← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 82

Sashe 54

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun gaisa cikin mutunci yayi mata ya gida ya mutanen gidan duk ta amsa da lafiyarsu kalau. A ranar ni da ita da shi duk a dinning muka yi breakfast ina ta Jefa masa hira sai ya ga dama yake amsawa, arziki na daya be fadi wata maganar marar dadi ba, har muka gama. Sai da zai tashi yake tambayar wa zai girka abinci a yau.

“Hana zata girka ai ita take girkawa a kullum yanzu”

“Me za a girka?”

“Me kake so?”

Na tambaye shi sai ya kalleta.

“Kin iya dambu?”

“Babu abincin da Hana bata iya ba, ta fi ni kokari ita bata jin wahalar aiki da girki ma”

“Sai na ci na ji zan tabbatar”

Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamar dai bakar magana kuma kamar a bakin gaskiyarsa kenan. Na yi murmushi

“Shikenan sai ta baka mamaki kuwa”

Ya kalleta kadan ya dauke kai.

“Za mu gani”

Na yi dariya ita kuma ta yi murmushi. Sai da ya bar dinning sannan take fada min next time zata zuba nata abincin ta ci a dakinta.

“Why?”

“Ni dai kawai na fi jin sakewa, ki bar ni na ci a dakina ku kuma ku ci a falo”

“Shikenan ba dole ai sai rai na so”

Na fada mata ina dariya. Ya ci abun da ya girka da rana saboda a gida ya wuni, be yaba ba amman kuma be isa yace be yi dadi ba domin kowa ya ci dambu a ranar ya san yayi dadi. Da haka dai har ya gaji ya fara yabawa idan ta yi girki, wani lokacin har cewa yake a sake yin jiyar jiya. Sannu a hankali ya fara sakewa da ita ita ta dan sake da shi har sukan zauna su yi hira a falo. A gaba ranar yake tambayar makaranta ta fada masa ta kare amman bata cigaba gaba ba saboda tana jin Baba ba zai aminta ba.

“Indai haka ne sai mu rike ki a nan a saka ki a makaranta, ga makarantu masu kyau a nan, kuma da ganinki zaki yi kokari ba kamar Noor ba”

Na kalleshi da sauri ina hade rai irin na wasa, jin yana shigar mata a yau, domin idan yana wasa da ita nuna yake na fita iya komai alhalin ya san kuma ta fi ni.

“Yau kuma?”

Yayi saurin kai hannu ya taba ni.

“Ke wasa nake, ta ina zata fi Mamata kokari, kawai ina dan zuga ta ne kar ta ji babu dadi”

Muka yi dariya dukanmu. After magariba ya fita titi zagayawa, ni kuma na yi dawo falon na zauna inda Hana take cin abinci.

“Noor gaskiya yanzu kam kin dace, yadda kuke rayuwa da Abdull abun ya burgeni Allah yasa hakan ya dore”

“Ameen”

Na amsa ina hamma, domin tun da na shiga wata na hudu nake ta yawan bachin dare, da zarar an yi magariba zan fara jin bachi sosai. Sai bayan sallah isha'i ya dawo tare da tsarabar suya. Hana ta dauko katon plate aka zube kamin kowa ya kai hannu ni har na kai baki tare da albasa da tumatir. Sai da ya ci yanka biyu sannan ya kalli Hana ya ce.

“Ci mana”

Sai ta mike tsaye.

“Bari na dauko plate a saka min”

“Kamar ya? Ki saka hannu mu ci a tare, hana karki zama bakauya yar zaria mana”

Muka kwashe da dariya daman kowa ya san yan zaria bayin kanawa ne.

“Ni dai zan fi jindadi na ci ni kadai”

“Wallahi ba zan zuba ba, idan ba zaki zo ki saka hannu mu ci tare ba sai dai ki hakura ci”

Jin yayi rantsuwa cikin zafin rai ya saka ni ma na yi mata magana sai ta dawo fa zauna ta saka hannu muka fara ci a tare dukanmu, har hira ta biyo baya yana fada min gurin wani basakkwacce mutumen yabo ya siyo suyar nan. A take kuwa Hana ta saka santi.

“Har na tuna da wani kilishi da Mama ta ba ni da naje mata bankwana tace daga Sokoto aka zo da shi a local government Dange, Dangin kilishi”

Muka saka dariya har sai da na sarke, ita kanta sai daga baya ta gane santi ta yi. Na jidadin yadda Abdull yake kula Hana, da farko na yi zaton wulakanci ne zai biyo bayan zuwanta gidan, sai gashi har da ni ya canja min na samu sassauci, na yadda yake mu'amala da ni daga samun cikin. Sai dai kuma a duk tsawon lokacin Abdull baya kai hannunsa balle jikinsa a nawa, zamu kwana a gado daya mu tashi amman ba zai ma bari ko a kafadarsa na kwanta ba.

Na yi masa uzurin wannan saboda na san baya son cikin, wata kila yana hora ni ne har yanzu. Ta dayan bangaren kuma bana mamakin kaurace min da yayi, musamman a yan kwanakin nan da nake yawan farkawa tsakar dare na ga baya nan amman ina jin motsin ruwa a bandaki, wata kila yana biyawa kansa b*ka*ta ne saboda ya kaurace min gaba daya.

