← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 82

Sashe 67

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Daga ranar ne ciki ya shige ni, tun daga lokacin yake bibiyata yana ba ni hakuri kuma yana lallaba ni ko zan amince amman ban amince masa ba, ba zan iya fada miki ba ne, saboda kar na zama silar lalacewar aurenki da na Mama na rumgumi a abun a matsayin kaddara. Shi da kansa ya ba ni abun auna ciki ya ce na auna idan babu ciki saboda kar mu ya bayyana mu ji kunya, kuma da na auna sai na samu akwai ciki amman ban san ko wata nawa ba ne, da na fada masa sai yace za a zubar amman sai na amince masa ya ci gaba da mu'alama da ni, da hakan ya ribance ni na amince saboda ina son a cire cikin kar ki gane, domin ya fada min ya san duk yadda zai yi ya wanke kansa ni ya bar ni a ruwa idan ban aminta ba, kuma gaskiya ya fada ni mace ce bayyanar cikin zai rusa rayuwata, shi kuma namiji ne, wanda ya riga ya gina rayuwarsa kaddarata bata isa ruguza komai ba_

Ya share hawayena ina kuka.

_Ki yi tunani mana Noor yadda dangi da iyaye suke murna da dan halak, haka suke bakinciki da na haram, na san Baba kashe ni zai yi idan ya sani, buri na yadda za a zubar da ciki ne ba tare da kowa ya ji ba. Kullum maganar da nake masa kenan kuma saboda haka nake amincewa da shi, shi kuma yana ga jan lokaci saboda biyan bukatarsa. Amman ni ba zan iya cin amanarki ba Noor zuciyata ba haka take ba, ba a mana wannan tarbiyarba, tsorona na lalacewar aurenki ne da na Mama, ba ki tsaya kin saurare ni ba, ban san ya zan miki bayani ba_

Na mike tsaye da sauri a lokacin da nake karanta sakonta na karshe.

_A lokacin da zaki samu sakon nan ki karanta bana gidanki, na bar gidanki Noor, kuma ba gida zan tafi ba, ba zan kaiwa Mama abun kunya ba, ba zan tafi da cikin shege gidan Baba ba, na san zaki fada musu dukan abun da ya faru a lokacin da zaki koma gida ko kuma aka neme ni aka rasa. Dan Allah ki fada musu gaskiya Wallahi ba da son na aikata ba, kaddara ce ta riga fata, zan tafi inda ban san kowa ba kuma kowa be san ni ba, na bar ku Noor ku yafe ni, musamman ke...!_

Na jefar da takardar na nufi dakinta da sauri ina kiranta.

“Hana Hana Hana...”

Na tura sai na samu dakin babu kowa, na fada bandaki nan ma bata nan, na fito da gudu na nufo gate ina tambayar mai gadi ko ya ga fitarta.

“Hana ai tun jiya da dare ta fita, misalin sha daya na dare”

Na fashe da kuka na bude gate din na fita da gudu kamar ance zan ganta. Na yi dama na kalli karshen Titi da babu mutane na juyo na yi hagu nan ma babu alamar sawunta. A gurin na zube na kwarara wani irin ihu da dukan karfina ina kuka har sai da abun da ke cikina na motsa....

Duk wanda ta karanta min littafi bata biya ba na barta da ALLAH. duk wanda ta yi min sharing paid pages na barta da ALLAH.

It's 500
Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660Be dade da kwanciya ba na ji nishanrinsa alamar bachi mai nauyi ya dauke shi. Juyowa na yi na kalli kwanciyarsa, ina mamakin karfin hali irin na ďa namiji a haka kuma yake kallo muna ta rayuwa a gidan kamar babu komai a tsakaninsa da Hana. Sallah bata wani dame shi ba daman ni ce mai tashi da wuri na yi, dan haka na sauko da kafafuwana kasa na nufi bandaki, wanka na fara yi sannan na yi alwala na fito sanyin ruwan da kuma ac dakin yana ratsani sai ya saka na dan ji sassauci a jikina.

Na zuciya kan na san har abada ba zan samu ba. Ni da farinciki mun yi bankwana. Doguwar riga na zuba na shimfida sallaya na sauke farali sannan na fara tasbihi. Ban daga sallayar ba har sai da na ji farkawarsa misalin bakwai na safe.

“Miyasa ba ki tashe ni ba gashi rana ta yi”

“Ni ma ban farka da wuri ba”

Shi kawai na iya amsawa na koma saman gadon na kwanta na lafe kamar mai bachi, domin har lokacin ban san me zan yi ba. Na nuna musu an san komai na rufe su da fada ko kuma na danna na barwa zuciyata komai na bar su da Allah? Amman zan yi? Ina jin abun kamar ba shi da sauki, ina jin zaba da radadin cin amanar da yar'uwata ta yi min fiye da kunar garwashin wuta. Ina jin da ya taba ni yana fadin.

“My soul ta so muje mu yo breakfast”

“Sai anjima bana son komai yanzu”

Na amsa hawaye na min zuba yayin da fuskata take lullube a cikin bargo.

“Okay, ba ki da lafiya ne?”

