← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 82

Sashe 2

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ji babbar tana fada, sai ya daga Haulat din ya dora a cinyarsa.

“Haulatu kin fara jin yunwa?”

Ta daga kai.

“Na san halinki ai sarkin cin abinci, daman ke kina rigan kowa karyawa acici”

Kannen suka saka dariya. Sai ya kalleni a yayin da ya mike tsaye yana dauke da karamar.

“Anty zo muje ki gaishe da yayarki ko ki yi mata ya jiki”

Na mike tsaye na dauki mayafina na saka sai Ikram ta kama hannuna hakan ya saka na dan ji kwarin guiwar tafiyar, yana gaba da yaransa biyu ni kuma ina daga baya tare da Ikram, har muka shiga bangaren matarsa wanda ya kasance iri daya da na nawa bangaren sai dai nata furnitures din da komai ya fi nawa kyau, a kudi kuma kana kallo zaka san nata ya fi nawa tsada nesa ba kusa ba. Hoton Hafiz da na yaranta da nata a naka manne a falon, wani gurin sun yi a tare wani gurin ita da yara wani gurin kuma shi da yara dayan kuma yaran ne su kadai aka yi ma hoton. Uwar daka muka shiga wato bedroom muka shiga, shi ya fara sallama sannan ni ma na yi na shiga. Zaune na hangota kafafuwanta a kasa, sam bata yi kama da mai aljannu ba, haka kuma bata yi yanayi da marar lafiya ba, sai dai tsoron aljannu ko mutane masu aljannu da nake ya hanani karasa kusa da ita, sai na zauna a kujerar dake kusa da kofar ina kallonta, shi kuma ya karasa ya zauna kusa da ita.

“Ina kwana?”

Ta yi min murmushi kamar yadda ta saba sannan ta amsa.

“Kin kwana lafiya Amarya? Ya bakunta?”

“Alhamdullahi”

“Madam ya jikin?”

Ta kalleshi tana wani irin lumshe ido ta bude kamar karuwa.

“Alhamdullahi ango”

Ta fada babu ko kishi sai ma murmushi da yake fuskarta. Ta kalli yaranta.

“Ku tafi falo, Abba zai zo ya hada muku breakfast yanzu”

“Okay”

Suka tashi suka fice daga dakin har karamar dake jikinsa. Kamar ficewarsu kawai yake jira sai ta kwantar da kanta a kafadar Hafiz tana kallona.

“Amarya karki ji haushi, dan Allah ki yi hakuri, jiya na kasa rike zuciyata ne shiyasa na yi kuka a gabanki ashe kuma wani abu zai biyo baya, bayan haka ban ma san na yi ba sai kusan azuba nan na samu kaina, uanzu haka jiri nake ji ina son na shiga bandaki na kasa”

“Ba komai Allah ya baki lafiya”

Na fada ina kallonta cike da tausayawa, shi kuma ya kai hannunsa ya daga ta daga kafadarsa yana tambayarta.

“Baki yi Sallah ba?”

“Na yi sallah ina son shiga bandaki ne na yi fitsari amman na kasa sai jiri nake ji”

“Lemme help you”

Ya fara kokarin kamata sai ta mike tsaye tana narke masa a jiki kamar wadda bata iya tafiya, ni kam sai mamaki yadda yake da kokari nake ba ma jin tsoron kar aljannunta su tashi ta makureshi. Bandakin suka shiga ya rufe, ina zaune shiru ina kallon furnitures din na ji an bude kofar kadan ta yadda za a iya jin sautin saukar ruwa ko murya. Kamar yadda na ji karar ruwan can kuma sautin karar kiss ya fara tashi. I was like da gaske kissing juna suke a bandakin? Mamaki da kunya suka baibaiye ni. Can kuma na ji ta ce.

“Dan Allah ka daina kai da kake da Amarya”

Kamar dai ta fada ne domin na ji, saboda muryarta yana daf da kofar bandakin. Ban ji me ya fada mata ba domin bana jin tashin nasa sautin, sai na ji ta kyalkyale da dariya sosai.

“Lafiya ta samu kenan tun da kika yi wannan dariyar”

Wannan karon na ji furucinsa domin yana daf da kofar ne a yayinta ita kuma ta bude kofar ta fito. Muna hada ido sai ta yi murmushi ya rika ta zauna bakin gadonta.

“Angon Noor ya kamata ka shiryawa amaryar abun karyawa, ni ya kamata na yi amman jikin ba dadi”

“Karki damu, yanzu zamu dafa wani abun”

Ta leko ni.

“Kanwata kuma yar'uwarta me kike son ki ci?”

Shi ma ya juyo yana kallona da alama amsata suke jira.

“Duk abun da ya samu, ba ni da zabi”

“Da dai kin fada zai fi, kar mu ba ki abun da ba shi kike ci a gidanku ba, ya bata miki ciki”

Furucinta na karshe sai na ji kamar bakar magana ta jefa min, kamar dai tana nufin babu a gidanmu na zo inda ke akwai. Hafiz na ji yace.

“Indan wannan ai ba matsala Noor tana son dadi sai idan bata samu ba, haka ne Amarya”

Na yi kamar ban ji shi ba, ban kuma amsa masa ba har ya mike tsaye ya karaso inda nake.

