← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 82

Sashe 13

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk maganar da nake Hana ce take amsa min shi dai be sake cewa komai ba sai dai ya kalleni. Ina zaune a gurin har ya gama wankin ya shiga yayi wanka ya fito Hana ta gama girkin ta zuba mana, na samu cin abincin da yawa kasancewar a tare muka ci da ita kuma muna ci muna hira. Bayan mun gama na yi alwala La'asar na yi sallah na zauna akan tabarma ina jiran shigowa Baba har lokacin na gagara fadawa Hana ko Yaya dalilin zuwan nawa. Yaya Nabil yana yi alwalar La'asar ya fice daga gidan, sai ya rage daga ni sai Hana ita din ma na kasa ce mata komai, gani nake kamar yayi wuri na fara fadar matsala wata kila ba za su yarda da ni ba. Shigowar Baba ta saka hantar cikina kadawa na kasa samun sukunin zama sai motsi na ke irin na marasa gaskiya.

“Ahh Yau Norriya ce a gidan na mu? Maraba maraba da zuwa Nooriyya an tuna da gida kuma?”

Na yi murmushin karfin hali na yi masa sannu da zuwa ya amsa Hana ta dauko masa kujera ya zauna kusa da ni yana kallona far'a kamar na zo masa da albishir.

“Ya gidan lafiya? Ina mijinki yana lafiya ko?”

“Lafiya Kalau Baba”

“Tun dazun kika zo?”

“Eh da rana na zo”

“Madallah kin ci abinci?”

“Eh na ci Baba”

“Haka ake so, Mijin na ki dai yana lafiya ko?”

“Eh Baba”

Na amsa cikin rashin sakewa, tsoron duka ko zagin da zan sha a gurin Baba ya hana ni fada masa damuwar da na zo da ita, haka na hade hannu ina kallon Baba yana cin abinci yana fada min wai kwanan baya ya kira Hafiz a waya be daga ba.

“Ina ta saurarensa yace zai kira ni kuma be kira ni, kuma na kira shi be daga ba”

“Wata kila baya kusa da wayar ne”

“Ni ma na yi tunanin haka, amman ai ya kamata ya kira idan ya ga kiran nawa, amman dai ba komai ai zai zo daukarki ko?”

“Eh zai zo, yace ma na tafi gurin Mama na dawo da wuri kamin ya zo”

Na yi karya ina jin kamar a gurin mahaifiyata zan fi samun sakewa na fada mata damuwa fiye da shi, da zai iya rufe ni da fada ko duka.

“Ah aha shi ne kuma kika zauna har yanzu? Tashi ki tafi mana ga yamma na yi sai ki dawo da wuri karki tafi ki zauna fa, ki dawo da wuri kar zo be same ki ba”

“Tohm Baba, amman ba ni da kudin abun hawa”

Ya saka hannu aljihu ya ciro tari bakwai ya ba ni.

“Tashi ki tafi, karki jima”

Na karba da hannu biyu na dauki jakata na mike tsaye ina kallon kanwata.

“Tafiya zaki yi”

“Eh ba zaki raka ni ba Hana?”

Jin haka ya saka ta shiga daki ta dauko hijab ta dora a saman zanen da take daure da shi, na yi ma Baba sallama da zimmar dawowa idan na tafi na fito Hana ta rako ni muka fito. Ko kadan ban yarda na daga kai na kalli kofar gidansu Zafeer ba, saboda ji nake kamar zan ganshi ne ko ya ganni hakan kuma ba zai mana dadi ba dukanmu. Har bakin Titi Hana ta rakoni na tari Napep ina tsaka da ciniki da shi na ji ta dafa ni.

“Noor Wallahi yanayinki kamar akwai matsala!”

“Akwai, ki min addu'a kawai Hana Allah ya min mafita”

“Ameen, je ki dawo sai mu yi magana”

Na daga mata kai na shiga Napep din. Yana tafiya ina hawaye har muka isa gidansu kakaninna. Farincikin ganin mahaifiyata da yan'uwanta da kuma su kansu yan'uwan mahaifiyata da suka yi farinciki ganina ya mantar da ni yar damuwar da na zo dauke da ita. Suka kawo min abinci har kusan hudu kasancewar gidan family house ne mai bangare dabam dabam irin na mutanen da da ake zama tare da jikoki da yaya da yan'uwa. Sai da na kebe da mahaifiyata sannan damuwa ta dawo min a take yanayi na ya canja.

“Ba zaki ci abincin ba?”

Mama ta tambaya, sai na kalleta ta yi jikinta ta yi haske kamar ba ita ba da alama hankalinta yanxu ya fi kwanciya fiye da lokacin da take gidan baba.

“Na ci abinci a gida kamin na zo”

“A gidan Baban na ki ko mijin? Ance ubanku ma aure zai yi? Kuma mai kudi wai Mama?”

Ta yi dariya.

“Eh ke ma ai Hana tace min aure zaki yi Mama”

“Eh In shaa Allahu jumma'ar nan ta sama za a daura auren, ina son daman sai an kusa na shirya na tafi na ga dakinki, yan'uwa sai yabawa suke, na san dai baki son auren amman ya miki komai Noor domin ubanki ba zai iya zuba miki wannan kayan ba, duk da dai ban gani ba amman ina jin ana ta yabawa”

Na yi shiru na sauke kaina kasa.

“ina abokiyar zaman naki kuna lafiya ko?”

Na dago na kalleta.

“Lafiya Mama sai dai...”

