← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 82

Sashe 10

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ina kudin yake Noor? Kin san yanzu abun duniya ba zama yake ba, ban da rayuwa ba ni da komai a yanzu, sai kuma wanda ya ga Allah ya ga Annabi ya kyautata mana, kina kallon yadda gida ya zama kamar kango, abun bakin cikin ma sai da na sake masa sabon fenti”

Ya fada kamar zai fasa kuka, na daga kai ina kallon bakin wutar da ya rufe ginin ya hana a gani fentin.

“Ai na so Hafiz din ya shigo ya ga yadda gidan ya koma”

Na kalli Baba bance komai ba. Kamin ya shiga tambayata ya kishiyata ya zaman gidan Baba wata matsala, na amsa masa da komai lafiya. Ina nan wasu makotan suka shigo jaje suna ta maraba da ganina har suna fadin wai na fara natsuwa saboda na kasa hada ido da su.

“Aure na natsar da mutun, wai Noor ce a haka, Allah ya bada zaman lafiya”

A fuskar Baba nake ganin yadda kalamansu suka masa dadi, bayan sun fita shi ma ya fita a nan na samu damar hira da Hana tana fada min yadda wutar ta fara.

“Daga dakin Mama ta fito, kuma bachin ya mana nauyi duk ba mu san ta kama ba sai da hayaki ta cika gidan, Yaya yana dakinsa na zaure Baba kuma a waje ya kwana ni kadai ce a daki”

“Ya aka yi ta kai ga jikinki?”

“A lokacin da na farka na ga wutar tana ci sosai har kusan kofa ba damar na wuce ta saman kuma ta sauka kan katifa sai ta kama tufafinmu ceiling saman kuma yana ta narkewa yana fado min a jiki kin san na roba ne idan ya digo kamar fatar zata cire nake ji, sai da Alhaji Bashiru ya shigo ya fitar da ni”

“Ni ma ban sani ba sai jiya da dare Hafiz yake fada min, amman Hana baki ma Yaya magana ba ya kai asibiti?”

“Ba shi da kudi ai kin ga da ya kai ni, Baba kuma ba zai iya kashe kudinsa ba ji yake hasara yayi, ban dan ma gobarar nan ba jibi za a kawo amaryarsa shiyasa kika ji yana fadar yayi fenti”

Na gyara zama ina mamaki.

“Auren dai yana nan da gaske?”

“Noor to me zai hana? Mama ma aure zata yi?”

“Ita ma? Yaushe? A ina?”

“Garin nan, wani mai rufin asiri ma kuwa motarsa ma abar kallo ce”

Dadi na saka ni murmushi.

“A ina Mama ta hadu da shi?”

“A cikin unguwa ya zo gidan wani abikinsa”

“Amman shi ne ba a fada min ba? Bani da labarin kowa babu mai zuwa gurina kun bar ni can ni kadai”

“Noor ba a kusa kike ba balle nace zan taka da kafa na tafi, ba ni da kudin abun hawa kuma mijinki ma zai gaji idan aka ce kullum zai na je”

“Ba zai gaji ba ita ma kanwarta tana yawan zuwa ai, ko jiya ma taje kuma baya cewa komai”

“Sai na samu lafiya zan zo”

Da kanwata da kusan zan iya cewa tawainiyata ma muka sha hira muka koshi, ina ta sake saken yadda zan saci kafa na tafi na ga Mama babu hali, domin na san Baba zai yi fada idan ya dawo be tarar da ni ba, dole a wayar Yaya na gaisa da ita har nake tambayarta ance zata yi aure.

“Da yardar Allah kuwa Noor, idan lokaci yayi ai dole za a fada muku”

“Mama yaushe zaki zo?”

“Yaushe aka yi auren ma balle na kwashi kafafuwa na tafi Noor? Ni fa uwace ba zai yiyu na tafi gidanki ba sai da dalili”

“Amman Mama kin ji Baba yayi wuta?”

