← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 82

Sashe 37

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Nabil an tafi ko? Ya zo min bankwana ai, Allah yasa ayi karatu cikin nasara”

“Ameen”

Na amsa ina daga kai na kalli Ridwan dake shirin tafiya.

“Zaki dare nan?”

“Aa idan dai ka yawato ka samu abun da zaka samu sai ka dawo ka dauke ni mu tafi gida”

“Yaya Ridwan har yanzu Napep din kake ja?”

“Toh ya za'ayi abincin a nan yake”

Ya amsawa Hana dake tambayarsa domin tun tashinmun, Yaya Ridwan ba shi da wata sana'a da ta wuce jan Napep, da ita ya rike gidansa ya yaransa da matansa biyu har ma da mahaifiyarsa.

“Allah ya taimaka”

Cewar Umma, dukanmu muka amsa da Ameen sannan ya fice. Shimkafa da miya Umma ta girka saboda zuwan Anty Larai, bayan mun ci mun yi sallah Hana ta dauki awara ta fice gurin sana'ar da ta zame mata dole, ni kuma na zauna da Anty Larai muna ta hira, a cikin hirar nake gutsura mata irin zaman da muka yi da Aisha da yadda yan'uwansa suka jajirce ba za su ba nu gado ba.

“Daman can Allah ya gani, zuciyarta bata natsu fa yarinyar nan dari bisa dari ba, mata makircinsu yana da yawa, ke kuma ba wayo ne da ke ba kuma babu mai tsawata a tare da ku, dama ace irin gidanmu ne da muke hade kin ga wani abun ko dan ganin idon uwar miji dole a bar shi”

“Ni kadai nake zaune kuma kowa da bangarensa, amman hakan be hana ta cutar da ni, gashi ya yarda da ita, komai aka fada masa akanta baya yarda”

“Ki barta da Allah, yanzu ai mai rabawa ta raba, Allah ya ba ki na gari ita kuma sai ta je can ta karata”

Na yi shiru ina zane a hannuna da karen tsintsiya, kamin na kira sunan Gwaggo.

“Anty Larai”

“Na'am Khadijatu”

“Anty Larai, alfarma nake nema a gurinki, na san Baba yana jin maganarki, dan Allah ki roka min shi yayi hakuri yace ya yafe min na yi magana da Zafeer”

Na kora bukatar tawa ne ba tare da na kalleta ba, domin ina jin nauyin kallon idonta a yanzu.

“Zafeer din ya dawo ne? Aiko ya kai masoyi kuma lallai yana sonki da gaskiya bawan Allah nan”

“Be dawo ba, yana da zuciya sosai wata kila ba zai sake sona ba har abada, amman ni ina son a duk lokacin da na ganshi ko kuma na samu dama na masa bayanin da zai gamsar da shi cewar ba wai na ki aurensa saboda ba shi da kudi ba ne, na lura yan'uwansa har yanzu ganin suke kudi na bi na bar Zafeer”

“Idan har yana sonki da gaske zai dawo, ai mai sonka be ganin ramar ka, be ganin tsufanka, kuma shi ma mahaifinku ai be dace ya shata muku layi mai kauri irin wannan ba, saboda zuciya bata da kashi”

“Dan Allah ki masa magana, yace ya yafe min”

“Zan mishi magana idan ya shigo, noor har yanzu kina son yaron nan ko?”

Na daga mata kai ba tare da boye ko jin kunya ba, zan iya fadar ina son Zafeer a gaban, duk kuwa da na san a yanzu yayi min nisa. Sai na ji ta yi dariya tana buga bayana.

“Aiko da har ina cewa Ridwanu ya shigo ko Allah zai ba shi sa'arki, sai ayi tuwona maina tankaden bakin gado?”

Murmushi ne kadai abun da zan iya yi na kwanci kaina a wannan lokacin kuma shi na yi, sai dai ko kadan manufar da take son isarwa a gareni ba mai yiyuwa ba, sai idan cilasta Baba zata yi yayi min auren dole. Baba be shigo gidan ba, sai da yamma liss ya dawo a gajiya. Na debi ruwan wanka na kai masa yayi wanka ya fito ya zauna kusa da yar'uwansa yana cin abinci suna gaisawa.

Ina alwalar magariba na ji tana yi nasa maganar Zafeer.

“Ai wannan duk da ne, yanzu kam komai ya wuce, ko lokacin da na yi mata wannan furucin ta fusata ni ne shiyasa kuma na lura a wacan lokacin tana son ta biyewa zugarsa ne ta bijirewa umarnina, amman yanzu komai ya wuce”

“Duk da haka dai ka ce ka yafe ka san bakin iyaye lalle ne”

“Haka ne, toh na yafe Yaya Larai kina shagwaba Noor”

Ta yi murmushi ni ma murmushin na yi ina jindadin janye takukun da Baba yayi tsakanina da Zafeer. Daki na shiga na yi sallah bayan na gama na fito na yi ma Anty Larai godiya a lokacin Baba yana masallaci. Shigowar Ridwan da mintuna kadan Baba ya dawo daga masallaci suka gaisa Ridwan yayi masa alheri sannan ya fita waje jiranta. Ni kuma na yi mata bankwana Baba ya rakata har waje suna tafe suna hira har suka fice daga gidan.

Hana na shigowa na labarta mata cewar Baba ya daga min kafa a yanzu, yace ya yafe min na yi magana da Zafeer, na yi zaton zata taya ni farinciki ne kawai sai na ji ta fashe da kuka marar sauti. Hankali ya tashi da sauri na dafata na dago kanta.

