← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 82

Sashe 30

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fara karanta ayatul kursiyu ta tofa min a kai ta busa ido. Ban sani ba ashe ba daidai nake kallon mutane ba, idanuwan nawa juyewa suka yi ina kallon mutane a baibai. Ta rumgume ni tana kuka, sannan yan'uwanta da na Baba suka shigo suka zauna suna gaisuwar kamar yadda yan'uwan Aisha ma suke cike a gidan, ita ma kuka take tana gurnani ko'ina ana jinta sai hakuri ake bata wasu na addu'ar Allah ya sauke ta lafiya. Ni kuwa a zuciyata ba ni da makiyiya irin Aisha domin ita ce silar duk wata fitina a gidan Hafiz, ashe ma ba dadewa zai yi tare da ni ba, me yasa ta zuge min kunne bata bar ni na yi zaman aure kamar ita ba? Amman laifin ba nata ba ne nawa ne miyasa na dauki zugarta? Why?

Har aka yi addu'a uku ban daina ganin laifin kaina ba, kuma ban daina fargabar yadda rayuwa zame min ba bayan tafiyar Hafiz, na san kowa zai dora min laifi ne a gidanmu, kuma na cancanci haka ya kamata ayi min kowane kalar hukunci a yanzu. Na gane ba laifin kowa ba ne nawa, ni ce wawuyar da ban fahimci duniya ba.
Wani irin nauyi na ji an dora min ashe haka ko wace mace take ji idan ta rasa abokin rayuwa, ni kenan da ban dade da shi ba kuma ban haihu da shi ba ina ga wandanda suke da yaya kuma suka dade a tare? Wani abun da zan iya cewa tsana ce ko tashin jindadi na ga ganina fuskar iyayen Hafiz bayan sadakan ukun ita ce ta mutuwar auren.

Ina da tabbacin a cikinsu babu mai iya bada shaidar abun da ya faru indai ba Aisha ta fada ba, domin sun ce ba su san da sakin ba har sai da ta fada, amman sai na ga nuna min wani kallo, mahaifiyarsa na tambayar me ya hada mu har tana fadan danta mutumen kwarai ne mai mutunci mai rike amana, domin tun da ya auri Aisha ba su taba jin wani abu ba, yana zaune lafiya da matarsa.

“Waya sani ma ko bakincikinki ne ya saka shi sakin motar har yaje yayi hatsarin, kin saka na rasa mijina uban Yayana mai so na tsakani da Allah”

Na kalli Aisha dake maganar ina hawaye.

“Allah ya isa tsakanina dake, ke ce silar da Hafiz ya sake ni, Allah ya isa ban yafe miki ba”

“Mijina be san tashin hankali ba sai da ya aureki, daga sunan taimako, Wallahi Hafiz baya sonki shi be taba sonki ba daga ya taimaka ya auroki sai kika zo cikin gidan suna son cin amanarsa”

Mahaifinsa ya daka mata tsawa.

“Aisha ya isa haka, ko dai minene ya riga ya faru, Allah ya masa rahama, babu amfanin maido baya”

“Ai amana bata barin kowa, Allah ya masa rahama, ni dai ina son na tafi da Noor can gidana idan kun yi min izini, yarinya ce ba zata iya wanka ita kadai a gidan ba”

“Ai wanka be hau kanta ba domin ya sake ta tun kamin ya rasu, da wanka da gado duk basa kanta”

Mahaifinsa ya fada. Sai Aisha ta karba.

“Balle ma bata taba yarda da shi ba, kullum addabarsa take da fitina bata taba yarda ya taba ta har ya rasu”

Na kalleta ban ce komai ba na dauke kai. Yayan mahaifin Hafiz ne ya ce.

“Ko ma dai minene ba mu yanke hukunci ba, sai mun bincike malamai mun ji me ake ciki tukuna, ki tafi da ita din idan mun bincika duk abun da yake nan za mu sanar miki”

Yana maganar yana kallon Mama sai ta amsa da tohm. A bisa wannan muka fito daga gidan, wani abun da ban yi tsammani ba shi ne direba ne da mota ya daukemu daga gidansu Iyayen Hafiz zuwa family house din su Mama. Muna shiga kowa sai tausaya min yake suna ta shawarar inda zan zauna a gidan, domin sun ce zaman wanka wai sai da mai kulawa da mace, domin gidan Baba babu mata Hana kuma karamar yarinya ce bata san komai ba.

“Ki barta gurin Kawu Garba, matarsa bata da matsala zata kula mata”

“Na fa yi magana da Alhaji, shi da kansa ya ce ta zo ta zauna ba wani matsala”

Yayanta ya girgiza kai.

