kukanta a lokacin da ta fado duniya ba. Sai dai ban tabbatar da sai bayan da aka min wanka aka gyara min jikina aka canja tufafina. Sannan Mama ta sake shigowa domin da taimakonta aka yi min komai. Ta shigo dakin da fuska a kumbure da alama ita ma ta yi kuka kamar ni.

“Sannu ya karfin jikin na ki?”

“Alhamdullahi”

Na amsa ina jin maganar ma kamar ba zan iya ba. Domin babu ragowar karfi a jikina kamar ba na da kashi haka nake ji.

“Mace kika haifa, amman bata zo da rai ba, na bada ita can gurin dangin mahaifinta, saboda Mahaifiyarki Abdull ta karba”

Abu ne da na riga na sani kuma na fahimtar da kaina. Amman da Mama ta fada min sai na ji wani irin babu dadi. Duk wahalar da na sha babyn bata zo da rai ba. Tea mai kauri Mama ta miko min na karba na sha rabin kofin sannan na aje sai ta miko min wayarta.

“Kin ganta nan”

Na karbi wayar na kalli hoton yarinyar mai kyau da jiki kamar ba yar wata bakwai ba, fara kyakkyawa kamar na kirata ta amsa amman babu rai, an lullube ta da zane gwanin sha'awa.

“Yi hakuri, Allah ya baki wata mai albarka, ita kuma Allah yasa mai ceto ce, na tsorata da nakudarki kin wahala har hankalina ya tashi”

Na share hawaye na mika mata wayarta.

“Mama baki ga waya a jakata ba?”

“Na gani, kuma na ga kira na amsa sai na ji muryar abokiyar zamanki wai zaki kashe mata aure Wallahi sai ta ga bayanki, da ta ji muryarta ina mayar mata da martani sai ta kashe bata sake cewa komai ba, fada kuka yi?”

Ta banbare magani ta miko min na karba na sha.

“Aa ba ni wayar na duba abu”

Ta bude jakarta ta dauko wayar ta miko min, sannan ta dauko ragowar tea da na aje ta ba ni.

“Daure ki shanye Noor kamin anjima sai ki ji jikinki ya sake, wata kila zuwa gobe su sallame ma idan ba wata matsalar ta biyo ba, yau dai sun ce zaki wuni a nan ki samu bachi”

Ba tare da na musa ba na karba na shanye na aje cup din sannan na duba wayata ko zan ga sakon Hana amman shiru.

“Ina kika bar Hana ya aka yi kika zo a tare da ita ba? Na kira wayarta kashe mijinki kuma na yi ta kira be daga ba, shiyasa na kira kanwarsa da uwargidanmu na fada musu, su suka kira mahaifiyarsa suka fada mata, kanensa ma jiya duk suna nan mahaifiyarsa kuma a nan ta kwana, ita ta tafi da jaririyar ma, shi din ne dai be kira ba”

Wata zuciyar tace na yi mata karyar cewar Hana tana makaranta shiyasa ban zo tare da ita ba. Sai dai tunawa da shawarar da Kareem ya ba ni ya saka na yanke shawarar fada mata gaskiya.

“Daman kin ji alamar haihuwar ne kika dawo? Ai kara da kika yi haka a can babu kida kowa sai Hana ita kuma yarinya ce ba sani komai kuka yi ba, ko da yake likitoci ne suke yin komai, amman dai hankali ba zai kwanta ba kara da kika haihu a gida”

Na daga kai a hankali na kalli fuskarta, wani tea take kokarin hada min.

“Mama”

“Na'am”

Ta kalleni.

“Hana bata tare da ni”

Ta kalleni da sauri.

“Kamar ya?”
Chapter 69 · 0% Book details