← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 82

Sashe 18

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Haba ke kuwa taya Kareem zai yi soyayya da wata yarinya, yana da damar aurenta kuma sai ya ki aurenta ya saka abokinsa ya aure ta? Daga baya kuma ya zo yana bibiyarta? Wane irin ƙidahumi ne ni? Ai da abun da aka fada miki ne ya faru to sai dai na aurota na kawo nan mu sha soyayya”

Abu ta hade da karfi ta juya ta haura sama ta barshi a gurin tsaye. Ta wani bangaren baya ganin laifin abun ta aikata domin gidanta suka shigo kuma neman mijinta, ta gurin da abun zai daure masa kai ace tana kishinsa domin abun da ake so ake kishi, shi kuma be saka ran samun haka daga gurin Yusura. Isakar bakinsa ya busar ya nufi dakinsa ya wayarsa ya dauka ya kira Hafiz.

“Hello...”

“Barrister kana gida?”

“Ina gida lafiya?”

“Zaka iya fita waje mu yi magana”

“Okay....”

Shiru na 2 minutes ne ya shiga tsakani kamin Hafiz ya amsa daga dayan bangaren.

“Ina jinka”

“Kun sake yin fada da Noor ne?”

“Daman ba fada muke ba, kawai dai na turata gidansu ne yau?”

“Saboda me?”

“Tana bukatar a koyar da ita zamantakewar aure Kareem, ba zan Boye maka ba na fara nadamar auren yarinyar nan!”

“Subhanallahi, to maybe wani abun ya faru a gidansu ko kuma bata tafi gidan ba, ta zo gidana by mistake Yusura ta fasa mata kai yanzu haka dai tana asibiti”

Hafiz yayi shiru kamar ba zai ce komai ba.

“Dan Allah kaje ka sameta kuma ko miye a tsakaninku ka yi hakuri mana Hafiz, hankalin Namiji baya zama daya da mace, kuma san halin mahaifin yarinyar yana daga cikin dalilin da ya saka ka aureta saboda ka tsamota daga kunci, to miyasa ba zaka jure ba kana lurar da ita har ta fahimta, ba mamaki mahaifinta korarta yayi ta rasa gurin zuwa ta zo nan, ni kuma ban ma sani ba sai fitowa na yi na samu Yusura ta yi mata aika aika, kuma kai ya kamata na kira domin responsibility dinta yana kanka as her husband don't misunderstand the issue please”

“Tana ina yanzu?”

“Tana asibitinmu, emergency room 44, please ka sassautawa yarinyar nan Hafiz duk yadda kake tunanin hankalinta be kai can ba, a yanayin yadda na fahimta ta tashi a wani yanayi ne na rashin dace da iyaye shi ne musabbabin komai, idan ka hada mata zafi iyayenta suka hada ma za ku iya sakawa ta kamu da depression domin bata da mai rarrashinta bata san gurin da zata tafi ta ji sanyi ba, ta yi kankanta ace ta fara samun matsalar aure tun a yanzu, and idan bata samu kwanciyar hankali a gidan ka ina zata samu? Already ta rabu da wanda take so, idan ta rabu da kai iyayenta za su iya juya mata baya, idan a gidanka bata jin sanyi kashe kanta kuke son ta yi? Kai da kanka ka ce za a iya koya mata son wani, to ka koya mata mana, ka nuna nata gurin da illar abu yake da sannu zata gyara”

Hafiz ya ki ce komai ba, sai wani cika zuciyarsa take duk abun da Kareem yake fada shi wani abun yake hangowa can dabam.

“Good Night”

Kareem ya kashe wayar ya jefar kan gado ya sauke dogon numfashi.

“Poor girl”

Ya furta, ya zauna bakin gadon yana jinjina kai.

NOOR POV.

“Good Morning...”

Na ji wata matar da ban taba arba da kalar fuskarta ba ta fada tana yi min murmushi. Yunkurin tashi na yi zaune sai ta rika ni na zauna na sake dubanta da idanuwa da ba su gama budewa ba.

“How are you feeling now?”

Na daga mata kai ina jin kamar an dora min wani dutse a gefen kaina saboda nauyin da yayi min. Hannu na kai na taba sai na ji an daure gurin, gefen wuyana ma an saka min wani abu a gurin sai ciwo yake min.

“Ya jikin na ki?”

“Da sauki”

Na amsa ina kallon dakin da ban san lokacin da aka kawo ni ba. Gashi babu kowa a kusa da ni sai wannan nurse din da ba musulma ba domin sakar cross ce a wuyanta sai gashin doki da ta dora. Ta taba jikina ya cire robar ruwan da be kare ba sannan ta yi rubutu akan files din dake hannunta tana min tambayoyi, sunana umguwata ina da aure ko babu sai kuma number wayar Mijina ko ta mahaifina, da alama dai sabon file take bude min a yanzu. Sai da ta gama sannan ta saka hannunta aljihu ta ciro wata takarda ta miko min.

“Ga wannan mijinki yace idan kika tashi a baki”

Na mika hannu na karba, a gabanta na fara warware takardar har na bude.

