← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 82

Sashe 79

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na kalleta da mamaki sai kuma na ji haushinta na fadar hakan fa ta yi ban sake cewa komai ba har muka sauka Napep din. Komai ya zamar mana kamar labari, ni na danne ciwon zuciyata Hana ma ta danne nata mun barwa Allah komai muka koma cigaba da rayuwa kamar yadda muka saba, a bayan. Sai wani shakuwa da kaunarnan junanmu da tausayi ya kara shigarmu, Mama kuma tana ta rayuwa a gidan aurenta ba tare da wani tashin hankali ba.

Abun da ya faru da Hana muka haka kasa muka rufe ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai ita sai kuma Mama da Kareem da kuma uban gayyar da yayi aikin.
Ranar da Baba ya saka ni gaba da tambayar dalilin da ya saka Abdull ya daina zuwa gidan na fada masa ya sake ni ne, Baba tsine min ne kawai be yi ba, amman duk wani kalar zagi na duniyar nan sai da yayi min shi. Musamman da na yi masa karyar cewar kawai bana son sa ne ni na bukaci ya sake ni, kuma da ya bincika sai Abdull ya tabbatar masa da cewar ba fada ba zagi kawai na bukaci sakin ne shi kuma ya aiwatar.

Har kusan korata Baba yayi sai da yan'uwansa suka saka baki, Umma ma sai ta koma tana jin haushina domin tallafin da yake bata na sana'ar da Hana bata mata a yanzu ya janye ya daina yi. Sai tace wai bakinciki nake mata saboda ita din ba uwata ba ce, kuma hassada ta bata tsaya kaina ba har da yar'uwata nake yi ma. Ni da Hana ba ma ce mata komai domin mun san abun da bata sani ba.

Hana ta samu sallama a yanzu da bata fita siyar da awara domin Mama tana ta shirye shiryen sakata wata makarantar ne a nan garin Kano, hakan ya saka hankalinta ya dan kwanta, kuma wani abun Allah samari da masu mata sai kawo mata hari suke a yanzu. Sai dai ni ban tsira daga maganar mutane unguwa ba, ganin na yi arba'in amman ban koma gidan mijina ba, ba mutanen unguwar kawai ba har cikin family na samu masu jefa min magana wai na ki zaman aure, Mama ta fada cewar wasu daga familyta sun ce haka za a zuba min ida ina aure ina fitowa na ki zaman aure.

Na kan yi murmushi kawai na bar maganar a bayan kunnena, domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyi, dadi dai ba zai saka mace ta kashe aurenta ta fito domin ta zauna a gidansu ba, ko kuma ta raba a wani guri, ba ni kadai ba mata da yawa al'umma basa musu uzuri, macen bata sakin kanta bata rike kanta amman ba a fahimtar haka, a koda yaushe mutuwar aure yana komawa a bangaren mace idan afku. Ba zan ina cikin jindadi ba, domin zaman gidan ba shi da dadi agaremu. Amman jiki ya dan bude haihuwa ta kara min kyau ta cike min gurbin kasusuwan da na nake da su a wuya, ba wani jiki na yi can sosai ba amman dai jikin ya bude na cika na zama mace.

Bayan bikin Zainab na je gidanta na wuni a can muka sha hira sosai na ji abubuwa da yawa da mutanen unguwa suke fada, wasu su ce hakkin Zafeer ne, wannan kam ba zan yi mamaki ba idan aka ce hakkinsa ne, domin ya cutu, wasu kuma suka ce TA KI ZAMAN AURE, har da masu cewa wai Zafeer asiri yayi min ba zan taba iya zaman aure ba, wasu kuma su ce ina da aljannu ne kawai da basa son aure. Na yi dariya sosai na danne ciwon dake zuciyata na bar sirrina a cikin raina. Ta rakoni bakin kofar gidanta ta koma ni kuma na haka hanya gyale na a kafada, kaina ya sha dauri fuska kuma ta dauki ido kamar wata budurwar kai wata budurwar ma albarka domin gyaran da nake yi a yanzu bana yinsa a lokacin da nake budurwa.

Ina kokarin tare mai Napep wani dattijo ya faka gabana, ya sauke gilashin motar yana kallona fuskarsa da murmushi.

“Ina zuwa?”

Na waiga na kalli bayana na kalleshi na yi zaton ko da wata yake magana ba ni ba domin ba yaro ba ne zai haifi kamata da wanda ta fi ni sau goma ma.

“Baba ni?”

Na nuna kaina, yayi dariya.

“Yan mata kenan, shigo na rage miki hanya”

“Aa na gode”

“Ba zaki shigo ba? To saka min number ki a nan”

Ya miko min wayarsa.

“Amman lafiya”

“Lafiya Kalau Wallahi, kawai na ga ruwan dake min wanka ne, saka min number ki yarinya”

Na karbi wayar na saka masa number na, sai ya miko min kudi.

“Rike wannan ki hau napep”

Na karba na masa godiya, sai ya wuce na bi matarsa da kallo ina dariya, to ko dai ya ga na yi masa kama da tsofi ne ya tare ni haka har da wani ruwan dake masa wanka, tsab kuwa zan masa wankan kwashe kudi na kara gaba domin ba zan iya da kayan majina ba. Allah ya tsare ni. Na tofar da yawu.
Ina yin gaba kadan wata motar ta faka shi ma dai sauke gilashin yayi yana min magana.

