← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 82

Sashe 52

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ko dai baki taba sanin komai ba sai akaina? Ko kuma tsananin gyara ne?”

Nan ma ban amsa ba.

“Ba zaki amsa min ba?”

“Ban taba ba”

Ya bude ido sosai irin na mamakin nan.

“Mijin da kika aura ba?”

Ba tare da tunani ko fargabar komai ba na fada masa irin zaman da na yi a gidan, sai ya cika da mamaki yana ta yaba hakurin Hafiz.

“Wannan shi ne garabasa, amman duk da haka gaskiya mutumen da kika aura mai hakuri ne, ni ba zan iya hakuri da wannan ba ko kadan, bana iya daukar wannan”

Na masa murmushi kadan ina mamakin idan baya iya hakuri taya yake iya wata hudu, uku a nan kamar yadda ya fada ba tare da matarsa ba. Ko da yake irin wannan hakurin kamawa take na dole ne. Shiyasa ya damu ya kara aure.

Akan ce aure dace ne, a yanzu kam ina ganin kamar na dace domin Abdull yana mutunta yana nuna min so da kauna, idan zai fita zan raka shi har gurin motarsa idan ya dawo kuma na tarboshi zai dawo min da tsaraba a kullum haka yake. Girkin ma da ke babu dadi ko ya chabe wani lokacin haka zai ci ko ya siyo wani abu be taba nuna min ransa ya bace ba ko kuma ya rufe ni da fada.

Abu daya ne zuwa biyu illar Abdull, shi ne an rashin son ibada, da azuba sai dai na yi sallah na bar shi idan ya farka misalin 8 ko 7 yayi duk yadda zan tashe shi ba zai tashi ba. Na kam lura idan ya dawo daga aiki yana rama sallah azahar kamin yayi La'asar wani lokacin ma sai ya kai magariba yake hadawa yayi, a tsawon zamana da shi ban taba ganin ya bude kur'ane ko da a wayarsa ne ya karanta ba. Sai kuma rashin kishi domin baya son ina saka hijab idan zamu fita shakatawa ko siyen wani abu ko kuma idan abokansa suka zo, yana yawan fada min wai shi yana son abokansa su san wayayin mata yake aure, ya nuna min rayuwar Lagos rayuwa ce da babu ruwan kowa da kowa.

Kuma na lura haka din ne, domin idan muka fita ina gani mata da wando ko guntun skirt, ni kuma ina dora hakan ne a mu'auni na banbancin yare, addinin da kuma al'adarmu ba su zama daya ba. Dole hakan ya haifar da banbancin abubuwa dama, amman shi ya kasa gane haka ya dauki rayuwar Lagos ya sakawa kansa kamar ba bahaushe ba.
Ba mamaki ta kan iya yiyuwa saboda yawan abokai mata da yake da su ne, yana da females friends da yawa, kuma suna saka kananan kaya wanda kusan ita ce 70% na suturar mutanen garin.

Ba illa ba ne idan ya bukaci na saka masa a gida, idan zamu fita sai na saka after dress a sama ko gown. Duk yakin duniyar nan da zan yi ba zai taba yarda na fita da hijab ba, sai dai guntun mayafi kamar wata budurwa. Ko da yake abayar ta kan rufe min jiki, gashi ni kuma din ba mai kiba bace balle na ce ta bayyana surata.

Mun sha ziyara har mun gode Allah bokansa sun yi ta kawo mana ziyara sosai, musamman na gurin aikinsu maza da mata, idan za su zo hotel yake tafiya ya siyo abinci, kamar kala biyu ya kawo na zuba a kulolin da ya siya min sabbi domin ban zo da komai ba, sai tufafi su ma atamfa ne sai laces kananan kayan a garin ya siya min su.

Ba ni da wata matsala da Abdull sai ta rashin sallah kamar yadda na lura tun farkon zuwana gidan.
Ina jin nauyin fada masa kuskurensa gudun kar ya fahimci a abun abaibai, har sai da na fahimci ba shi da niyar gyarawa sannan na fara nuna masa masa muhimmancin sallah da illar da barinta yake kawowa, cikin hikima da dan gutun ilmina.

Idan na fadi hadisi ko karatun wasu malamai akan sallah sai na ji ya karasa min, da alama ya san komai ba zahili ba ne, kawai dai shedan yayi nasara a kansa ne ta wannan bangaren. Na kara jajircewa ina tunatar da shi a duk lokacin Sallah ko da kuwa baya gidan. Ya kan dan motsa yayi Sallah a cikin lokacinta wani sa'in, musamman idan weekend ne yana gida tare da ni a tare muke yi. Sai dai a yadda na lura kamar takurawar da nake masa bata masa dadi kawai dai yana min kawaici ne yana yi saboda yana son farincikina.

A kwana a tashi hausawa suka ce hasarar mai rai, a haka mu ka kwashe wata uku a gidan, ni kam kadaici ya hana ni na saba da gidan har yanzu, gashi ta inda muke makota na duk yarbawa ne babu wasu kuma ibo ne bana jin yarensu basa jin nawa, sai dai a yadda Abdull ya fada min yawancinsu suna jin turanci, duk da haka dai be amince min na leka gidan kowa ba kullum ina ciki gida kamar kifin gwangwani.

