← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 82

Sashe 31

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kasan da hakan kuma kake zaune da ni har yanzu? Idan zaka kwatanta Noor da misalta ta da Safeena mana, ka ce ta fi Safeena wayo, amman ba ni ba, ni din na san abun da nake so da wanda bana so. Ko da yake dole ka yaba Noor ai, saboda kana sonta shiyasa ka cilastawa abokinka aurenta, yanzu kuma ya tafi ya barku sai ku cigaba daga inda kuka tsay....”

Tana kai aya yana wanke mata fuska da wani zazzafan mari, har sai da ta ja baya

“Ka mare ni Kareem? How dare you...!!”

“Saki kike so? Tafi na sake ki Yusura”

A take ta daina jin zafin marin, farinciki furucinsa ya wanke mata damuwarta. Idan ta tace bata ji tausayin Kareem na mutuwar amininsa ba ta yi karfa haka ma idan tace bata yi farinciki da sakin da Kareem yayi mata a yau ba, ta yi babbar karya. A gurin ta yi sujudar godiya sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin.
Slowly ya zauna bakin gadonsa be taba tsammanin kiyayyar da Yusura take masa ta kai haka ba. Be yi tunanin akwai kiyayyar da zata kai irin ta Yusura ba a zaman aure, ba zai yana sonta ba, amman baya ganin rabuwa da ita a yanzu mafita ne saboda yaransu.

#KhadeejaCandyBaba yana kallona ne kamar ni na kashe Hafiz saboda, Hafiz ya tafi be samu kyautatawa Baba kamar gyara masa gida ko kuma yi masa wata babbar kyauta da yake tsammani ba tun a bayan aurena.
Ni ma ban fahimci hakan ba sai a ranar da Hafiz ya cika sati daya da barin duniya, Mama ta kira waya tana kara kwantar min da hankali, bayan mun gama wayar ne Baba ya rufe ni da fada wai na ci amanarsa wata kila da na kyautata masa da yanzu Allah kadai ya san yadda rayuwa zata zame mana.

“Daman sai da zuciyata ta raya min ba zaman lafiya kike da yaron nan ba, saboda juya min baya da yayi ko lokacin da gobarar nan ta tashi be zo yayi min jaje ba, be ba ni komai ba, ashe ma ba zai dade duniyar ba, kina ta shuka masa rashin mutunci, in ba shi ba taya za su ce wai ba za ki masa wanka ba? Ta ina aka taba haka so suke su hana miki gadonsa kenan”

Ni dai bance komai ba, gaba daya duniyar bata min dadi, ni kaina ina dorawa kaina nauyin da ba zai gogu ba saboda hana mijina hakkinsa da na yi, ya tafi da abun a ransa kuma na daukarwa kaina zunubi.

“Wallahi zan iya kararsu akan haka, domin babu hujjar da tace ba za a baki gado ba, na bincike limin yace kina da hakkin wanka domin an riga da an daura muku aure, kuma sakin da yayi miki ai ba ki cika idda ba”

Sai a lokacin na kalleshi cikin wani irin rauni da damuwa na ce.

“Baba dan Allah ko da sun ce ba za su ba ni hakkin wanka ba, dan girman Allah dan Isar Annabi, Baba kar kace zaka yi kara ko fada ko kuma daukar wani mataki, dan Allah ka kyale su, idan ma ina da hakki Allah ya sani zai saka min”

“Toh haka za a zuba musu ido su ci su cinye hakkinki Noor? Idan aka karba ai ko wani abun a rage da shi, dubi yadda gidan nan yake fa, ko gyara aka yi ba a rage ba? Allah kadai ya san abun da bawan Allah nan ya bari”

“Ko ma dai miye bari Baba mai karewa ne, rayuwar ma ta kare balle kuma abun da rayuwarta ta aje, ni dai da zaka yarda da magana ta Baba da ka yi hakuri ka kyale komai dan Allah”

“Ai daman ke sakarya ce baki san komai ba, sai shashanshanci, ba dan kin nuna masa rashin tarbiya da rashin hankali ba yaushe zai sake ki? Allah ya wadarranki Noor, duk yadda nake ganin kamar zaki natsu ko ki yi hankali ba zaki taba yi ba, duk yadda bake ganin kamar sanadinki wata kila zan warke sai kin kunyartar da ni, ke dai har abada va yar arziki ba ce”

Ya rufe da fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ni dai kam na san ban yi dacen abubuwa da yawa ba a rayuwa ciki har da uba. Domin ko a labari ban taba jin uba makamancin nawa ba, mai tsananin kwadayi da son abun duniya.
Na sani sarai idan na kara wata maganar zai iya rufe ni da duka, a dole na yi shiru na ina ta sauraren masifarsa har yayi ya gama ya fice daga gidan. Haka na gagara tashi a gurin har Hana ta dawo daga makaranta ta same ni zaune a kofar dakin, ni ba kuka nake ba damuwa karara a fuskata, tunanin yadda rayuwa zata zame min nake, hankali ko tunanin da suke ganin kamar ba ni da shi ina da shi, ni na san ina da shi, idan ma babu a da to yanzu yana tare da ni. Rayuwar gidance nake jin kamar ba zata min dadin zama ba, gashi kuma ba ni da wani gurin rabawa da zan zauna na ji sanyi.