“Hajiya ina zuwa haka?”

Na dan taba fuska, yau dai wata kila aljannu sun shafa min maganin farinjini a fuska ko kuma kwaliyar da na yi ce ta dauki hankalin mazan oho.

“Gida”

Na amsa sai kawai na ga ya bude motarsa ya zagayo ya bude min front seat.

“Ki min alfarma motana ta samu lada, na sauke ki gida Hajiya, karki ce aa”

Ta ina zan ce aa bayan yace kar na musu, shi din ma be yi kama da wanda za a musa masa ba. Na samu kaina da bin umarninsa duk kuwa da na san ba mutuncina ba ne, na zauna a motar ya rufe ya zagaya ya shiga ya tashi motar.

“Sunana Salees”

“Noor”

“Thank you”

Ya fada ba tare da ya kalleni ba, ni kuwa sai satar kallonsa nake baki ne mai dogon hanci ga yalwataccen gashin gemu da zaje gwanin sha'awa.

“A ina unguwar take?”

Na fada masa, har lokacin be kalleni ba sai da muka shiga cikin unguwar, nesa da gidanmu na ce ya sauke ni.

“Baki son na ga gidanku ne?”

“Ba kasafai ake kawo ni da mota ba, mutane za su iya wani zaton, kuma Baba baya son haka”

Ya juya ya kalleni first eye contact da muka yi gabana ya buga da karfi.

“Hakan yana da kyau, tarbiya ce amman da kika san Babanki baya so sai ki kiyaye, abu na biyu ki daina saka veil idan zaki fita, hijab ya fi mutunci, idan kina sha'awar veil ki saka babba wanda zai suturta ki, kina da kyau na zan maza da yawa sun fada miki haka, so ki suturta kyaunki ga wanda yake halalinki haka Allah ya fada”

“Na gode zan kiyaye”

“Idan kin min izini zan tsaya daga nan har na ga shigarki, saboda zan dawo ko kuma ki saka min number wayarki”

Ya miko min wayarsa na karba na saka masa numberta sai ya kira ni.

“Ki yi saving number zan kira ki anjima, na gode da kika shiga motata”

Na bude na fita ba tare da na ce masa komai ba. Shi kuma yayi reverse ya juya, na ciro wayar a jakata na yi saving number, ashe Kareem ya ga fitowa motar domin motarsa tana fake a gefen gidan makotanmu ne, ban lura ba sai da na karasa, gaba daya sai farinciki ya baibaye ni, ganinsa da na yi.

“Laa Kareem baka fada min zaka zo?”

“Laa Kareem baka fada min zaka zo?”

Ya kwaikwaye ni da wata murya kamar ba shi ba yana mocking dina fuska a hade.

“Ba ki da aiki sai raba Number, ki so wannan ki so wannan, ke baki ma san abun da kike so ba, baki san mai son ki ba, ke baki ma gajiya da halin maza ne?”

“Haka zan yi ta yi har na dace Kareem”

Na fada a shagwabe murya kamar zan yi kuka.

“Ba ni wayata”

Yana fada be jira na ba shi ya fisge wayarsa dake hannuna ya bude motarsa ya shiga.

“To ai line na yana ciki ka ba ni layina”

Banza yayi min ya ja motarsa baya ya bar ni tsaye na fara dora hannu a fuska zan yi kuka, ganin hakan ya saka tsaya da motar be tafi ba kuma be yi gaba zuwa inda yake dazun ba, ya dade a ciki sannan ya fito motar ya tako da kafa ya zo ya mika min wayar.

“Kalli wani mayafi da kika saka kika fita, haba Noor, kin saka duk raina ya bace Wallahi, idan kika sake shiga motar wani ko kika saka mayafi irin wannan kika fita, ban yafe miki ba, kuma mun bata ba zan sake kula ki ba”

Na karbi wayar ina kara bata fuska alamar zan yi masa kuka, i feel so childish when ever I'm near him, da wani ne ya fada min haka ba zan damu ba amman shi na ji babu dadi, kuma abu kadan idan yayi min sai na masa kuka nake jindadi. Motarsa ya koma rai a hade ya bar ni a gurin, sai da ya wuce na duba sai na ga babu liyi a wayar, ashe sim din ne ya cire a motar ya kawo min wayar kawai. Kamar na kwala ihu haka na ji a wane dalili zai karbe min layi ya tafi da shi.

Hayaniyar da na ji a zaure ne ya saka ni karasawa cikin gidan da sauri, Hana na zube a kasa tana rusar kuka Baba kuma yana ta zazzaga masifa.

“Shiyasa aka boye min, saboda tana auren ubansa, wato kar aka taba mutumcin aurenta ko? Bayan ni kuma ya taba mutuncin aurena”

“Me ya faru Hana?”

Hana nake tambaya sai Baba ya amsa min.

“Munafukar yarinya, daman ai uwarki ta koya miki kiyayya da ni, shiyasa ni baki son farinciki ba ruwanki da damuwa da uwarki kawai kika damu, ashe abun da ya kashe miki aure kenan amman kika boye”

“Baba me kake fada?”
Chapter 79 · 0% Book details