“Madam a ba ni aron amaryar nan ta rika min wani abu a kitchen na rage mata kadaici”

“Aa ban yarda ba, ba zaka gajiyar min da kanwa ba, kana ganinta ka san yar hutu ce bata saba wahala ba, ba yar kananan mutane ba ce ai, ka tafi kai da yaranka ku yi aikin”

“Amarya karki zancenta tashi mu tafi”

Na mike tsaye a zatona da gaske yake, sai na ji tana masa gargadi cikin wasa.

“Barrister, ka san doka ka san Shari'a ka bar min amaryata mu yi hira”

Ya juya yana kallonta da dariya.

“Au amaryarki ce ma?”

“Eh mana abun ka ai abuna ne, ko kana da ja? Yanzu na zubar maka da hakware”

Ya girgiza kai ya daga hannu sama like yayi surrender sannan ya fice daga dakin. Na yi murmushin zamantakewarsu ta burge ni sosai, yadda bata nuna min kishi bata nuna masa sai na ke jin kamar ta cancanci a bata kambun Sarauta na Matan Arewa.

“Amarya zauna mana, amman fa karki yarda ki ba da ni, ba'a yi ma Namiji rawar jiki, Na ga yana cewa ki tashi muje kika tashi, ai mace yar sarauta ce da isa, balle kuma ke da ba wani son shi kike ba, Wallahi ki rika ja masa aji, gaisuwa ma idan ba shi ya fara yi miki ba karki yarda ki fara gaishe shi, kullum shi yake fara gaishe ni da safe ya bincika lafiyata idan na tashi kalau, and most of aikin gidan yawancin shi yake yi ban cika yin aiki ba gaskiya, Barrister yana da kirki ba ko wace mace ke samun irinsa ba”

Na sauke kaina kasa ina tunawa da gaisuwar da yayi min da dazun. Ta gyara zama tana fuskata.

“Akwai abubuwa da ya kamata ki sani a tare da mijinki, sannu sannu zan fada miki In Shaa Allah, amman dai ina shawartarki ki rage rawar jiki, ba ayi ma namiji haka kara ki rika nuna masa alfarma kika masa fa kika aureshi damam can ba son shi kike ba kuma ya sani, kin gan ni auren soyayya muka yi ni da shi, amman ya sha wahala kamin na amince masa a shimfida, haka ni ma na sha wahala suma na biyu, ban taba jin azaba irin ta ranar ba, Barrister ba shi da tausayi a wannan bangaren”

“Suma kuma?”

Mamakin suma ya mantar da ni mamakin fada min sirrin aurenta da nake ganin be kamata ta yi ba.

“Kwarai kuwa? Kawayena ba su fada miki ba? Wata kila saboda sun san baki son auren ne, ba dan kar na daga miki hankali ba da sai na turo miki wasu littaffan kin karanta ki fahimci yadda abun yake domin na fahimci ke yarinya ce kurciya na damunki”

Gaba daya ta firgita min kwakwalwata, daman ni ina jin cewar ba zan iya yarda wani namijin da ba Zafeer ba ya aikata wani abun da ni balle kuma yanzu da ta fada min waye Hafiz ko kuma na ce Barrister kuma ai ba zata masa karya ba a matsayinsa na matarsa uwar yaransa kuma mace mai kirki.

“Amman...”

Ta yi hanzari yi min alama da na yi shiru tana nuna min kofar dakin da Barrister ya turo ya shigo, yana Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un.

“Me ya faru?”

Ta tambaya ni da ita muka kallonsa cikin tashi hankali.

“Momy ta kwanta dama, mahaifiyar Kareem ta rasu yanzu...”

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Ta fada ni kuma na mike tsaye da sauri ina kuka.

“Wayyo Allah Kareem, ya rasa uwa na shiga uku... Allah kadai ya san halin da zai shiga, dama matarsa da bata da kirki, amman uwa akwai ciwo yanzu zai shiga damuwa sosai, wayyo Allah Kareem...”

Kuka nake sosai ina fadin haka, na dafe zuciyata ina girgiza kai, har cikin kahon zuciyata nake jin tsananin tausayin Kareem ya kamani. Daga Hafiz din har matarsa tsayawa suka yi kallona.

_______________________

Toh fa Anya akwai Uwargida mai karfin zuciya da iya danne kishi ta rike kishiya a matsayin yar'uwa kamar yadda Matar Hafiz ta yi? 🤔

Ko wane hali Kareem yake a yanzu 😪

Ya zamanta kewar Noor zata kasance a gidan Hafiz? Ga tafiyar dai mun fara... 😊

#KhadeejaCandy as always... 👌
#TKZMAPAID PAGE 2️⃣

©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....

You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153

_______•••_______

“Daman kin san ta ne?”

Na juya na kalleta sai na girgiza kai har lokacin ina kuka sosai.

“Aa ni ban ma taba ganinta ba, Kareem ne ya ba ni tausayi, zai shiga damuwa sosai yanzu”

“Daman duk mai rai mamaci ne, Addu'a kawai suke bukata, amman wannan kuka haka ai ko mahaifiyarki kika rasa iyaka kenan”

Ban sake ce mata komai ba, wata kila ita din bata shaku da iyaye ba shiyasa bata san zafin rabuwa da su ba. Barrister kuma ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta.

“Ki yi hakuri Noor kowa baya wuce lokacin, bari na tafi gurinsa yanzu”
Chapter 2 · 0% Book details