Ranar da Hana da cika wata biyu da sati biyu a gidan ta fara min zancen komawarta gida, saboda Baba ya matsa ta dawo, kullum ya kira waya fada yake mata, bata dawo ba. Sai tace masa ban ji sauki ba, da muka kai shi makura sai ya rufe mu da masifa daga ni da har ita yana ta zaginmu a waya.

Washe gari friday kamar kowace jumma'a ya shirya cikin manya kaya na malam bahaushe yana ta kamshi, yana tsaka da saka agogo na ce.

“My Soul jiya Hana ta yi min zacen tafiya gida”

Ya juyo ya kalleni.

“Tafiya gida kamar ya?”

“Gida dai wai tana son ta koma saboda na fara jin sauki, kuma Baba ma ya matsa gaskiya Saboda Umma take yi ma sana'a”

“Aa ba yanzu ba, ta bari sai kin haihu tukuna, idan zaki koma gida sai ku koma tare, ko ma ku yi zamanku a nan gaba daya”

“Baba ba zai yarda ba, yayi ta mana fada jiya fa sosai saboda dawowarta, wai taje ta zauna”

“Toh wai idan ta koma me zata masa ne?”

“Babu fa kawai tana yi ma Umma talla ne ina tunanin Umma ke zugawa ta dawo, saboda sana'arta”

“Ki yi magana da ita ta yi hakuri ta zauna a har sai kin isa haihuwa mana”

Zan yi magana ya riga

“Bari na yi mata magana”

Ya juya ya fita, sai na sauka daga kan gadon na bi bayansa. A falo muka same ta zaune tana rike da remote. Abdull ya fara mata magana sai ta nuna masa ita bata da matsalar zama, matsalar ta Baba ce sai ya aminta.

“Fada min gaskiya ko dai saurayinki ne ya matsa ki dawo”

“Hana bata da saurayi for now”

Na amsa sai ya wara ido yana tsokanarta.

“Taya tsaleliyar budurwa irinki, ace bata da saurayi duk kyaun nan na ki”

Ta rufe ido tana jin kunya. Sai yayi murmushi ya ce.

“Zan kira shi na yi magana da shi, wata kila yana jin nauyi na ne shiyasa be taba kirana yayi min magana ba, idan ma ta kama na rika saka masa wani abu a account da za a rika bawa Umma madadin kudin tallarki zan yi haka, daga nan ma sai ya aiko mana da takardunki a sama miki makaranta ki samu ko nce ko diploma”

Ni da ita muka kwalo ido waje ta taso da gudu ta rumgume tana tsalle tana murna, ta duka kasa tana masa godiya. Ni ma na masa godiyar ina jin kamar Allah ya amsa addu'a ta ne ya sauya masa yar rayuwar da ya fara na wulakanta. Domin kyautatawa yar'uwa ta jini kamar kyautata min ne. Be ce komai ba sai kallonta yake yana murmushi har ta dauki karamar wayarta ta kira Mama ta shiga dakinta tana fada mata.

“Kanwarki ta fi ki kyau Noor, ko wani friend dina da ya zo ranar ya ganta sai da yace yana da kyau”

Ya fada min kai tsaye, ba tare da fargabar komai ba na yi murmushi, ai jindadi ne a yabawa dan'uwanka a gabanka.

“Tana da kyau, kuma ita tana da jiki ba kamar ba”

Ya mike tsaye yana lalaba aljihunsa.

“Ba wani jiki da ita sosai ba, ta dai fiki cika ne kawai. Zan tafi sai na dawo”

“Allah ya tsare, ka siyo min rake idan zaka dawo”

“Toh”

Na raka shi har waje sannan na dawo cikin gidan. Ina jin hana tana ihu da murna kamar zata fasa gidan dan murna, na zauna kan kujera ina murmushi yau kuma ta zama kamar ni da hauka. Kamar jira ake na zauna sai na dan abun da ke cikina yayi motsi, ban taba ji ba sai ranar na bude rigar da sauri na kalli cikin, sai ya sake yin motsi da sauri. Hawayen farinciki ya cika idona na kai hannu na shafa cikin ina jin sanyi a cikin raina.

It's 500

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0

KAREEM POV.

Dagowa yayi daga rubutun da yake a diary ya kalli Safeena dake zaune gabansa fuska a murtuke kamar an mata mutuwa.

“I thought na fada maki bana bukatar sake ganinki?”

A take ta yi murmushi.

“Ta ina zaka so ganina ka samu sabuwar mace? Ka ba ni mamaki Kareem, ashe zaka iya bude zuciyarka wata ta shiga not just zuciyarka jikinka ma zaka iya hadawa da ita?”

“For the very last time ko ki fita ko na saka security su fitar da ke”

Wannan karon dariya ta yi.

“Ashe zaka iya wulakanta ni saboda wata banzar bazara, me ta fi kwarewa akai? Karamar yarinyar kamar Noor zata dauke maka hankali”

“Karki sake zaginta, tana gidan mijinki tana zaman aure noor ba karuwa ba ce, ta san mutumcin aurenta”

Ta runtse ido kadan ta tauna halshenta.

“Ni da kai ne ba mu san darajar aure ba kenan? Da rarrashi na zo gurin amman na lura gaba daya ta canja maka tunani akaina ta canja maka kwakwalwa, shikenan”

Ta mike tsaye.

“Daman na zo nan ne na ji, cikin dake jikinta na mijina ne ko naka?”

Kareem ya watsa mata wani mugun kallo.

“Ita fa ba fasika ba ce”
Chapter 54 · 0% Book details