Yunkurawa na yi na tashi na nufi gurin da kayan wanke wankemu suke na wanke komai tass Hana kuma ta dora girki ta girka mana shimkafa da miya, duk da kasancewa white rice and stew are my favorite amman ban iya cin wani abun kirki ba, daman abinci ya daina burge ni. Kamar wani zanenen al'amari a daren da muka yi haka da Baba sai ga kanen margayi ya zo gidanmu, ban san ya aka yi ya gane gidan ba, kusan ni dai zan iya cewa ban taba ganinsa ba, idan ma na ganshi ba zan iya shaidar fuskarsa ba, domin ban jima a gidan ba balle na san duka yan'uwansa balle kuma mazan da be gabatar min da su ba. A zauren gidanmu ya shigo bayan yayi sallama Hana ta yi masa izinin shigowa. Dogon hijab ne a jikina har kasa kaina kuma a kasa na kasa kallonsa ganin nake kowa kallona yake a wani muhalli da Aisha ta saka ni a idonsu.
Bayan mun gaisa ya gyara tsayuwarsa ya ce.

“Ya Hakuri Noor?”

“Alhamdullahi”

“Haka Allah ya so sai hakuri, shi kuma Allah yayi masa rahama”

“Ameen”

Na amsa ina jin idanuwa suna cika da kwalla.

“Na san babu dadi, musamman ma ke da kike farkon shiga gidansa ba ki jima ba mutuwa ta yi muku gaggawa, amman duk da haka ki yi hakuri yana cikin jarabawa ne”

“Haka ne, na gode”

“Na san ba ki san ni sosai ba, ni kane ne a gurin Margayi uwa daya uba daya, ni ne kanensa na biyu, makasodin zuwa na a nan shi ne... Abubuwa marasa dadi sun shiga kuma za su biyo baya na sani, amman dan Allah ina son ku kawar da kanku musamman ma ke, ki yi hakuri da abubuwan da zaki ji ko ki gani”

Na yi shiru ina ta sauraren bayaninsa da ban fahimci inda ya dosa ba.

“Na ji wasu abubuwan ne da ba su min dadi a gidanmu, na iya yadda zan iya na taushe abun amman ya gagara saboda haihuwarmu aka yi ba mu muka haife su ba, dole sai hakuri, amman na san ke zan iya neman alfarma a gurinki kuma na roke ki duk kuwa da ba ki san ni ba, amman ina rokon alfarmar dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen margayi akan gadonki, ke ba da kike da shi ba balle ace saboda da gaba, kina gama wanka na san In Shaa Allahu zaki yi aurenki, bana son na ji wata matsala ta taso daga gurinki, ni dai ina kyautata miki zato sosai”

“Ni ba zan iya jayaya akan abun da rai ya tara kuma ya tafi ya bari ba, wanda ya tara abun ma ina yake? Toh me zai saka ni yin jayayya? Idan ma ina da hakki abun da za su ba ni ba zai taka kara ya karya ba, ba shi ne gabana ba, kuma na maka alkawari ba zaka taba jin wani abu makamancin wannan daga bangarena ba”

Ya sauke ajiyar zuciya yana kallona.

“Na yi farinciki da jin haka, na jidadi sosai Allah ya saka miki da alheri, ya baki wanda zai maye miki gurbin Ya Hafiz har ma ya fi shi”

Na yi shiru ban iya amsawa da Ameen ba. Daga haka yayi min sallama ya tafi, ni kuma na dawo cikin gidan ina ta mamaki mi ya ji danginsa ana fada har dauko kafafuwansa ya zo ya tari nawa fadan, ni kan idan gado ne ko nawa ne ba zai daga min hankali ba balle ya saka ni yin magana ko daukar wata dokar tsorona duk na Baba ne.

Ban fadawa Baba wani ya zo ba, sai dai na lura hakan be yanke komai daga hanzarinsa na niyar saka iyayen Hafiz a kotu ba, idan har ba su ba da hakkina na wanka ba, na fahinci hakan ne ta dalilin wayar da na ji yana yi da yayansa wai ya bincika ko'ina ance ina da gado, dan haka ba zai saka musu ido su cinye min hakkin ba. Ban ce komai ba daman kuma ban isa na ce ya rufe da fada ba mamaki ma ya kara min duka. Zaman gidan sam baya min dadi kamar ina zaune a kaya haka nake ji. Ba ka kamar lokacin da sabuwar matar da Baba ya aura ta tare a gidan.

Gaba daya sai gidan ya kara fice min a rai, domin na lura ta shigo da wani salo na hana mu walwala ni da Hana da kuma Yaya, gara ma yaya ba a gidan yake wuni ba, sai dare yake dawowa ni da Hana ne muke ganin rayuwa a gidan. Babu kuma wanda ya isa yayi magana domin mun san halin Baba ba zai taba yarda da mu ba.
Chapter 31 · 0% Book details