← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 82

Sashe 59

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya san dai yana tsaka da tuki hudu ya sauko masa daga lokacin kuma be sake sanin inda yake ba, maybe ya hadari yayi, ba ma wata kila idan be yi hadarin ba ai ba za a kawo shi nan a aje ba. But why ICU shi da be ji ciwo ko daya a jikinsa ba, domin be ga wani guri da ya ji ciwo bako ya bugu. Hannu ya mika ya janyo files dinsa ya bude ya duba. Daman ya sani zama unconscious or in a critical condition ke saka a aje mutum a gurin. Ya duba ya gani kwanansa biyu a dakin amman be sani ba sai yau da ya farka, babu wata rauni a jikinsa but hankalinsa da numfashi sun yi nisan da an dauka barin duniyar zai yi.

Ko me ua buga oho, ya san dai hakan baya rasa nasara da damuwar da yake ciki, kusan ita ce silar faruwa komai. Ya aje files din ya shafa kan dansa dake sanye da uniform din makaranta yana murmushi ko dan yaran nan yana bukatar rayuwa. Areef ya bude ido sakamakon shafa kansa da Dadynsa yayi.

“Hey young Man”

Yaron ya tashi zaune ya matsa ya rumgume mahaifinsa yana murna.

“Dady ka farka”

Kareem ya saka hannu ya shafa bayansa yana murmushi kamin wani azababben ciwo ya ratsa zuciyarsa har sai da ya ji ta motsa kamar ta bar muhallinta.

“Oh...”

Ya furta Areef ya dago ya kalleshi.

“Dady minene?”

Kareem ya murmushi.

“Ba komai ina Tine”

“Suna waje bari na kira ta har da Mama ma tana nan, kullum zai mun zo kana bachi, Hajiya tana nan ita da Uncle Aaryan nan yake kwana”

Har ya isa kofa sai kuma ya juyo ya kalleshi.

“Daddy ma kullum yana zuwa, yana yin addu'a yana tofa maka, Dady kuma Momy ta kwashe kayanta gaba daya ta koma gurin Hajiya an bata bangare daya tace tare zata zauna da mu”

Kareem ya daga mishi kai. Areef ya fita da gudunsa, Kareem kuma ya mike tsaye ya fito daga dakin da kafafuwa normal yake jin kansa kamar be yi hadari ba. Ya san yadda asibitin take fa kuma dokokinta sai ya canja ma kansa daki bayan ya gaisa da ma'aikatan dake ta masa sannu Doctor dake duty yana da tsokarsa yana fadin ya bari yayi aikinsa yanzu shi majinyaci ne ba likita ba

Files din dake dayan dakin likita ya dauko ya dawo da su sabon dakin da Kareem yake, sannan aka bawa visitors damar shiga, yan'uwa na ta shigowa suna masa sannu na nesa kuma suna kira a waya. Duk wani motsi nasa yana kan idon Yusura kallonsa take sosai kamar bata taba ganinsa ba, sau daya ta yi masa ya jiki bata sake ba sai dai duk dagowar da zai yi sai ya ga tana kallonsa. Tun daga ranar kuma bata sake zuwa ba duba shi har aka sallame shi after four day's da yayi a asibitin.

Ranar da zai bar asibitin babu yadda Hajiya bata yi ba akan ya dawo family house ya zauna har sai jikin ya kara warwarewa da kyau saboda a can gidan babu kowa a yanzu amman ya ki, domin baya son zama gidan zai fi sakewa a gida ko da kuwa ba shi da lafiyar balle baya jin ciwon komai a jikinsa. Taya zai saki matarsa ta tare a family house dinsu shi ma ya koma can ya tare kamar mace.

Ba karamin godiya yayi ma Allah ba lokacin da Aaryam ya kai shi gidan ya ga yadda gaban motarsa ya lalace, bayan ma ya bugu ba karamin accident yayi ba amman Allah ya kawo masa sauki tun da be ji rauni a ko'ina ba. Aaryam ya fada masa yadda hadarin ya afko sai da ya cika da tsananin mamaki.

“Babu wanda ya dauka zaka rayu fa, Wallahi duk mun tsorata, babba mota ka buga irin mai zube yashin tefa. Mai motar yace yana ta maka horn domin ya ga yadda ka zo da gudu amman baka tsaya ba sai da ka bugu shi, gashi ita kuma wata motar ta bugi taka a baya, daker aka fito da kai motar babu rauni amman baka numfashi hankali ya bace gaba daya, asibitin ma sai da aka yi da gaske sannan numfashinka ya dawo”

Yayi murmushi.

“Kwana ne ba su kare ba, da lokacin yayi da ba zan farka ba, Alhamdullahi”

“Gaskiya mun auna arziki, da mun rasa ka rayuwa ba zata yi dadi ba”

Kareem ya kalli falon ya mike tsaye.

“Wata rana dole za ku rasa ni Aaryan dole kuma ayi hakuri da rayuwar”

“Haka ne, amman ba ma fatan zuwanta yanzu, Allah dai ya kara maka lafiya”

“Ameen”

Aayam ya sauke ajiyar zuciya.

“Yusura da Khadija sun sha kuka, Hajiya har sai da aka zuba mata ruwa, ban taba ganinta cikin tashin hankali irin na ranar ba, babu wanda be yi kuka ba sai ni”

Kareem ya juyo ya kalleshi.

