← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 82

Sashe 58

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya ya fara tafiya, ta juya tana kallonsa? Me yasa yau ta ji dabam? Ta dade tana jiran zuwan ranar amman ta kasa farinciki, wacam karon ta jidadi da ya sake ta amman ta kasa farinciki.

“Yaran fa?”

Ya juyo ya kalleta hawaye ya gani suna fitowa daga idonta suna zuba a fuskarta.

“Zan kula da su”

“Za su fi jindadin zama a gurina”

Ya taka zuwa inda take tsaye.

“Idan haka kike so, zan minta, but only on one condition, no matter how happen a raye ko a mace zaki fadawa yaran nan cewar mahaifinsu yana kaunarsu, duk wani abun bacin rai ko bakinciki da zai biyo baya ko ya biyo i still love them, ki fada musu mahaifinsu yayi kokari ganin ya tsare duka hakkinsu sai abun da ya fi karfinsu”

Ya juya ya nufi kofa sai ta risina kasa ta kira sunansa.

“Ka yafe min Kareem, na cutar da kai na sani, kiyayya bata bari na yi biyayya ba”

“Komai ya kare yanzu Yusura it over now”

Ya amsa mata ba tare fa ya juyo ba ya fice daga falon. Yana shiga motarsa ya murza key mai gadi ya bude masa gate ya dauki hanyar da zata sadashi da gurin aikinsa. Be yi nisa da gida ba hudu ya rufe masa ido kansa ya fara juyawa yana ta kokarin controlling motar amman ya kasa.

NOOR POV.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Abun da na fada kenan a lokacin da na farka da karfi, sakamakon mummunan mafarkin da na yi. Wai muna tafiya a jirgi sai ya muka fado kasa ni har da ni ciki, na bugi icce har sai da hankalina ya gushe. Addu'a na yi na neman tsari daga mummunan mafarki. Na yi a'uzubillahi har karshe na tofar dama na sake yi na tofar hagu, sai haki nake kamar wanda ta yi yaki, hannu na kai na lalaba ban ji Abdull ba, sai na sauka daga kan gadon na kunna wuta na nufi bathroom din da nake jin motsin ruwa na tsaya jiran ya fito na shiga.

Da na lura ba shi da niyar fitowa sai na tura kofar na fara lekawa babu kowa a ciki, shiga na yi ciki da mamaki, tab din ne a kunne ruwa na zuba kadan kadan amman babu kowa a ciki. Kashewa na yi na bayan na gama fitsari wata kila ya manta ya bar shi a kunne ne. Sai da na nufo gado na zauna sai kuma wata zuciyar ta tambaye ni ina ya tafi? Bargon na sake yayewa na sauko da kafafuwana ina mikewa tsaye sai gashi ya shigo dakin.

“Ina ka tafi?”

“Ruwan na ji na hada tea, ina zaki ke?”

“Ai dai ba zan bata ba a gidana ko? Idan bana dakin nan ina falo ko kitchen”

Ya hauro saman gadon ya kwanata rai a bace kamar an masa wani abun, har ya manta be kashe wutar ba, wata kila tambaya ta ce ta bata masa rai.
Sauka na yi na kashe wutar na dawo na kwanta.

It's not Free pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0

Washe Gari na tashi da wuri saboda zan tafi asibiti, dan haka na gyara da wuri na fito falo, ina jin motsin Hana na nufi kitchen din na dan rikawa mata aiki.
Ina tsaka da kashe socket ta yi min wata magana da ta saka na kalleta.

“Noor ina son na tafi gida”

“Me yasa Baba ya sake magana ne?”

“Aa kawai dai ina son gida yanzu, na fi jindadin zama gida sama da nan”

Na juyo da kyau na fuskance.

“Hana wani abu na yi miki ba daidai ba ko Abdull yayi miki?”

“Aa ba ko daya, kawai dai na fi sha'awar tafiya gida ne”

Na dan jimm ina mamakin dalilinta na fadar haka a yanzu, daman na lura yanayinta gaba daya ya canja.

“Hana mafarki kika yi marar kyau ko me?”

“Ba komai ni dai kawai ina son na tafi gida”

“To kije ki dawo ko kuma ki koma gidan gaba daya?”

“Gaba daya dai nake son na koma”

“Karatunkin fa?”

“Zan hakura na san idan naje can Mama zata iya sakani idan Baba ya yarda”

Na matsa kusa da ita domin babu ta yadda lafiya zata saka ya yanke karatunta ta koma gida haka nan kawai sai da dalili.

“Hana na san muma yawan samun tsabani da ke a gida, amman nan gidan aurena ne, idan kina ganin akwai abun da nake miki da baya miki dadi zaki iya fada min sai na gyara, idan kuma aiki ne kike ganin na sakar miki ragamarsa zan rika yin rabi, amman dan Allah ki zauna ina jindadin zamanki ina son yar'uwa a kusa da ni, ba ni da kowa nan zamanki a gidan nan yana rage min kewa”

“Babu wani tsabani da zamu samu har ya saka na ji bana bukarki a kusa da ni, mu na samu tsabani a gida a nan ma zamu iya samu, saboda zama tare dole wata rana zaka ji an maka ba daidai ba, amman Noor ni ba zan iya cin amanarki ba”

Ta rumgume ni tana kuka, jikina yayi sanyi sosai kalaminta na karshe ya saka min shakku a zuciya.

