← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 82

Sashe 6

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“In Shaa Allah, ina ta kokarin danne zuciyata Barrister, ni kadai nake iya jin halin da zuciyata take ciki, amman da sannu komai zai wuce”

“Da yardar Allah komai zai zama tarihi”

Cewar Barrister yana duba wayarsa dake ringing wannan karon Aisha ce take kiran. Ya amsa ya kara a kunne

“Hello Madam...”

“Ba Aisha bace Noor ce, Hafiz ina son na tafi gida”

“Gida gurin me?”

“Ni dai kawai ina son na tafi ina marmarin gidan ne”

“Toh yaushe aka yi auren da za ace kin fara fita Noor?”

His last sentence make Kareem ya kalleshi da sauri.

“Ni dai ina son na tafi, ai ana tafiya ganin gida ko?”

“Eh amman ba yanzu, kuma idan kina son magana da ni irin wannan ki jira mana na dawo sai mu yi magana, amman ba wai ki ari waya ki kira kai tsaye kamar ke kika aje ba ni na aje ba ki fada min zaki tafi gida”

Ya yanke kiran rai a bace sannan ya mike tsaye, ba tare da yace da Kareem komai ba ya fice, Kareem din ma binsa yayi da kallo har ya fice.

NOOR POV.

“Ya kashe wayar”

Na fada ina mika mata wayarsa sai na ji babu dadi kamar ya wulakanta ni a gaban matarsa, domin ita shekaranjiya a gaban idona ta kira shi tace masa tana son ta tafi gida kuma ya bar ta amman ni ya hana ni har da kashe min waya.

“Wata kila be son ki tafi yanzu ne, kin san baki wani jima da zuwa gidan ba, girma ma yau kika fara, ki hakura sai nan gaba”

Na daga mata kai cikin rashin jindadi.

“Ai indai Barrister ne haka yake wani lokaci, shi fa abu kadan ya fusata shi, yanzu zai iya zuwa ya rufe ki da fada ma ko kuma ni da na ara miki wayar, kuma baya son yana fada ka yi shiru sai dai ka yi ta amsa shi in ba haka ba, abu kadan ne zai kai miki hannu”

Na kalleta da sauri.

“Duka kenan?”

“Hmmm, bana son fadar wani abun kar ki yi zaton ina tsorata ki ne, amman fa yana da kirki yana aje komai a wadace gwargwadon hali”

Na yi shiru ina jin kara tsanarsa a raina daman ba son shi nake ba, balle kuma yanzu da nake ta kara jin halayyarsa.

“Me kike girka yau?”

“Taliya”

Na fada domin ita na fi kwarewa a girkin, ita ma kuma idan ta yi yawa tsabe min take. Ta wara ido.

“Eyyy bari na je na dandana na ji”

Kamin na ce komai ta mike tsaye ta nufi kitchen nawa da bayan gama girki ban gyara ba na zo na yi wanka na zauna a falon ina hutawa. Bata jimaba ta fito tana fadin.

“Amman Noor kamar kin cika gishiri ko?”

“Aa daidai na saka sai dai ko idan bakinki ne”

“To kam bakina ne, kin san mai ciki komai nata dabam yake, kuma na manta ban fada miki ba mijinki yana son miyar yauki sosai kamar kuka ko kubewa ko karkashi komai dai mai yauki yana son shi sosai”

“Okay”

Ta fada gabana na faduwa domin ni ba iyar miyar kuka na yi ba, ita ma ta take na yayan talaka balle kuma wani miyar karkashi ko kubewa.

“Bari na tafi bangarena na barki ki huta”

Da ido na bita har ta fice sannan na juyo ina kallon tv dake kunne. Gaba daya baya jin sakewa a gidan, ko dan ban saba da Hafiz din ba ne kuma matarsa Aisha ko kuma dai dan bana son auren ne oho, ni nake kamar a gidan yari nake rayuwa ba gidan aure ba. Bata wani jima da fita ba na ji tsayawar motarsa wannan karon be shiga bangarenta ba kamar yadda ya saba sai ya shigo bangarena kai tsaye. Juyawa na yi ina kallon kofar Falon da ya turo ya shigo, zan iya fadar cewar be shigo da far'a domin na ga alamar hakan a fuskarsa kuma gashi be yi sallama ba kamar yadda ya saba yi. Sai kawai ya tsaya yana kallona ni ma kallonsa nake ido cikin ido gabana na faduwa domin matarsa ta fada min zai iya rufe ni da fada ko duka.

“Wai ke wace irin yarinya ce Noor? Idan na shigo baki san ki ce min sannu da zuwa ba, idan zan fita babu Allah ya tsare ko a dawo lafiya, idan safiya ta waye baki san ki gaishe ni ba, ba dama kuma dare yayi na kai hannu na taba ki ki fara min ihu kamar kanki aka fara hada shimfida, yanzu kuma ki kira ni kai tsaye ki fada min wai kina son ki tafi gida, haka kika ga ana yi a gidanku? Ki gaba daya baki da tunani baki da hankali ba a koya miki zaman aure ba?”