“Eh kai mai zuciyar fir'auna ko?”

Aaryam yayi dariya.

“Ai duk abun da zai saka namiji kuka ba karamin abu ba ne, Allah dai ya tsare faruwar hakan”

Dinning Kareem ya dafa.

“Yusura bata fada muku abun da ya faru ba?”

“Ta fada mana, har ta kwashe kayanta ai Hajiya ta bata bangare daya ta zauna saboda ta samu sakewa ita da yaranta, Khadija da Nana sun koma bangarenta, na yi mamakin kukanta wata kila ita ma ta dauka mutuwa zaka yi”

“Daddy be ce komai ba a game da rabuwarmu?”

“Ba ka da matsala da shi, tun a lokacin da aka fada min halin da kake ciki sai na same shi na yi masa bayanin komai, saboda mu samu goyon bayansa idan zaka kara aure, ashe Allah da kai ba, amman dai ya sani kuma ya daga maka kafa. Kawai addu'a yayi Allah yasa hakan shi ne mafi alheri”

Dogon numfashi Kareem yaja ya sauke ya daga kansa sama.

“Ameen”

A gidan Aaryam ya wuni saboda ya ragewa dan'uwansa Zango har sai da yamma ta yi sannan ya tafi bayan sun sha hira sosai. Kareem ya juyo kenan daga rakiyar da yayi ma Aaryan bakin kofar falon sako ya shigo wayarsa.

“Wata kila ni ce silar hadarinka? Shin ka aikata hakan ne da nufin kashe kanka? Ka ji zafin gaskiyar da ka sani ne Kareem? Ni ma daga baya na gane ban kyauta ba na yi kuskure, amman na maka alkwari babu wanda zai ji wannan, ina zuwa dubaka asibiti a kullum amman bana samun damar shiga na ganka saboda yan'uwanka da matarka suna gurin. Yau kuma na tafi aka ce an sallame ka na jidadin haka kuma na ji tausayinka na yi bakinciki abun da ua faru da kai, ina kaunarka Kareem Wallahi ina kaunarka”

Ya goge sakon bayan ya gama karantawa, ko ya fada mata yayi hadarin ma oho, falon ya shiga ya kwanta akan kujera ya rufe ido yana maida numfashi a hankali.

NOOR POV.

A lokacin da cikina ya shiga wata bakwai na samu sauki abubuwa da yawa na daina amai da kwadayin sosai, ko zabar abinci. Har ta kai ni nake shirya abun karyawa da safe da kaina. Domin yanzu Hana ce mai tsananin bachin safe idan ta gama sallah ta koma ta kwana sai kace ba yar makaranta ba. Kullum sai ta buga latti saboda bachi, har tausayi take ba ni domin na san wahala ce ta yi mata yawa, na aikin gida da take ga kuma karatu da basa daga kafa.

Abun sai ya zame mana kamar duty ni ce mai saurin bachin dare ita kuma ta yi rankon na safe. Domin da zarar na gama sallah Isha'i Abdull ya kawo lemun juice da yake hada min a kullum, domin likita yace na rika cin yayan itatuwa sosai a yanzu fiye da kayan zafi ko kwadayi irin su madara da danginsu. Saboda kina yana ta girma ne a yanzu, ban yi kasa a guiwa ba na rumgumi kayan marmari, kullum sai na ci da dare kuma sai Abdull ya hada min lemun juice da juicer da ya siya gurin Khadeeja Candy Store, zallar ruwan fruit take matsewa sai dan sukari kadan da yake kasa min ko kuma abar da bana so wato zuma, wani lokacin saboda bakin nawa ya saba da zaki idan babu ba zan sha ba. Da zarar ya hada min na sha sai bachi yayi gaba da ni, ko motsi ba zan yi ba sai safe.

Ina tsaka da shafa face cream ya shigo dakin ya aje min cup din natural orange juice. Sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko kayan bachinsa ya saka.

“Kina bukatar wani abu?”

Na kalleshi kamar na ce ina da bukatar ka, yau wata shida kenan ban hada shimfida da mijina ba, tun cikina na wata daya da yan kwanaki ya nade sha'awata ya jefar saboda kawai na ki yarda a zubar da cikin. Sai kuma wata zuciyar tace na daure mana na zuba masa ido tun da haka ya zaba.

“Aa”

“Okay to zaki yi kallo?”

“Aa bachi zan yi”

“Yanzu ai kin lalace da bachin dare, da dare yayi sai bachi kamin tara na dare ta yi har kin kai Morocco, Allah yasa ba raguwa ko rago zaki haifa ba, wannan lalaci yayi yawa”

Na yi dariya mai sauti ina masa gwalo.

“Bachin yana min dadi, da na kwanta bana sanin me duniya take ciki sai na farka”

“Asha bachi lafiya Mom Unborn”

Ya fice ya bar ni na cigaba da shafa face cream din, sai da na gama sannan na dauki lemun juice din na sha kadan sai na ji zakin zumar yayi min yawa gashi ba son zuma nake sosai ba, haka na saka dole na tashi na shiga bathroom na kunna tap na tara lemun na kara ruwa kadan, na kashe juyowar da zan yi santsin tile ya kwashe ni, aiko ba shiri na saki kofin na rike tab din sai kofin ya fadi kasa lemun ya zube.

“Allah ya tsare na auna arziki yau kai...”
Chapter 59 · 0% Book details