← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 82

Sashe 73

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Karki, taba yarinyar da bata miki komai ba saboda ni, kin cutar da ni that's enough, you have no idea what she's going though, because of your stupid husband, and yanzu kuma ke ki ce zaki saka ta gaba, kuma duk a kaina, ya ishe ki haka”

Ta fara bugun hannunsa da karfinta jin da gaske kokarin kasheta yake, she's fighting for her life. Sai da wayarsa ta fara ringing sannan ya sake ta fuska a hade, ita kanta bata taba ganinsa cikin bacin rai irin na yau ba. Tari ta fara tana hakki kamin ta juya da sauri ta fice daga falon.
Wayarsa dake ringing ya nufa ya dauka number Yusura ce, for the first time take kiransa bayan rabuwarsu, be haddace number duka ba but ya rike karshen numberta tun a lokacin da take gidan.

“Hello”

“Sallamu Alaikum”

“Wa'alaikumussalam, Lafiya?”

“Tine ce bata da lafiya, tun shekaran jiya, an bata magani amman abun be yi ba, jikinta ya tsanani yanzu”

“Ganin nan zuwa”

Ya sauke wayar ya dauki wayoyin duka biyu ya nufi stairs keys dinsa ya dauko ya sauko ya fita daga falon. 30m ya isa family house dinsu be faka ko'ina ba sai a bangaren da Yusura take tare da kanensa da yaransa. A falo ya same su daga Yusura har Tine din da aka yi ma shimfida a falon. Tun da ya shigo Yusura take kallonsa har ya karaso falon da babu kowa sai yarsa da tsohuwar matarsa dake sanye da katon Hijab domin a yanzu shi din ba muharraminta ba ne.
Ya kai hannu ya taba jikin Tine sai ya ji shi da zafi sai dai ba sosai ba, domin bachi ma take.

“Me yake damunta?”

“Zazzabi ne kawai sai ciwon kai da take cewa ta yawan tari da ciwon ciki”

Ya saka hannayensa ya tallafota ya maidata jikinsa yana taba cikin nata, a nan ta bude ido ta kalleshi.

“Dady ka zo?”

“Eh baki da lafiya”

“Eh amman da sauki”

“Fada min abun da kike ji”

Ta nuna masa gun da ke mata ciwo ta fada masa.

“Okay zan siyo miki magani yanzu, idan baki ji sauki ba daga nan zuwa gobe sai mu auna ki mu gani kin ji?”

Ta daga mishi kai tana kwantar da kanta jikinsa.

“Dady i miss you i miss our home, yaushe zamu koma?”

Ya kama hannunta ya rike yana wasa da shi.

“Tine akwai abun da ya kamata ku sani, the thing is...”

“Yara ne ba za su fahimta ba”

Yusura ta tari numfashinsa sai ya daka mata tsawa.

“We have to make them understand...”

“Are you Okay?”

“I'm Not...”

Nan ma ya amsa mata a tsawace, Tine ta dago daga jikinsa ta kalleshi

“Dady why are you shouting?”

“Am... Uhm..”

Ya rasa me zai ce, sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume. Kamin ya kwantar da ita ya mike tsaye ya fice daga falon.

**** **** ****

Ta faka a harabar gidanta misalin karfe goma daidai na dare. Kanta ta jinginar a kujerar dake bayanta tana kuka.

“So cuta ne Allah ka cire min son bawan Allah nan, shi baya ganina ba ni ce a gabansa ba, ina kaunarsa amman baya gani”

Ta fada tana kuka sosai, ta bugi gambun motar.

“Ba zan kyale mutanen ba, taya za su lalata rayuwata su kuma su zauna a free? Ni na rayuwa a bakinciki shi kuma ya auri wacce yake so ya rayuwa cikin farinciki? Na san duk shi ya shirya wannan ai daman yana cire ciki, ta kashe aurenta ta fito yanzu ya aureta ko? Tun fa ya rabu da matarsa, bayan ni tawa rayuwar ta gama lalacewa, shiyasa ya fada mata sirrina, to ba ni kadai zai shafa ba har da kai Kareem, ganin yake idan yayi haka zai wanke kansa zai tsira ko? Okay zamu ga ni ai”

Ta bude motar ta fita sannan ta share hawayenta ta nufi cikin gidan cikin zafin zuciya tana taba wuyanta da dayan hannunta, dayan kuma yana rike da key din mota.“Lafiya Hajiya Lafiya?”

Ban kula mai gadin ba na dago da guduna na dawo cikin gidan na nufi jakata na bude na kira number wayarta. Na yi sa'a ta shiga kamin ta amsa har wani jiri nake ganin tsabar bugun da zuciyata yake yi. Ringing tayi ta katse bata daga ba, ina sake kira sai na ji wayar a kashe. Faduwa na yi zaune kan kujerar, ban san abun da zan yi ba, ban san ta ina zan fara nemanta ba. Ban san kowa cikin kawayenta ba. Hana bata da kawaye a garin nan sai yan makaranta kuma ban san waye zan fara bincika ba, ni ban ma san ina makarantarsu yake ba.