“Akwai abun da yake faruwa tsakaninki da Abdull ne?”

Ta dago da sauri.

“Aa Wallahi Babu, dan Allah karki zarge shi ki lalata aurenki, Wallahi Wallahi na rantse miki da Allah babu wani abu tsakanina da Abdull”

Hankali ya dan kwanta da ta yi min rantsuwa cewar ba tsakaninta da Abdull ba ne.

“To ya kawo zancen cin amana Hana?”

Ta share hawayenta.

“Ina nufin kamar na guje ki saboda kin min wani laifi, ai kamar na ci amanarki ne a matsayinki na yar'uwata”

“To me yasa kike son tafiya gida? Kina karatunki a nan, Abdull ma idan ya ji ai zai yi fada, Mama ma sai ta miki fada tace kin san ba zaki karatu ba kika saka bata kudi aka biya miki har na shekara uku”

“Kawai ina yawan mafarkin marar kyau ne, kuma ana baki tsoro a gidan nan ina tunanin akwai aljannu a gidan”

“To ki rika addu'a mana Hana, ke da kike fada min yadda zan bi da rayuwa na jidadi yau kuma ke kika rasa ya zaki yi?”

Ta yi murmushi

“Gaba daya na rikice mugun mafarkin da na yi ya daga min hankali”

Zan sake yin magana Abdull ya kirani.

“Noor kin fasa zuwa awon ne? Karki makara fa”

Na dauki ruwan zafi na fice daga kitchen, sai da ta jera mana komai a dinning sannan ta zuba nata ta dauka.

“Lafiya na ga kamar yanayinta ya canja”

Abdull ya tambaya she dai shi ma ya lura da yadda take ta hade rai bata son kallon kowa.

“Lafiya kalau”

Ta wuce dakinta bayan ta amsa mishi, da kallo na bita sai da ta shige sannan na juyo na kalleshi, kamar na fada masa kudurinta sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na san ba abu ne da zai masa dadi ba, saboda kudin makaranta da ya biya mata ga yawan hidima da yake mata, tafiya makaranta ma kullum sai ya bata kudin bus kuma ya rage mata hanya saboda akwai tazara daga unguwarmu zuwa makaranta kuma babu abun hawa sosai ta gurarenmu sai idan sun kawo Passenger.

“Ina jin bata da lafiya ne”

“Me yake damunta? Ko kuma dai mood swings ne”

“Yeah”

Ko da muka gama karyawa ta yi shirin makaranta da uniform dinta da suke sakawa kullum. Tare muka fita sai da ya fara sauketa sannan ya sauke ni a asibitin ya wuce gurin aikinsa.

Tun daga ranar Hana bata sake yi min maganar komawa gida ba, sai dai na lura da yanayinta gaba daya ya canja kamar zaman gidan ya daina mata dadi a yanzu, domin ko hirar da take zama muna yi tare da Abdull a da yanzu duk ta daina, ko da yake yanzu ba kamar da ba ne, da take gida kullum yanzu kuma idan ta tafi bata dawowa sai yamma idan ta dawo wani sa'in ta hau aikin gida ko da ta gama kuma sai bachi. Sai can ba a rasa ba muke zama muna hira a falo da zarar Abdull ya shigo zata masa sannu da zuwa ta shige dakinta ba zata sake fitowa sai gobe.

Ko wani abun ya siyo sai dai na kai mata nata dakinta, ko kuma shi ya kwankwasa kofar dakin ya aje mata daga bakin kofa, wani sa'in idan ina jin wahalar tashi. Wata kila ta fara haduwa da abokan banza masu hore mata kunne ne, ko kuma dai ta gaji da yin aikin gida ne, ko kuma nata gidan mijin take son tafiya ita ma.
Ko ma dai yaya ne na daure ma zuciyata na zauna da ita a haka, saboda bana son ta lakata karatunta a lokacin da take tsananin bukatarsa, kuma ana yi da kai ya fi ba'ayi, zamanta yana taimaka min ko yaya ne tun da ita take min komai a gidan kuma ina ganinta na san ina da yar'uwa a kusa ina jin sanyi a haka din ma.

KAREEM POV.

Da sauri ya maida idon ya rufe ya kai hannunsa dake sanye da drip ya murza idon sannan ya sake budewa. Hannun ya kai ya cire robar dake bakinsa yana kokarin daga hannunsa daya sai ya ji yayi masa nauyi dubawar da zai yi sai yayi arba kan dansa Areef a hannun. Yunkurawa yayi a haka ya tashi zaune ya saka dayan hannun a hankali ya cire hannunsa. Haka ya cire duk wani abu da aka laka masa sannan ya sauko da kafafuwansa yana tuna abun da ya faru.
Chapter 58 · 0% Book details