Sai kuma na yi shiru, ita ma shirun ta yi tana kallona.

“sai dai me? Noor karki fara dan Allah, yaushe aka miki auren balle har ace matsala ta fara shiga, shi zaman aure dan hakuri, kina kallon yadda na sha wahala gidan ubanki balle wannan dake kaunarki kamar ya hade, na san halinki Noor shiyasa tun farko na gargade ki, wauta da sakarci sun miki yawa, abun kadan zaki iya ganinsa ba daidai”

“Wata kila kuma ni nake da gaskiya Mama”

Na fada murya kamar zan fasa kuka, idona na tara ruwan hawaye. Sai ta hade min rai ta dauke kai.

“Bana son na ji, indai shi ya kawo ki gidan nan, to tashi ki tafi ba ki zo ganina cikin dadin rai ba sai zaki kawo min wani korafi? Je ki samu Babanki shi da ya daura miki auren ki fada masa, sai ni da kika raina, salon ace ni yanxu zan yi aure ke kuma na kashe miki aure? Noor kin san iya idon da yake kanki kuwa? Ana kalle da ke ana jiran wani abu ya faru, aure kasa da wata daya ki fara zuwa zaki fada min an miki ba daidai, daman miki daidai sai Allah Noor ki rufa ma kanki asiri ki zauna dakin mijinki, in har kika ce haka zaki fara da shi, to ko ba zaki taba zaman auren ba, ni bana son na ji komai tashi ki koma dakinki”

Kamin ta gama bayanin kuka ya gama cin karfi, haka na tashi ina share hawaye na saka hijabina na dauki jakata na fito gidan ana sallah magariba. Hanya na kama na rasa ina zanje, yanzu kuma waye zan fadawa kukana? Ko dai na tafi gidansu? Kuma da wane idon zan kalli iyayensa? Me zan fada musu cewar ya ga wani abu a jakata yayi fushi da ni? Wata kila ya ji haushin haka ko kuma su ma su kasa fahimta kamar yadda shi ma be min uzuri ba, gashi ban san gidan na su ba. Ko dai na koma gida? Kuma idan na koma haka zai cigaba da yi min na san zuwa yanzu kuma ya dawo be same ni a gidan ba. A take zuciya ta raya min na tafi gidan Kareem na fada masa halin da nake ciki na fada masa abun da abokinsa yake min wata kila zan samu mafita, domin ina jin babu dadi yadda ya wofintar da ni babu ruwanshi da ni akan laifin da ban aikata ba. Mai napep din da na shiga be sauke ni ko'ina ba sai kofar gidan Kareem. Na bashi kudin Napep 400 sannan na doshi kofar na buga mai gadin ya bude min.

“Dan Allah Kareem yana ciki?”

“Gaskiya yana ciki be dawo ba, amman dai iyalinsa tana nan”

Sanin halin matarsa na rashin maraba da mutane, da kuma kokarin fasa min kai da ta yi a wacan karon ya saka ban yi sha'awar shiga ciki na zauna a gefen gate din cikin flowers din da suka yi ma gidan ado. Ina zaune a gurin har aka kira sallah Isha'i aka sauko daga sallah sannan motar Kareem ya tsaya a gaban gate din yana horn. Na mike tsaye da sauri na nufi gilashin motar na kwankwasa sai ya sauke farin gilashin yana kallona.

“Noor...”

“Na'am”

Na amsa ina hade hannayena waje daya yanayina na karantar da duk wanda ke kallona damuwata.

“Ke da wa kika zo nan? And lafiya?”

Hawaye ya fara sauko min.

“Kareem ina cikin matsala, kuma ina jin kai kadai zaka iya taimaka min, dan Allah karka ce ba zaka saurereni ba, ina jin tsoron Baba na kasa fada masa kar ya kure ni ko ya min duka, Mama kuma ta ki ta saurare ni”

Ya dan tsaya kallona kamin ya ce.

“Shiga cikin gida”

Na wuce sai da na fara shiga sannan na shigo da motarsa ya faka kusa da ni, ya bude ya fito ya kalleni.

“Hafiz ya san kin zo nan?”

“Aa be sani ba”

“Me ya faru?”

Na hade yawu.

“Baya shiga bangarena yau kusan sati biyu, baya min magana matarsa ma fushi take da ni, ba ni da walwala Kareem gaba daya na ji na tsani gidan na tsani kaina”

Ya ciro wayarsa ya fara tabawa.

“Wani abun kika masa ko?”

“Ban masa komai ba, kawai dai wani abu ya gani a jakata ya fara fada....”

Na fada masa komai cikin kuka.

“Minene to?”

Na Cire jakar daga kafata na bude na dauko maganin da balloon din na mikawa Kareem.  Sai yaja baya da sauri kamar ya ga abun kyama.

“What the F**uk, miye hadin ki da wannan Noor”

Na kalli maganin na kalleshi.

“Na minene? Ban san maganin miye ba Wallahi, wannan ballom din ma ban taba ganin irinta ba, Wallahi Wallahi ban san ko abun miye ba Kareem”

“To ya aka yi kika samu?”

“Ban san ya aka yi ba kawai shi ya ganshi a jaka”

“Wannan maganin hana daukar ciki ne, wannan kuma Condom ne”

“To me zai hada ni da maganin hana daukar ciki? Wallahi ban san shi ba ban taba ganinshi ba ma, ban san inda aka siyarwa ba, shi condom din me ake yi da shi?”
Chapter 13 · 0% Book details