← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 82

Sashe 78

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Suna hannunta, idan Kareem yana son ganinsu zai zo ya gansu ne sai ya koma, shi kadai yake rayuwa a gidan yanzu, yana cikin kadaici da ban tausayi sosai, gashi ya rasa yarinyar da ya so ya aura, abun ba dadi, ni ba zan iya biyayyar da Kareem yayi ba, ba zan iya auren macen da bana so ba, auren kiyayya ba shi da dadi shiyasa Yayana yake matukar ba ni tausayi, yana da zuciya da hallaya masu kyau, amman har yanzu be samu farinciki ba”

Tausayinsa ya kama ni sosai domin na san yadda rayuwa da wanda baka so take, na gwada na san yadda ake ji.

“Kin san me yasa nake baki labarin nan?”

Na amsa masa da alamar ban sani ba.

“I want you to be his best friend, domin yanzu ba shi da abokin shawara ya rasa Hafiz, ya rasa mahaifiya ni kuma tawa safgar nake dabam, na lura da wani abu yayana yana samun farinciki idan kuna tare ko yana zancenki, please idan kin ganshi a cikin damuwa ki yi kokarin cire shi, kuma ki yi iya yadda zaki iya ki ga ya auri wacce yake so take ba shi farinciki yana cikin damuwa sosai...”

Aaryam yana maganar ina kallon Kareem dake tsaye hannayensa zube a aljihu yana jiran karasowarmu.

“Kin min alkawari zaki saka shi ya auri wacce yake so? Shi ma ya samu farinciki kamar kowa? Farincikinsa shi ne na mu, and don't tell anyone mun yi maganar nan”

Ban iya amsa masa da eh ko aa ba har muka isa gurin da Kareem yake shi kadai yana kallonmu. Da dan zargi yake kallon kanensa sai Aaryam ya daga masa hannu ba tare da ya ce komai ba ya wuce cikin asibiti. Sai da na daina hango shi sannan na juyo na kalli Kareem.

“Me ya fada miki?”

“Yadda akan samu Hana”

Na amsa kai tsaye.

“Come on karki wasa da ni mana, na san ki fa”

Na yi murmushi.

“Ba ka ce ba zaka zo ba?”

“Na ji kamar hakan da na fada be miki dadi ba, shiyasa kika yanke wayar maybe you want to see me huh?”

Ya daga min gira sai na yi murmushi

“I miss you, i just wanna say thank you, ban taba haduwa da wani mutum mai karamci da sanin ya kamata da kawaici da son farinciki ba sai Kareem, ba alakar uwa ba ta uba amman komai nake so kana yi min, people like you a rare, kai mutumen kirki ne, kai mutum ne mai damuwa da damuwar wani, Allah ya faranta maka ya baka abun da kake nema Kareem”

Yayi murmushi mai kyau ya daga kansa yana kallon saman kaina domin yana tsaye ne a matakar dake bawa mutum damar hawa ward din dake cike da mutane, ni kuma ina kasa daman ya fi ni tsayi balle ya hau akan abu.

“Kalamanki sun lashi zuciyata, a duk lokacin da kike bukatar wani abu, ko wani ya taba ki just come to me zan miki duk abin da kike so, if you ever need safe just come to me”

“Da me zan saka maka Kareem?”

Yayi dariya mai dadin sauraro.

“Thank you, just let me be right beside you in anything you do”

Ya fada yana lumshe ido.

Na yi murmushi ina kallon mutane fake ta kai da kawo.

“Mu je ciki ki ganta”

Muka jera muna tafiya sai kamshi yake mai kwantar da hankali.

“Kareem”

“Uhm mmn”

“Ina Yusura?”

Ya tsaya cak ya daina tafiyar da yake ya kalleni. Zai yi magana wani mutum ya ba shi hannu suka gaisa, after ya gaisa da shi ya juyo ya kalleni.

“Ina wannan ya fito kuma?”

“Kawai ka amsa min mana”

“Tana gida family house dinmu, ba ma tare yanzu”

“I'm happy for both of you, rayuwa da wanda baka so ba shi da dadi”

Ya sauke gutun numfashi.

“Haka ne, rayuwa mutum shi kadai ma bata da dadi, amman dai da sannu zan saba”

“Ai ba haka zaka zauna ba, zaka yi aure kai ma ka auri wanda kake so take sonka”

“Ba zan taba wani auren ba Noor, yarinya daya nake so kuma na rasa ta, shi ke nan, ba zan sake son wata ba”

“Maybe zaka iya son wata, ita ma ai baka san zaka sota ba sai daga baya ko?”

“No tun farko haduwa da wannan yarinyar na ji wani akanta, amman ban fahimta sai daga baya, kuma yanzu na yi latti I'm not the one she mean to find, every thing keep us apart, amman ni na san ina kaunarta sosai, i love her so much”

Ban san miyasa ba, na dan ji babu dadi da yace yana kaunarta sosai.

“Amman ka yi sanyi ne da baka same ta ba? Kai din nan babu wanda zata ce bata sonka”

“Na je ne a makare, wani ya riga ni shiga zuciyarta, kuma ita dai tana jin ban mata ba zata iya aurena ba, har yanzu bata da wayo bata gama fahimtar duniya ba, amman dai zan jira har lokacin da zata yi hankali ta natsu ta fahimce ni, maybe we can rewrite the start...”