“Lafiya kalau bana son damuwa dan Allah ka tafi”

“Okay.. I'm sorry dear...”

Ya fice daga dakin sai after like 40m ya dawo yayi shirin office.

“Bachin be ishe ki ba kenan? Ni zan wuce aiki sai na dawo”

Bance masa komai har ya fita. Sannan na tashi zaune gaba daya na rasa me zan yi kaina ya daure abun yayi min muni. Sauka na yi saman gadon na fito falo na nufi windows ya na daga curtain ina kallon motar da Abdull ya shiga Hana kuma ta bude front seat ta shiga ta zauna. Hawaye ya sauko min a haka suke kallona? Yar'uwata ta zama kishiyata ta san sirrina ta san komai akan mijina.

Kusan a falon na wuni ina ta yawo ya kasa sukuni na rasa kalar tunanin da zan yi, kamin na samu natsuwar yankewa kaina shawarar da nake ganin ta dace da ni. Bayan ruwa ban iya sha ko cin komai ba har karfe biyu ta yi na rana na je na yi sallah na fito falo na zauna ina jiran dawowar Hana, domin ita ce mai dawowa da wuri Abdull sai biyar ko shida yake dawowa gidan. Na bata awa daya a zaune sannan ta turo kofar falon ta shigo da sallama na amsa mata ba tare da na bari ta kalli ido na.

Domin na yi kuka har idon ya kumbura, kai tsaye ta wuce dakinta, kaya kawai ta canja ta fito ta nufi kitchen kamar yadda ta saba sai na bi da kallo wai yanzu ita ma tana dauke da ciki kamar yadda nake dauke da shi kuma cikin mutum daya. Sai da ta shiga ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ta tambaye daga can kitchen din.

“Noor me za a dora”

Na mike tsaye na nufi kitchen din na shiga, sai na zame ta tana yanka lemu zata sha sai dai gani na ya saka ta tsayar da yankan da take.

“Lafiya? Me ya samu idonki?”

“Kuka na yi”

Ta aje lemun da wukar ta matso kusa da ni.

“Kuka dai? Fada kuka yi da Ya Abdull ne ko baki da Lafiya?”

Na kalleta ina mamakin yadda take nuna min kulawa kamar ba zata ci amanata a bayan idona ba.

“Na san muna samun tsabani Hana, amman ina sonki ina sonki sosai, zuciyata bata taba raya min na cutar da ke ba, ni ba zan iya?”

“Me ya kawo wannan maganar Noor?”

“Ina tunanar da ke ne idan kin manta, Wallahi Hana ko rayuwata kika ce kina so zan iya baki, balle mijina zan iya mallaka miki Abdull mallakawa ta har abada Hana, Wallahi zan iya yin duk yadda zan yi na ga ya sake ni in ya so sai ki aureshi”

Ta matsa baya tana kallona cikin tashin hankalin da ya bayyana a fuskarta.

“Me Abdull ya fada miki? Wallahi sheri yayi min”

“Babu wanda ya fada min komai, ni na ji da kunena, na kuma gani da idona, kika hada kai da mijina yana ba ni maganin bachi saboda yayi tarayya dake”

Ta daga hannu biyu tana yi min rantsuwa.

“Wallahi Wallahi Wallahi Noor ban hada kai da shi ba?”

Na daka mata tsawa.

“To me yake zuwa yi dakinki? Kullum sai ya ba ni maganin bachi na sha sannan ya tafi dakinki kishiyata ce ke?”

Ta girgiza kai tana kuka.

“Aa amman ba yadda kika tunani ba ne, Wallahi ni ban ci amanarki ba, Wallahi Noor ba son raina ba ne”

“Haka ne, shiyasa ai yake tafiya dakinki har kuna hira kina tambayarsa yaushe za a zubar da ciki, ina dauke da cikinsa kina dauke da cikinsa wane irin wulakanci da kaskaanci ne wannan?”

Ta zube kasan guiwoyinta tana kuka.

“Na shiga uku dan Allah Noor ki yi hakuri ki fahimce ni”

“Wace fahimta zan miki wanda ta wuce wannan? Ko karya nake baki dauke da cikin Abdull ba ki tarayya da shi?”

“Gaskiya ne ina dauke da cikin ina tarayya da shi, amman ba ta yadda kike tunani ba ne, ina son dan Allah ki fahimce ni”

“Toh ina jinki fahimtar da ni”

Ta kasa magana sai kuka take daman ai ba zata iya magana ba, tun da bata da kalaman da zata wanke kanta da su a gurina.

“Tun yaushe kuke cin amanata?”

Nan ma ta kasa magana, sai na matsa kusa da ita na tabbatar mata da abun da shi ne tabbbatacce a zuciyata.

“Na bar miki Abdull har abada, na bar miki Hana, yau ba zan kwana da aurensa ba”

Na wuce na shige dakina na fada kan gadona ina kuka mai karfi. Abincin da bata girka ba kenan ni kuma ban sake fita dakin ba sai da na ji motar Abdull. Tsanar hada ido da shi ne ta saka na fice daga dakin na nufi kitchen na tsaya a cikin har ya shigo.

“Bacchi kuke ne?”
Chapter 67 · 0% Book details