← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 82

Sashe 65

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai ko zan ji cewar mafarki, amman ban ga alamar haka ba. Na mari kaina sai na ji zafin na tsara kunci na, tabbas gaske ne ba mafarki nake ba. Amman taya? Kanwata ce fa uwa daya uba daya, kanwata da mijina? Kanwata ta jini mai bina, kanwata da muka kwanta a mahaifa daya ciki daya uwa daya ta kawo mu duniya? Kuma mijina mijin da nake aure auren sunna! Mijin da nake dauke da cikin dansa ko diyarsa. Tun yaushe haka take faruwa?

Na mike tsaye na nufi madubi na sai kuma na zauna a kasa. Me na yi da na cancanci haka? Why me? Why? Kanwata? Jinina?

“Wayyo Allah na”

Na dafa zuciyata sai wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya ya zo min. Wannan abun yayi min muni ina ji a wasu gurare amman ban dauka abun zai zo kusa ni ba. Na tashi daker na koma saman gadon na kwanta jikina na rawa na takure guri daya na rumgume fillo, a wannan daren bachi be samu damar ziyarta idona ba, kunci be bar ni, kamin safe zazzabi ya rufe ni, filon da na rumgume kuma ya jike da hawaye na. Abdull be dawo dakin ba sai asuba, ina jin shigowarsa da lokacin da ya kwanta saman gadon ya lulluba...

Littafin nan ba kyauta ba ne. Biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.Be dade da kwanciya ba na ji nishanrinsa alamar bachi mai nauyi ya dauke shi. Juyowa na yi na kalli kwanciyarsa, ina mamakin karfin hali irin na ďa namiji a haka kuma yake kallo muna ta rayuwa a gidan kamar babu komai a tsakaninsa da Hana. Sallah bata wani dame shi ba daman ni ce mai tashi da wuri na yi, dan haka na sauko da kafafuwana kasa na nufi bandaki, wanka na fara yi sannan na yi alwala na fito sanyin ruwan da kuma ac dakin yana ratsani sai ya saka na dan ji sassauci a jikina.

Na zuciya kan na san har abada ba zan samu ba. Ni da farinciki mun yi bankwana. Doguwar riga na zuba na shimfida sallaya na sauke farali sannan na fara tasbihi. Ban daga sallayar ba har sai da na ji farkawarsa misalin bakwai na safe.

“Miyasa ba ki tashe ni ba gashi rana ta yi”

“Ni ma ban farka da wuri ba”

Shi kawai na iya amsawa na koma saman gadon na kwanta na lafe kamar mai bachi, domin har lokacin ban san me zan yi ba. Na nuna musu an san komai na rufe su da fada ko kuma na danna na barwa zuciyata komai na bar su da Allah? Amman zan yi? Ina jin abun kamar ba shi da sauki, ina jin zaba da radadin cin amanar da yar'uwata ta yi min fiye da kunar garwashin wuta. Ina jin da ya taba ni yana fadin.

“My soul ta so muje mu yo breakfast”

“Sai anjima bana son komai yanzu”

Na amsa hawaye na min zuba yayin da fuskata take lullube a cikin bargo.

“Okay, ba ki da lafiya ne?”

“Lafiya kalau bana son damuwa dan Allah ka tafi”

“Okay.. I'm sorry dear...”

Ya fice daga dakin sai after like 40m ya dawo yayi shirin office.

“Bachin be ishe ki ba kenan? Ni zan wuce aiki sai na dawo”

Bance masa komai har ya fita. Sannan na tashi zaune gaba daya na rasa me zan yi kaina ya daure abun yayi min muni. Sauka na yi saman gadon na fito falo na nufi windows ya na daga curtain ina kallon motar da Abdull ya shiga Hana kuma ta bude front seat ta shiga ta zauna. Hawaye ya sauko min a haka suke kallona? Yar'uwata ta zama kishiyata ta san sirrina ta san komai akan mijina.

Kusan a falon na wuni ina ta yawo ya kasa sukuni na rasa kalar tunanin da zan yi, kamin na samu natsuwar yankewa kaina shawarar da nake ganin ta dace da ni. Bayan ruwa ban iya sha ko cin komai ba har karfe biyu ta yi na rana na je na yi sallah na fito falo na zauna ina jiran dawowar Hana, domin ita ce mai dawowa da wuri Abdull sai biyar ko shida yake dawowa gidan. Na bata awa daya a zaune sannan ta turo kofar falon ta shigo da sallama na amsa mata ba tare da na bari ta kalli ido na.

Domin na yi kuka har idon ya kumbura, kai tsaye ta wuce dakinta, kaya kawai ta canja ta fito ta nufi kitchen kamar yadda ta saba sai na bi da kallo wai yanzu ita ma tana dauke da ciki kamar yadda nake dauke da shi kuma cikin mutum daya. Sai da ta shiga ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ta tambaye daga can kitchen din.

“Noor me za a dora”

Na mike tsaye na nufi kitchen din na shiga, sai na zame ta tana yanka lemu zata sha sai dai gani na ya saka ta tsayar da yankan da take.

“Lafiya? Me ya samu idonki?”

“Kuka na yi”

Ta aje lemun da wukar ta matso kusa da ni.

“Kuka dai? Fada kuka yi da Ya Abdull ne ko baki da Lafiya?”

Na kalleta ina mamakin yadda take nuna min kulawa kamar ba zata ci amanata a bayan idona ba.