Na masa duba mai cike da tambayoyi, na ji wani bangare na zuciyata na raya min ko dai da ni yake.?

“Ya sunanta ma?”

“Sunanta Hafsat”

“Ta yi aure ai ka ce ko?”

“Eh”

“To tace maka zata fito ne da ka ce zaka jira ta?”

“No, tana gidan mijinta har yanzu”

Ya bude min kofar dakin yana kallon cikin idanuwa.

“Noor”

Kiran da Hana ta yi min ya saka na dauke idona daga kallon Kareem na kalleta, na shiga dakin da farinciki da murna da jindadi sosai ta ji rauni a kai da kai da kuma hannu har an saka mata bandeje an daure. Na rumgume sai ta fashe da kuka sosai.

“Inna a ba su guri su tattauna mana, Aaryam mu tafi ko?”

Ina jin lokacin da Kareem yake fadar haka, ban dago ba sai da suka fice gaba daya daga dakin har kanwar Mama.

“Dan Allah ki yi hakuri, da na sani ba zan je na zauna a gidanki ba Wallahi”

“Ba laifinki ba ne, halinsa ne daman da ace ba halinsa ba ne ba zai fara ba, ke ya kamata na bawa hakuri na janyo ki a jiki gashi sanadina kin cutu, kuma ban fahimce ki ba sai da kika tafi”

“Haka Allah ya tsara min, ban isa na wuce wannan ba, arziki na ma daya an cire cikin”

Na dafata.

“An cire? Waya cire? Yaushe?”

“Tun a ranar da na dawo yayi min allurar amman sai jiya ya dauke ni ya kai ni wani gida wata nurse ta wanke min marata yace an cire komai?”

Farinciki ya lullube ni.

“Amman ta sani amman?”

“Eh ta sani, tare muka je da ita yace a bar maganar ne ba sai an fadawa kowa ba, kanensa ma be sani ba”

Na sake rumgume ta ina jin kamar Kareem na rumgume tsabar farinciki.

“Amman Kareem din nan son ki yake yi ko Noor?”

Na dago daga jikinta

“Aa be taba nuna min ba, be taba fada min ba”

“Kyautatawar da yake miki ta wuce misali”

“Wata kila saboda ina matar abokinsa ne, kuma yana da tausayi ke ma kin ba shi tausayi shiyasa ya saka aka cire cikin”

Na sauke kanta kasa hawaye suka sake idonta.

“Na yi nufin kashe kaina, lokacin da na bar gidanki, ba ni da gurin tafiya, kuma ba zan iya koma gida ba, da kaina na tara kaina a titi mota ta bugu ni, amman ban mutu ba sai na ji ciwo a hannu da kafa da kai, mutumen be tsaya kai ni asibiti ba ya gudu, sai mutane ne suka taimaka min suka kai ni, su ma suna kai ni suka gudu, asibitin kuma suka ce ba za su taba ni ba, sai da dansa kuma sai an siye kati, a gurin aka bar ni wulakance, sai da wahala ta yi min yawa na kunna wayar na ga sakonki, da kuma wani sakon ta wata number yace min shi Aaryam ne idan ina bukatar taimako na fada masa, a madadin na kira ki sai na kira shi, da muka yi magana sai yace kar na kira ki, shi yasa aka dauko ni daga can aka kawo ni Kano. Abdull ba zai gama lafiya ba, kuma na jidadi da baki samu ďa da shi ba Noor, ni kadai na san me nake ji a raina, kuma shi kenan ya sha a free babu abun da za a masa”

“Saboda gudun abun da zai biyo ba ne, Mama ta ce idan wani ya ji ba za a aure ki ba, kuma zai zama abun magana a cikin unguwarmu, amman ki kaiwa Allah kararsa zai saka miki”

“Kullum sai na fadawa Allah, ina masa Allaj ya isa, amman wannan abun ba zai taba gogewa ba”

Turo kofar dakin da aka yi ne ya saka ta yi saurin share hawayenta ni ma na share nawa. Zainab ce take fadar na tashi mu tafi dare yayi, Mama Talatu ma ta dawo dakin sai na yi mata sallama sannan muka tafi. A napep ma Zainab ta tambaye ni kwatankwacen abun da Hana ta tambaye ni cewa wai Kareem so na yake.

“Be taba fada min ba”

“Amman ke baki lura ba, ji yadda yake kallonki fa, kuma yana ta yi min tambayoyi a kanki”

“Amman ni be taba cewa yana so na ba, kuma yana ma da wacce yake so sunanta Hafsatu”

“Ikon Allah, toh amman dai abun da mamaki wata kila jini ne ya hadu ko kuma ya riga ya fara sonta ne ba yadda zai yi da ke”

“Tun kamin ya hadu da ita fa, muke tare ai da ya fada min, kuma ni bana ma son shi”

Na yamutsa fuska tunawa da na yi da wani abu. Zainab ta gwalo ido.

“Saboda me?”

“Haka nan dai”

“Tab Wallahi baki san abun da kike so ba, kamar wannan zaki ce baki son shi? Mutum mai kyau mai kudi mai komai, ko ni za'ayi aurena a watan nan Wallahi yace yana so na zan iya balle auren na aure shi”
Chapter 78 · 0% Book details