Takardar na dauka na saka a jakata na koma dakin na dauko babban akwatina na zuba iya kayan da nake iya gani na rufe na janyo akwati na fito ina kuka. Bana son na kira Mama na fada mata domin bana son su san abun da yake faruwa da Hana, musamman Baba da ba fahimta zai yi ba. Idan kuma na koma me zan fada musu? Miye silar mutuwar aurena? Kuma ina zan ce na bar Hana. Ban amsa tambaya ko daya da mai gadin date din yake min ba. Na mike hanya na fara tafiya ina hawaye har na isa babban titi na tari okada na fada masa tashar da zan hau motar Kano zai kai ni.

Ya charje ni dubu biyu daga unguwar da nake zuwa unguwar da ya kai na hau mota. Na taki sa'a na isar tashar a lokacin da ake neman mutum daya motar Kano ta tashi na mika duka kudin da nake da su na shiga motar na zauna bayan sun karbi information dina. Tafiyar ta min nisa sosai wata kila saboda mota na hau, domin ban tana zuwa ko dawowa a mota ba sai wannan karon, wata kila kuma saboda abubuwan da suka saka ni gaba ne. Dan carjin da ya rage min na siye ruwa da shi su nayi ta sha, har muka isa Kano.

Karfe shida muka sauka garin Kano, domin Tafiyar awa tara ne daga Kano to Lagos a babbar mota. Na fito motar aka cire min akwatina na karba na fara ja zuwa gate din tashar. Napep na shiga na fada masa kasuwar da zai ni, wato kasuwar yan waya.

“Dan Allah ka dan jira ni sako kawai zai karbo”

“Okay amman Karki dade”

“Ba zan dade ba”

Na bar akwatina a ciki na shiga cikin kasuwar a lokacin da wasu suke ta hada hadar tashi saboda yamma ta yi. Wani shagon na nufa na nuna masa wayar hannuna.

“Malam kuna siyen irin wannan wayar?”

Ya kalleni irin duban nan na rashin yarda. Sannan ya karbi wayar ya duba waje da ciki.

“Wayar waye?”

“Tawa ce siyarwa zan yi”

“Saboda me zaki siyar?”

“Ina cikin matsalane ina bukatar kudi”

“Ina receipt da kwalin wayar”

“Suna gida”

“To kije ki dauko waya a hannuna haka ai ta sata ce”

“Wallahi tawa ce, ka duba ciki akwai hotuna na a ciki, kawai ina cikin matsala ne ina bukatar kudi”

Na fada hawaye na jika fuskata. Dayan dake gefensa ya taso ya karbi wayar ya duba.

“Nawa zaki siyar”

“Ni ban san kudinta ba ku siya kawai”

“Iphone 14pro max mu baki 305k kin ga ta dan ji jiki”

Na zaro ido ashe babbar waya nake riko ban sani ba. A zatona wayar ba zata wuce 50k ba idan ma ta yi tsada.

“Ka dai kara, dan Allah matsala ce ta saka zan siyar Wallahi”

Sai ya miko min wayar.

“Ba zan iya siyenta fiye da haka ba, siyen waya haka ma ai it's risk kawai dan na ga kina cikin damuwa ne zan siya, kin ga ma yanzu tashi zamu yi”

“To kawo kudi”

Ya cire min layina ya miko min sannan ya kirgo kudin ya miko min ba tare da na kirga ba na karba ina masa godiya. Na fito da sauri na samu mai napep din nan a inda na bar shi ina shiga ciki ya rufe ni da fada wai na bar shi yana ta jira.

“Yi hakuri”

“Ina zan kaiki?”

“Hotel”

Na fada kai tsaye domin kudirin da ya saka na siyar da wayar kenan domin babu sauran kudi a hannuna.

“Wace hotel”

“Ko wace ma wacce dai mutane ba su cika yawan cikawa ba”

Ya fara lissafa min sunayen hotel yana tambayar wacce za zai kai ni. Zuciyata kuma taya raya me kamata na tafi can ba, gida ya kamata na tafi, amman idan na tafi gida me zan fada.

“Kai ni ko wace ma”

“Okay”

Na share hawaye ina jin bakinciki a zuciyata, yau ga ni a garin Kano amman ba damar tafiya gidanmu. Ina yar'uwata take a wane hali take yanzu? Me ye makomar cikin dake jikinta? Me yasa ban saurareta ba wata kila da bata gudu ba. Ya sauke ni a gaban wata katafariyar hotel mai girma da haske ko'ina.

“Mu shiga ciki ko na sauke ki a nan?”

“Nan ma ya isa”

Na fito na dauko akwaiti na bude jakata na dauko 3k cikin kudin wayar na mika masa, sai ya karba yana min godiya. Na juya na hotel din sai kuma na ji bana ra'ayin shiga ciki. Dan haka na tari wata Napep din na shiga domin aiwatar da kudirina.
A kofar gidan Kareem mai napep din ya sauke ni, na sallame shi na nufi flowers din da suke gefen gidan na daga akwaitina na jefa a ciki sannan na nufi gate din. Na kwankwasa na san by that time yana gida ko hanyar gida, domin muna hanya aka yi sallah Magariba.
Mai gadin ya bude ya leko.

“Mai gidan yana nan?”

Ina magana numfashi daker domin karfina ya gama karewa ga bakina ya bushe, har lokacin kuma ban ji ina sha'awar komai ba duk da kasancewar ina jin yunwa.

“Eh yana nan”

“Dan Allah ka ce mishi yana da bako a waje dan Allah ya fito abu ne mai muhimmanci”

“Wa zan ce masa?”

“Kawai ka fadi haka dai”

“Tohm”
Chapter 73 · 0% Book details