“Na san muna samun tsabani Hana, amman ina sonki ina sonki sosai, zuciyata bata taba raya min na cutar da ke ba, ni ba zan iya?”

“Me ya kawo wannan maganar Noor?”

“Ina tunanar da ke ne idan kin manta, Wallahi Hana ko rayuwata kika ce kina so zan iya baki, balle mijina zan iya mallaka miki Abdull mallakawa ta har abada Hana, Wallahi zan iya yin duk yadda zan yi na ga ya sake ni in ya so sai ki aureshi”

Ta matsa baya tana kallona cikin tashin hankalin da ya bayyana a fuskarta.

“Me Abdull ya fada miki? Wallahi sheri yayi min”

“Babu wanda ya fada min komai, ni na ji da kunena, na kuma gani da idona, kika hada kai da mijina yana ba ni maganin bachi saboda yayi tarayya dake”

Ta daga hannu biyu tana yi min rantsuwa.

“Wallahi Wallahi Wallahi Noor ban hada kai da shi ba?”

Na daka mata tsawa.

“To me yake zuwa yi dakinki? Kullum sai ya ba ni maganin bachi na sha sannan ya tafi dakinki kishiyata ce ke?”

Ta girgiza kai tana kuka.

“Aa amman ba yadda kika tunani ba ne, Wallahi ni ban ci amanarki ba, Wallahi Noor ba son raina ba ne”

“Haka ne, shiyasa ai yake tafiya dakinki har kuna hira kina tambayarsa yaushe za a zubar da ciki, ina dauke da cikinsa kina dauke da cikinsa wane irin wulakanci da kaskaanci ne wannan?”

Ta zube kasan guiwoyinta tana kuka.

“Na shiga uku dan Allah Noor ki yi hakuri ki fahimce ni”

“Wace fahimta zan miki wanda ta wuce wannan? Ko karya nake baki dauke da cikin Abdull ba ki tarayya da shi?”

“Gaskiya ne ina dauke da cikin ina tarayya da shi, amman ba ta yadda kike tunani ba ne, ina son dan Allah ki fahimce ni”

“Toh ina jinki fahimtar da ni”

Ta kasa magana sai kuka take daman ai ba zata iya magana ba, tun da bata da kalaman da zata wanke kanta da su a gurina.

“Tun yaushe kuke cin amanata?”

Nan ma ta kasa magana, sai na matsa kusa da ita na tabbatar mata da abun da shi ne tabbbatacce a zuciyata.

“Na bar miki Abdull har abada, na bar miki Hana, yau ba zan kwana da aurensa ba”

Na wuce na shige dakina na fada kan gadona ina kuka mai karfi. Abincin da bata girka ba kenan ni kuma ban sake fita dakin ba sai da na ji motar Abdull. Tsanar hada ido da shi ne ta saka na fice daga dakin na nufi kitchen na tsaya a cikin har ya shigo.

“Bacchi kuke ne?”

Na ji ya fada domin yayi sallama be ji kowa ya amsa masa ba. Sai da na tabbatar ya shiga dakin, sannan na fito kitchen din.
Dakin da Hana take na shiga na nufi gurin da takardunta suke na bude jakarta na dauko littafi na cire paper na dauki pen, sannan na kalli kofar bandakinta da nake jiyo kukanta na munafurci daman na san haka zata yi ai, karshen munafuki jin kunya.

Na shiga da kuzarina, domin na gama yanke shawara Wallahi ko auren Abdull ne rayuwata yau kam na shiryawa mutuwa domin ba zan iya kara awa daya da aurensa ba. Zaune na same shi sanye da suit dinsa na aiki da be cire ba yana duba wayarsa da alama wani abun yake kallo. A lokacin da na kalli fuskarsa sai na ji ban taba tsanar kowa a duniya kamar yadda nake jin tsanarsa ba. Kusa da shi na karasa na aje masa takardar da biron.
Ya kalli takardar da biron da na aje masa.

“Miye wannan?”

“Me ka gani?”

Na tambaya ina kallonsa cike da tsana da kyama.

“Takardar da biro”

“So na nake ka rubuta min saki”

Ya kalleni.

“Are you okay?”

“Ka ji ni ai i mean it ka rubuta min saki na ce!!!”

Na karashe zance a tsawace. Ya aje wayar hannunsa ya mike tsaye.

“Saki? My soul kin san me kike fada kuwa? Ba a wasa da wannan kalmar fa”

Ya dafa ni sai na buge hannunsa ina tauna hakora ta cikin bakina.

“Wani abu kika sha yau?”

“Eh... Na sha bala'i da masifa da wutar da zan amayar maka a yanzu nan idan baka sake ni ba”

“Na sake ki kamar yaya me yake damunki?”

“Kai ne kai kake damuna Abdullahi, na tsane ka, damba marar tunani dan duniya wulakantacce, barikin ta wuce waje har sai ta shigo cikin gidana? Sai ka hurumina da yar'uwata?”

“Kina da hankali kuwa? Ni kike kira damba...”

Ya daga hannu zai mare ni, a nan Allah ya ba ni iko da karfin iya rike hannun da dukanin karfina.

“Maci amana, karka sake tsinanen hannunka ya kai ga halattaciyar fuskata ma ci amana ka bi yaya ka bi kanwarta, haihuwar hasara”
Chapter 65 · 0% Book details