Sashe 55
Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kawai dai na tambaya ne, saboda na sani kamar yadda ita ma ta san cewa dan da na haifa yanzu naka ne”
Ya kalleta without blinking try to connect his heart with his brain.
“You're stupid...”
Ta yi murmushi
“Yau har na kai haka? Lallai Kareem kai ba dan goyo ba ne, cikin kanen lokaci ka canja min, gaba daya yarinyar nan ta dauke maka hankali, haka mijina yanzu ba shi da lokaci na”
“Daman mijinki be taba lokacinki ba, dan haka karki zargi Noor, idan ya koma garin da yake manta ki yake yana can yana sha'aninsa kina na ki”
“Muna na mu dai”
Ta gyara masa tana kallon idonsa cikin bakin rai.
“Me yarinyar nan ta tare miki ne wai? Baki da magana sai na ta”
Ta zagayo Inda yake yana ganin hakan ya mike tsaye.
“saboda ita ta kwace min kai, a rayuwa kai ne kadai mutumen da zaka nesanta da ni, azabar son ka ta azabtar da ni na kasa hakuri da kai, da ba haka kake ba, amman zuwan yarinyar gaba daya ka sauya min kuma ka kwashe sirrinmu gaba daya ka fada mata, har tana yakata da shi, baka jin kunyar mu'alama da mata har biyu? Bayan karyar da ka yi min akan Yusura?”
“Ban taba hada shimfida da Noor ba, kuma ba zan taba ba har abada, indai har sai ta kazantacciyar hanya zan samu Noor, to ina rokon Allah ya hana min ita har abada, kuma aure take a yanzu bana fatan ya mutu, fatana ta samu kwanciyar hankali a ko'ina zata kasancewa?”
Ta dan matsa baya.
“Baka taba kaiwa jikinta ba? To me ya dauke hankalinka ka fada mata sirrinmu? Ba na mu'alama kadai ba wai har na haihuwar da muka yi?”
“What? You're not serious? Taya za fada mata abun da ba ayi ba?”
Ta matso kusa da shi tana kallon wayar idonsa.
“Miye ba a ayi ba a ciki? Haihuwa ko alaka?”
“Na ji na fada mata alaka, amman yaushe muka haihuwa balle na fada mata?”
“Yanzu kuma kokarin wasa kake da hankalina?”
“Wane irin wasa da hankali? Karya kika mata cewar mun haihu ne? Idan ma kin yi haka to kin yi akan aurenki ne kina kashe kanki ne, domin Noor baki ba linzami ce”
Ta kalli gefe sannan ta sake kallonsa.
“Taya zan fada mata sirrina? Kai ka fada mata, shiyasa da ta zo gidana ta fada min magana son ranta”
Ya fisgota ya rike cinyar hannunta.
“Stop talking about Noor, yaushe muk haihu? Are you out of your mind?”
Ta fisge hannunta.
“Ai na fada maka tun ina da ciki ko? A asibitin nan aka karbi haihuwa danka, kuma Wallahi jininka ne! Au kenan baka yarda ba da na fada maka? Ka dauka karya nake?”
Kareem ya daka mata tsawa.
“Yaushe rabon da na yi wani abu da ke? Akwai dai abun da kike kokarin yi Safeena”
“Babu abun da nake kokarin yi, ni ba zan iya cutar da kai ba, amman ďan da na haifa yanzu Wallahi naka ne, last haduwar da muka yi na samu cikin, sati biyu na kara akan lokacin da nake period a satin Abdull ya dawo, yana barin garin nan naje aka min test aka ce ina da ciki dan sati uku, yaron da na haifa yanzu idan aka kalleshi kallon kurilla za a san cewar danka ne, idan baka yarda zan kawo shi ka gwada jininsa”
He lost his temper when he was saying.
“Baki da hankali Safeena? Taya zaki aje ciki i mean taya zaki haihu? Dan Haram ne Safeena kuma ki dauka ki kawai mijinki? Ina da aure da yaya safeena kina da aure da yaya taya zaki yi haka?”
Ya fadi zaune yana rufe bakinsa.
“I don't believe you?”
“Na kawo maka yaron ka auna?”
Ya kalleta.
“Idan gaskiya me ye hujjarki na aikata haka?”
Ta risina a gabansa.
“So so ne, Kareem ina kaunarka ba zan iya zubarwa ba, ko da ba zan same ka ba zan so aje jininka, kuma waya sani ko nan gaba mu kasance ma'aurata”
“Ina zamu kai zunubin Safeena? Ga na zina ga na daukar alhaki? Mu dauki alhakin yaron mu dauki na mijinki? Why how? Why why why Safeena why?”
“Ni ma bayan na haihu na yi tunanin be kamata mu yi haka ba, amman komai ai ya riga da ya faru, kuma ba a kanmu farau ba, suna nan da yawa yaran da ba na iyayensu ba”
Ya kalleta babu alamar wasa ya ce.
“Je ki dauko yaron”
Ta mike tsaye ta dauki jakarta ta fice daga office din. Fuskarsa ya shafa yana jin gumi na karyo masa, daman da ta fada masa tana dauke da cikinsa gaskiya ta fada? Ya dauka tana masa wasa ne ko barazana shiyasa ta dawo asibitin. Kuma tun bayan rabuwa da ita be sake bincikarta komai ba saboda yana tunanin ya yanke alaka da ita.