“Hana lafiya?”

“Na gaji da rayuwar gidan nan Noor tun da Mama ta tafi ba mu da jindadi babu walwala, zuwan Umma ya kara mana matsuwa kuma ban mu isa mu yi magana ba, ni ban taba talla ba, sai wannan karon idan na fita da la'asar ba zan dawo ba sai bayan Isha'i dole sai na siyar da komai idan ba haka ba idan na dawo sai ta fara fada tace keta nake son mata. Baba kuma ba zai shigar mana ba sai ita, kawayena a yanzu babu mai talla sai ni, maganar nan har ya kai makarantar mu na boko, gashi yanzu mun fara jawaba, muna karewa zata oya kirkiro wani abun da zai hana ni zaman gida da safe, yanzu kina gani yadda karatun addini na bar shi saboda tallar nan, gaba daya rayuwar gidan nan ta isheni Noor ji nake kamar na gudu”

Tausayinta da kuma na kaina ya kamani, idan har ita zata fadi haka to ni nace me, kashi uku na ukuncin rayuwarta data gidan Hana bata shiga daya ba, domin ita har yanzu bata kula kowa ba balle a rabata da wanda take so kamar yadda Baba yayi min. Bata yi aure ba balle ta hadu da kishiya irin Aisha wani abun na rayuwar har yanzu bata san ya zafinsa yake ba.

“Ya muka iya? Tun Mama tana gidan nan muna cikin takurawar Baba balle kuma yanzu da bata nan, ni ina ganin idan kin kare karatunki kawai ki koma gurin Mama ki zauna, za ki jidadi kuma mijinta da take aure a yanzu yana son mutane ba kamar Baba ba”

Ta kalleni hawaye na mata zuba.

“Amman kina ganin Baba zai yarda? Ba zai yarda?”

“Me zai hana idan ma be yarda ba ki yi ma Anty Larai magana zata saka baki, kin san kuma Baba yana jin maganarta”

Ta fara share hawayenta.

“Allah yasa”

Ta mike tsaye ta cire hijabinta ni kuma na tashi na fita waje gurin aikin gyaran wake da nake kullum da dare. Tiya uku na zuba a tray na shimfida matacciyar tabarmarmu na zauna kamin na saka hannuna a waken wani yaron unguwarmu ya shigo wai ana sallama da Noor.

“Je ka ce waye?”

Umma ta ba shi umarni yaron ya juya ya fita.

“Gashi Malam baya nan balle na ce a nemi izini gurinsa, yaran yanzu kuma ba natsuwa ce da su ba, musamman zaurawa”

Tana maganar tana kallo, wata kila so take na yi mata ba daidai ba ta fada min ba dadi ko kuma ta hada ni da Baba, idan ba haka me miye na cin fuskar, ita ba zarwacin ta yi ba kamin ta auri Baba, su zaurawan dabam suke da sauran mata.?

“Sallamu Alaikum, ya ce wai wanda ya saba zuwa”

Ina jin amsar yaron zuciyata ta raya min Kareem ne, wata kila ita ma ta fahimci hakan shiyasa ta ce na tashi na tafi bayan ta gindaya min sharadin kar na jima saboda gyaran wankenta. To me ya zo yi kuma wannan karon? Biyo yayi ya duba ni ko kuma dai wata matsalar ce ta taso daga bangaren iyayen Hafiz da na tattara lamarinsu a gefe na aje.

Bakuwa mota ce da ban taba gani ba mai bakin gilashi baka ganin wanda ke ciki duk da kasancewar akwai hasken lantarki a lokacin. Tsaye na yi ina jiran Kareem ya bude motar ya fito, sai akasinsa ya fito, mutumen nan da na taba haduwa da shi a mall kuma shi ne dai wanda ya dauko ni daga gidan Mama ya kawo ni gida.

“Hajiya Nooriya kin yi mamakin ganina ko?”

Toh ko dai yayi arba da mamakin a fuskata ne shiyasa ya ke tambaya.

“Eh gaskiya na yi mamaki, ban yi tsammanin kai zan gani ba”

Na fada ina rumgume hannayena.

“Akwai wanda kike tsamanin zuwansa kenan, kar fa bazawarin ya tarar da mu ya dauka soyayya muke yi, yayi fushi”

Na yi murmushi feeling Speechless daman mi zan ce bayan shi ya zo shi ya kamata yayi magana ai.

“Well kawai hanya ce ta biyo da ni, sai na tuna i have a friend here na ce bari na biyo just to say, hope ban yi laifi ba?”

“Are we friends daman?”

Tambaya nake a bakin gaskiya ta domin ban san wata rana da muka zama kawaye ko abokai ni da shi ba. Da alama kuma tambayar tawa ta ba shi dariya har sai da ya bayyana hakoransa.

“Uhm ba ma bukatar request ai, idan ba mu zama abokai ba mun zama yan'uwa saboda Mama ko?”

“Maybe”

Na fada ina dan wara ido.

“Not maybe, pretty gal ban da jan aji, ko da yake kamata yayi na gabatar da kai ne, taya za ayi abota ba a san juna ba”

Ya miko min hannunsa.

“I'm Abdull by name, engineer ne ina zama a Lagos for now, ko da yake ni dan garin Kano ne haifaffen garin kano aiki ne ya kai ni Lagos kuma idan na tafi na kan yi wata biyar hudu uku har fi a can, am ina da mata da yara uku a yanzu”
Chapter 37 · 0% Book details