“A yau 2 ga watan 6 ni Hafiz Abdullahi na saki Matata Noor saki daya”

Shi ne a rubuce, gashi sunana da nasa ne a rubuce balle na ce kuskuren fahimta aka yi aka ba ni abin da ba nawa ba.

“Wayyo Allah.. Na shiga uku na lalace, wayyo ni Allah me yasa Hafiz zai sake ni yanzu na shiga uku, yanzu ina zan je? Wayyo Allah... Baba kashe ni zai yi, yanzu korata za su yi, na shiga uku”

Na kalli matar ina kuka mai taba zuciya.

“Dan Allah ki kira min shi”

“Ya riga ya tafi, but bari na kira Doc abokinsa ne ai sosai”

Ta fita dakin, sai na sauko daga kan gadon i don't even care about the pain haka na zube kasa kaina ya sake buga da gadon asibitin ina wani irin kuka, domin na san karshena ya zo, matar bata dade ba ta dawo ta miko min waya.

“Ga Doctor zai yi magana da ke”

Na karbi wayar da sauri na kara a kunne na saka hannu na dafe.

“Noor sakinki yayi?”

“Ya sake ni Kareem, rayuwata ta kare Baba zai iya tsine min ma, ba za su fahimta ba, dan Allah ka taimaka min ka ba shi hakuri, ka ce yayi hakuri ya maida ni gidansa ya yafe min, ka ce masa zan zauna a haka ba zan sake kai kararsa wani gurin ba, Kareem ka ba shi hakuri dan Allah ya hakura ya maida ni...”

Ina maganar ina kara matse wayar a kunnena ji nake kamar yana tsaye a gabana ne na kama kafafuwansa na bashi hakuri, domin ni kadai na san halin da zan shiga a sakin nan da yayi min.

“Ba zan ba shi hakurin ba”

Ta cikin wayar Kareem ya daka min tsawa ya kashe wayar. Na kalli matar da bana iya ganin fuskarta a yanzu saboda hawaye ya tare ko'ina na idona.

“Ya kashe... Ya kashe... Sun ruguza min rayuwa, sun raba ni da mai so na tsakani da Allah mai kaunata mai fahimtata mai tausayina, yanzu kuma sun hada ni da mahaifina shikenan rayuwata ta kare wayyo Allah na ni Khadija, Allah ba ni da gata sai na ka...”

Nurse din ta dafa ni.

“I'm sorry... Please take heart”

Na kwanta jikinta ina kuka sosai kamar zan mutu, ni kadai na san waye mahaifina ni kadai na san halin da zan shiga. Da sauri na dago daga jikin matar mai sanyin hali na fara share hawaye, so nake na tafi na samu Hafiz a duk inda yake na ba shi hakuri ya maida ni gidansa...

#KhadeejaCandyPAID PAGE 1️⃣1️⃣

©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....

You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153

_______•••_______

KAREEM POV

Fuskarsa a hade yana tsaye gaban madubi yana kokarin saka agogonsa Yusura ta turo kofar dakin ta shigo. Be dago ya kalli kofar ba amman hakan be hana shi fahimtar ita dince ta shigo dakin ba. Tsayawa ta yi nesa da shi ita dai fuska babu annuri ta ce.

“Ina kwana?”

“Lafiya Kalau”

Ya amsa a taikaice sannan ya fuskanci madubin da kyau ya dauki turare ya fara fesawa.

“Ka ce zaka yi shawara, zaka duba lokacin da ya dace ka aiwatar da abun da zai bawa kowa yanci a tsakaninmu, har zuwa yaushe ne Kareem”

“Abokiyar shawarata wadda ta bani shawarar aurenki ko na ce umarni bata duniya, amman zan yi shawara da Daddy tukuna”

Ya danna abun da ta ji yana taso mata a zuciya.

“Har zuwa yaushe kenan? Tsawon shekarun da muka yi da kai ina numfashi ne cikin matsuwa, ina ta jiran ranar samun yanci”

Kwalbar turaren ya aje ya juyo ya kalleta.

“Na fiki shiga kangin na takura da kunci, da kin san matsalolin da aurenki ya janyo min wata kila, kin shiga daki kin rufe kanki kin yi kuka, Yusura na rasa natsuwata, na rasa farinciki, rayuwar da nake buri ko mafarkin yi aurenki ya ruguza ta, ba ke kadai ba ce a dakin damuwa, ni ma yancin nake nema, i deserved happiness too ba kullum bakin ciki ba, so please karki matsa komai a sannu yake zuwa, kuma zan fi jindadi idan kika daina shigowa dakina kamar yadda kike yi tun farkon zamanmu, bincikar kayana ko bibiyar rayuwata ba na ki ba ne. And ki daina biyo ni har daki da abinci, a dinning ma ya isa idan ina ra'ayi zan ci a can... Please excuse me... ”

Ya zagayeta ya fice daga dakin, binsa ta yi da kallon ita kadai ta san yadda take danne zuciyarta take rayuwa da a gidan, amman yau ya kalli idonta ya fada mata magana son ransa.

“You got to be kidding me... I'm doing all this saboda na sauke hakkina da Allah ya dora min, waya fada maka a cikin dadin rai ko neman kauna nake? I need space...”
Chapter 18 · 0% Book details