Kamar an hura min wuta haka na ji ruwan zafin zuciyata na tafasa. Na mike tsaye cikin fushi na ce.

“Ka san yadda nake ai kamin ka auro ni, taya zaka ce ba ni da hankali bani da tunani kuma haka na ga ana zaman aure, kana nufin ba ni da tarbiya kenan? Kuma Aisha a gaba shekaranjiya ta buga maka waya ta tambaya ta tafi unguwa kace mata eh, sai ni da ka raina zaka rufe da fada”

“Ke daya kike da Aisha? Shekararta nawa a gidan nan haihuwarta nawa? Ke kuma yaushe kika zo? Noor ko kiran sunana da kika kai tsaye ba tarbiya ba ce, Aisha ma da kanta ta fada min bata jindadin yadda kike fadar sunanta, ko ba komai ta girme ki ya kamata ki ce mata Yaya ko maman wane”

“Ba ni da tarbiya Hafiz, ai kasan wacece ni ka san gidanmu miyasa ka yarda ka auro ni? Ko an maka dole ne? Ka raba ni da wanda yake so na ka kawo ni cikin gidanka kuma kana son ka kuntata min, zafin rabuwa da masoyina zan ji ko bakinciki zama da kai”

Tsayawa yayi kallona irin kallon nan na mamaki.

“Baki da tarbiya Noor, ba a fada miki muhimmancin aure da zama da miji ba, shiyasa kike kallona kai tsaye ki fada min maganar da duk ta zo bakinki, to ni ba irin Kareem ba ne, iskancin da matarsa take masa kwatarsa ba zan dauka ba, ba zan taimake ki na tsamoki daga wannan gidan da unguwar ta ku ba ki zo nan ki hana ni kwanciyar hankali, shiyasa ana kusan auren nan sai da na ce a fasa kika ce a a mahaifinki zai iya fushi da ke, saboda Mahaifinki.... ”

Sai kuma yayi shiru, idona cike da kwalla na ce.

“Ka karasa mana ka ce mahaifina mai kwadayi ne, saboda ya siyar da mutuncinsa ya siyar da nawa, kana da hujja na siye shi da kudi, amman ni har abada ba zaka taba iya siye ba Hafiz ba zan taba sonka ba”

Na wuce shi na shige dakina ina kuka, na bakinciki da Baba ya janyo min daman na san Hafiz ba zai taba ganin kimata ba, duk mace da ta samu uba irin nawa bata dace ba. Na bata minti talati akan gadona ina kuka sannan ya shigo dakin rike da plate din taliyar da na dafa yana nuna min.

“Wane irin abinci ne haka? Gishiri yayi yawa kamar zaki yanka halshen mutane? Kuma kin bar kitchen kacha kacha ke baki san ki gyara guri ba? Idan baki canja rayuwa ba Noor Wallahi zaman gidan nan sai ya miki wahala, tashi ki tafi ki girka min wani abincin”

Na tashi zaune ina kuka.

“Ni ban iya kalar girkin da kake so”

Kamar abun arziki sai na ga ya aje plate din hannunsa ya zauna kusa da ni yana sauke ajiyar zuciya ya fara rarrashina.

“Shikenan ya isa, yi hakuri na taba amarya hmmm a yafe min kin ji yar Amaryata”

Ya kwantar da ni jikinsa sannan ya ce min na tashi mu yi wanka, na san manufar hakan domin ya gwada min ba sau daya ba. Na yi saurin naje jikina daga na shi na tashi daga jikinsa na matsa. Sai ya tashi ya dauki plate din ya fice daga dakin. Ya dade kamin ya sake shigowa ina kallon yadda ya sakawa kofar dakin key hankalina ya tashi na mike tsaye kan gadon ina kallonsa...

#KhadeejaCandyPAID PAGE 4️⃣

©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....

You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153

_______•••_______

Zaunawa yayi bakin gadon yana kallona.

“Noor dan Allah ki kwantar da hankalinki, abun nan be kai yadda kike tunani ba, kuma ke ba fa jaririya ba ce da za ace idan zan matsa kusa da ki ri rika ihu kina daga hankalinki kamar yar shekara shida, haba Noor tun yaushe muke abu daya gashi har yau nake shirin barin dakinki? Hmmm i promise you i won't hurt you”

Ya miko hannunsa gaba daya sai na ji hankalina ya kara tashi, ko da ace ina son shi yadda Aisha ta fada min halinshi yake da yadda zafin abun yake dole na tsorata balle kuma bana son shi.

“Zo mana Noor...”
Chapter 6 · 0% Book details