“Amman Hajara baki yi tunani ba, saure sati daya ki yi masa maganar kawo yarki a gida? Haba dan Allah”

“Wallahi Yaya ba ni na yi masa magana ba, tun da aka yi rasuwar na fada masa yace na shirya na zo matarsa ma sau biyu tana zuwa, to kuma jiya da aka yi sadakan uku yake min maganar cewa na maidota a gidan ta zauna tare da ni zata fi sanyi, saman da zaman gidan ubanta domin babu mai kula mata a can din, babu yadda ban yi amman yace na kawota ai kowa ya san lalura ce bata wuce kowa ba, kuma gidan gida ne babba mai yalwa zata iya yin sha'aninta har ya shigo ya fita bata sani ba, domin bangarena dabam bangaren matarsa dabam kuma bangaren nawa ma babba ne sosai”

“Aa ni dai ban aminta da hakan ba, kawai dai ya fada ne saboda kawaici, da dai kin hakura ki barta a nan din ta zauna idan ta gama wanka idan ya sake magana sai ta koma amman a yanzu ki barta a nan”

Cewar wata yayarta. Sai Mama ta ce

“Toh ai na ji suna fadar wai ba zata yi wanka ba, saboda ya sake ta”

Yayanta ya kalleni.

“Sakinta yayi? Yaushe?”

Mama ta fada musu komai sai dai ita ma ba zata iya fadar dalilin sakin ba. Ni kuma na gagara fadar abun da ya gani a jakata har ya zama silar lalacewarki komai.

“Ni fa yadda ba lura wannan matar tasa kamar ba ta Allah ba ce, duba yadda yake son kunyata Noor cikin danginsa”

“Na lura Wallahi Yaya, ai gata ga su idan wani za su kara aura mata sai mu gani, na san Noor bata jin magana amman a yanzu na lura wannan matar ta fi ta wayo, wata kila da zaman ya dade Allah kadai ya san me zai kasance”

Mama ta fada.

“Aa laifin duk na wannan yarinyar ne, ba mamaki taje tana masa hauka da nuna masa ita wacan take ba kin san halinta da shirme da shashanci to ya bar miki duniyar kin huta”

Cewar Yayanta, haka dai suka ci suka cinye ni dai bana iya cewa komai idona sai ciwo suke saboda kuka da na sha. Daman na san laifin a kaina zai dawo duk juyin da za'ayi ba zan taba wankuwa a idonsu ba. Daga karshe dai aka yanke shawarar bari a gidan Baba domin ya tsaya kai da fata ba zan zauna ko'ina ba sai a gidan, bayan har Kawu Garba ya ce zan zauna a gidansa.

A dole na dawo gidan da zama sai wani sabon kunci ya bude min kofa. Hana ta min magana ta kan ja ni da hira Yaya ya kan min magana amman Baba har lokacin fushi yake da ni, yar karamar rayuwar da na yi a gidan Hafiz ta dawo min sabuwa, ina tuna lokacin da ya siya min waya ko kuma yake rarrashina idan kuma na tuna abun da na yi masa na bacin rai sai na ji kamar zan runtse ido na mutu na huta, ina ma ace zai dawo na kyautata masa? Ina ma ace zai dawo ya fahimci ba ni na saka robar nan da magani a jakana ba. But the part da na tuna Aisha tace shi ma haya so na ya kan saka na ji wani iri, be so kuma ya aure ne? Saboda me? Ya san be so ya raba ni da mai so na kuma ya aure ni....

KAREEM POV.

Yana zaune a kan tool holding his best friend picture yana kallo, har lokacin baya iya kukan rashin abokinsa zuciyarsa tana nan da nauyinsa pain din ya fi karfin kuka, har gobe he can't believe abokinsa ya tafi ya barshi.

“Sun ce mutanen kirki ne suke tafiya da wuri, ka fini kirki har a gurin Allah domin baka aikata abun da nake aikatawa ba, kana kokarin tsare dokokin Allah, kullum burinka na daina abun da nake marar kyau, a lokacin da ka fahimci bana cikin farinciki sai ka fara gina tubalin matso min da shi kusa, maganar mu ta karshe ma umanine kake kokarin cikawa saboda ka faranta min, ba zan taba barin iyalinka su shiga kuncin rashinka ba Hafiz”

Yana maganar idonsa suka fara tara hawaye, at the same time Yusura ta turo kofar dakin ta shigo. Kusa da shi ta karaso ta tsaya sai da ta kalli hoton dake hannunsa sannan ta kalli Kareem ta ce

“Kyautatawa abokin zama, makoci ko aboki wajibi ne gudun kar ya tafi a dawo nadamar da bata da amfani”

Ya aje hoton ya rufe drawer madubin.

“A iya sanina Noor bata son Hafiz ko kadan, saboda ya raba ta da wanda take so kuma ya aurenta alhalin shi ma kansa ya san baya sonta kamar dai ke, banbancin mu da su, ba iyaye ne suka cilasta ba, duk wani yunkuri da yake saboda ni ne, daga karshe kuma sai abun ya fada kansa, ashe saboda ya tafi ya bar ni da bakinciki kasa cika masa burinsa ne da ban yi ba...”

Ya dago ya kalleta yana murmushi.

“Kin san banbancinki da Noor? Ta fi ki wayo ta fi ki imani da yardar da kaddara, ta fi ki tsoron duniya, yarinyar nan bata iya munafurci da pretending ba, tsabar saka shi da ta yi a zuciya na nesan da ta yi na kwana biyu sai da ta yi mafarkin mutuwarsa tun kamin a fada mata ya rasu, a ranar da za a binne Hafiz na ga wani abun da ban yi zato ba gurin yarinyar nan, ta rike karagarsa tana kuka, na tabbatar da ni aka sanar miki na mutu murna zaki yi...”

Ta yi murmushi.
Chapter 30 · 0% Book details