Ya mike tsaye yana jin kamar baya iya numfashi.
“I can't believe this ba gaskiya ba ne, Kareem”
Ya fadawa kansa yana nufar windows din ya rika gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Juyowa yayi da karfi ya dauki keys dinsa ya fice daga restaurant din gaba daya. Gurin aikinsa ya koma, ya kira waya ya sanar mata inda yake, a can Safeena ta kai masa yaron mai cike da koshin lafiya mai jiki da haske gwanin sha'awa. Tun da Safeena ta aje yaron yana kallonsa gabansa na faduwa domin ya ga kamaninsa a fuskar yaron, ta dayan gefen kuma yana kama da Safeena.
Be ce mata komai ya fita office din, babu jiwa ya dawo sanye da safar hannu ya debi jinin yaron a syringe.
“Idan har abun da kika fada ya tabbata Safeena kin cutar da ni, kin cutar da kanki kuma kin cutar da yaron nan”
Ta kalli yadda yake kuka bayan Kareem ya dauki jininsa ta ce.
“Abu ne da zamu iya ajewa, mijina be sani ba, matarka bata sani ba, to mu bar shi a boye mana, sirrinmu ne ai”
Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din. Tun tana jiran dawowarsa har ta gaji ta tashi ta fita. Be bar asibitin ba sai da ya debi nashi ya hada ya kai laboratory suka auna masa. He wait they sai da aka hada results aka ba shi. Tsoron abun da zai gani ya saka shi kasa duba takardar har ya shiga motarsa.
Ta zauna a motar na tsawon awa daya yana tunanin yadda rayuwa zata kasance masa a yanzu, idan har ta tabbata dansa ne, idan a gurin wasu ba abun kunya ba ne shi a gurinsa abun kunya ne. Daker ya ja motar ya fice daga asibitin, be yi nisa ba ya faka gefe titi ya kai hannu ya dauki result din ya duba. Booom..... Zuciyarsa ta buga da karfi, gaskiya Safeena ta fada, dansa ne jininsa ne.
“Why Safeena Why?”
Na hade takardar da karfi ya yaga ya jefar ya bugu sitiyarin motar da karfi, ya bude motar ya fita ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya dawo ya halbi motar da kafarsa. Ya jingina ya rufe ido ya zai yi? Me yasa ya aikata tun farko? Yaya kenan yanzu? Ya bude motar ya shiga ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ya rufe ido. Be daga ba sai da lokacin sallah magariba yayi, a wani masallaci dake kusa da gurin yayi sallah Magariba ya kasa fitowa masallacin har aka yi sallah Isha'i. Sai kusan Tara da rabi ya doshi gidansa.
Yana driving yana jin kamar kar ya tafi, kunya hada ido da iyalinsa yake duk kuwa da kasancewar ba su san komai akai ba. Harabar gidan ya faka ya kwanta a motar ba bachi yake ba tunanin yadda zai tafi da wasu abubuwa yake. Yana tuna shawarwarin da abokinsa ya ba shi lokacin da yake raye. Da kuma yadda zuciya ta debi shi ta saka idonsa ya rufe a lokacin ya kasa fahimtar illar da Zina zata yi a rayuwarsa.
Ya sani duk wani abu da Allah yace kar a kusance shi, ba abu ne mai kyau ba. Ba ma karku aikata ba kar ma kusanci inda take balle har ku aikata haka Allah ya fada, amman ya take sanin ya murje ido ya aikata, yanzu wa gari ya waya? Kamar zai fadi haka ya bude motar ya fito jikinsa babu kuzari. Sai da ya daga kansa sama ya kalli gidan gabas da yamma sannan ya taka ya isa bakin kofar falon ya shiga.
A hankali yake takawa har ya haura sama, dakin yaransa ya fara turawa sai ya samu suna bachi an kashe wutar dakin an kunna musu ocean, sakin kofar yayi ya shiga cikin dakin dakin ya zauna kusa akan gadon Tine yana kallonta kamin ya juya ya kalli Areef.
“Maybe nan gaba ku ji kun tsane ni, idan ina raye ko a mace, ku yi bakinciki da na kasance ubanku, kuna da yancin yin haka, domin na bar muku abun kunya, bayan ni kuma nawa iyayen ba su bar min abun kunya ba, sun yi kokarin tsare mutuncinsu da na mu”
Ya hade yawu.
“Ni dai na san ba zan kashe yaron nan ba, duk wani abun da zan biyo baya dole na karbe shi domin ni na aikata, but no matter what ku sani ina matukar kaunarku kuma ina kokarin na tsare mutuncinku, saboda kar na lalata Future dinku”
Ya shafa kan Tine ya sumbance ta, sannan ya tashi ya nufi dayan ma ya shafa kansa ya sumbance shi, ya kallesu cike da bakinciki sannan ya fice daga dakin ya ja musu kofa. Dakinsa ya shiga, yadda ya shigo sanye da talkami da kananan kaya haka ya fada saman gadonsa ya rufe ido, ko agogonsa be iya cirewa ba. Haka ya kwanta har safe ko kadan be yi bachi ba, sai juyi yake idan ya gaji da kwanciyar sai ya sauko kasa ya zauna.