Ta wani bangaren kuma ai yana da gaskiya zaman aure na zo ba yawo ba, a yanzu kuma bana bukatar duk wani abu da zai daga hankalin mijina ko rayuwar aurena. A haka na cije na daure na yi zaman da ban tsammaci zan iya ba, a garin da ba ni da kowa sai Allah, sai mijina wanda nake gani a matsayin farincikina a yanzu.

Sai da na cika wata uku da sati biyu cif sannan ya yi min izinin tafiya gida domin duba yan'uwa da yan'uwansa. A tare da shi muka tafi ba saboda yanayin aikinsa ba su ba shi izinin tafiya, kuma na lura kamar baya son zuwan ma, zaman garin ya fi masa fadi fiye da Kano a yanzu.

Ticket din jirgi ya siya min daga Lagos to Kano, da kansa ya kai ni Airport ya tsaya har sai da jirginmu ya tashi, ina sauka na kira shi na fada masa sai ya turo kanensa ya dauke ni, gidan Safeena aka fara kai ni, wanda zan iya kira da gidan mijinmu a yanzu. Daman ya fada min gidan yake son na fara sauka saboda mu san juna ni da ita.

Abun da ya kamata yayi tun kamin mu bar garin be yi ba sai a yanzu. Gida ne mai fadi sosai bangare daya ne a gidan dayan bangaren kuma zallar fili ne da ba a gida komai ba, da alama a nan zai min nawa bangaren idan mun tashi dawowa garin gaba daya.

Kanensa ya wuce gaba ya shiga da sallama sai ta amsa masa da karfinta da far'ata.
Ina rangada tawa sallamar sai murmushin dake fuskarta ya gushe, waya sani ko be fada mata zan biyo ba, wata kila bata san da zuwan nawa a gidanta ba. Ko ma dai minene oho mata ni ma dai gidan nawa mijin ne bata fi ni iko da gidan ba.

Ban jira ta min izini ba na zauna ina kallon falon da aka kawata yayi kyau sosai kamar na sabuwar amarya, hotunan Abdull da yaransa ne suka yi ma falon ado, domin frame ne babba mai wadatar da mai kallonsa. Na fi maida hankali gurin hoton karamin danta da yake kama da Kareem, kuma yake kama da ita, shi kadai ya fita dabam da sauran yan'uwansa dukansu bakake ne kamar mahaifinsu, sai dai farinsa ba mamaki ba ne domin ita ma fara ce.

“Duk suna makaranta, Abulkhari kuma bachi yake”

Ta amsawa kanenta dake tambayar ina yara. Kamar dai yaron ya ji me ake fada sai ya fara ihu, ta tashi da sauri ta shiga wani daki dake fuskantar dayan ta dauko shi ta fito. Yaro ne dan wata biyar da kwanaki fari sol kamar dai ita, ta zauna a kujera tana rarrashinsa. Sosai nake ganin kamarsa da Kareem, wata kila dai saboda na san alakar da ta taba shiga tsakaninsu ne zuciya yake raya min abun da be dace ba kuma bana fatan ya faru.

“Amarya ya angon na ki?”

Na dago daga tsananin kallon da nake yi ma danta na kalleta.

“Lafiya kalau muke, ya muka same ku?”

“Muna cikin aminci da kwanciyar hankali”

Ta amsa min fuska babu annuri tana min kallon biri ina mata kallon bishiyar hawa.

“Dawood a kawo maka abinci?”

Ta tambaye shi kadai ba tare da ni ba.

“Aa ni wuce zan yi sai dai kanwarki idan zata ci”

“Kanwata tana gidanmu tana taya iyayena aiki, kanwata ai ba zata aure min miji ba, kuma ta ne mi daga min hankali”

“Idan har ni na daga miki hankali, to daman can cikin tashin hankalin kike na abun da yake boye a zuciyarki, ni kan aurena sai dai ya haifar muku da kwanciyar hankali ke da mijinki”

Na bata amsa daidai da furucinta. Dawood ya mike tsaye

“Miye wannan abun dan Allah? Ku da za ku hada kai ku kwantar masa da hankali, cewa fa yayi na kawo ta ku gaisa miye na wasu kananan magana dan Allah? Haba”

“Har a bada ba zan hada kai da macijiya ba, ki sare ni a gaba ki sare ni a baya kuma ki yi sammanin hada kai da ni, ai kin yi shuka ne a idon makurwa, shi dai da ya ji zai iya da yaje can yayi ta yi, ma san abun da maza suke gani a jikinki da suke rawar jiki, abu kamar daurawa muciya zane”

Na yi murmushi kai kace ban ji zafin maganar da ta jefa min ba.

“Abun da baki da shi, shi suke hangowa”

Sannan na mike tsaye ina tabe baki.

“Ni ba fada ya kawo ni ba, mijina yace na biyo na gaishe da matar kuma na cika umarni, kin san ni ban iya cin amanar miji, Malama kin ga tafiyata”

Har na juya sai kuma na juyo na kalli yaron dake hannunta.

“Allah ya yara abulkhari yayi masa albarka, sauran yaran kuma idan sun dawo a ce new Momynsu tana gaishe su”

Ta aje yaron ta mike tsaye a lokacin da Dawoo ya kai kofa ya bude min yana fadin na zo mu wuce.
Chapter 52 · 0% Book details