“Uhmmm Allah ya kyauta gaba, Noor ki rike aurenki da mutuncinki, idon mutane yana kanki kowa jiran yake wani abu ya faru da ke, kuma kin ga zaman gidanku nan ba shi da dadi, da alama kuma mijinki mai hankali ne da tunani, kishiyarki kuma ki rike ta da mutuncin kuma ki yi taka tsantsan da ita, ki rika kula da rayuwa na san halinki da sakarci, balle kuma an dauke ki an kai ki gurin babbar mace ina yarinya karama, ta fiki wayo ta fiki hankali kuma ta fiki sanin kan mijinku, ki bi a hankali kuma ki rike addu'a kar na ji kar na gaji wani abu ya faru, kuman ko da wasa bana son na ji kin bibiye Zafeer aure ya rabaki da kowa yanzu”

“Toh Mama, zan kiyaye, Zafeer ni ba zan taba yin magana da shi ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi masa magana”

“Toh sai ki kiyaye, ki zauna lafiya a gidanki kin ji?”

“Toh Mama”

Sallama muka yi sannan ta kashe wayar na mikawa Yaya.

“Mahaifiyar Kareem ta rasu ko Yaya?”

“Eh kwana uku aka yi ai ba a bude restaurant din ba, sai da aka yi sadakan uku duk mun je masa gaisuwa”

“Yayi kuka?”

“A gabanmu zai yi kuka? Sai dai a boye ko? Kin masa gaisuwa”

“Hafiz be bari na tafi ba matarsa kawai ta tafi, wata kila sai nan gaba idan na fara fita”

“Kila”

Saman sama muke taba hirar Yaya na fada min Kareem din ya rame sosai abun ya taba shi. Na yi zaton Hafiz zai dawo da rana ya dauke ni saboda yayi min zancen girki amnan shiru be zo ba sai bayan Isha'i a lokacin Baba har ya gaji da jiransa. Yana yin sallama Baba ya tarbeshi jiki na rawa suka gaisa sannan ya shiga nuna masa gidan yana fada masa yadda gobarar ta fara.

“In shaa Allah zan kira ka Baba sai mu yi magana na ga abun da ya dace ayi”

“Na gode Allah ya saka da alheri ya kara rufa asiri...”

Baki har kunne baba yake Fadar haka, sai dai ko kadan ban ga alamar sake fuska a gurin Hafiz ba, yadda yake rawar jiki da Baba ma wannan karon ban ga yayi haka ba. Ba Baba kadai ba ni kadai na yi tsammanin zai bawa Baba kudi ko kuma ya ce akai Hana asibiti amman ba ko daya har muka fito gidan. Na shiga motarsa shi ma ya zagaya ya shiga sai da yayi min wani kallo da ban fahimci ma'anarsa ba sannan ya tashi motar muka fara tafiya.
Ban kalleshi ba, sai dai na ji a jikina yana yawan kallon gefe da nake zaune.

“Noor na ga kin bata rai, ko kin yi marmarin gida ne?”

Na yi shiru bance komai ba, hannu na ga ya mika bayan motar ya dauko kwali ya dora min a cinya.

“Ya kamata ke ma ace kina da waya ko?”

Na kalli kwalin wayar na kalleshi ina zaro ido.

“Tawa ce?”

Ya daga min kai, sai na rasa ina zan saka kaina tsabar farinciki domin taba rike wayar kaina ba. Yana faka mota harabar gidan na fita da sauri na shiga bangaren Aisha ina nuna mata wayar, sai ta fini farinciki da jindadi ma ita ta taimaka min na saka sim din ta nuna min yadda ake operating wayarsa.

#KhadeejaCandyPAID PAGE 6️⃣

©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....

You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153

_______•••_______

“Allah ya tsare ya sa albarka”

Ta yi min addu'a sai na amsa da amin sannan na karbi wayar bayan ya saka min number shi da number Baba da kuma na Aisha.

“Amman fa karki je ki kira Saurayinki da wayar nan na sa halinki”

Ta fada tana min wani kallo kamar na zolaya, ni kuwa na kalli Mijina na kalleta da mamaki.

“Ya za'ayi na kira sho kuma? Na fa yi aure yanzu na sani”

Ta sake fuskar zolaya tana min wani kallo na rashin yarda.

“Ke dai kin san yadda muke sirrinmu ko? Kawai dai ki kiyaye, ke matar aure ce a yanzu kin ji kanwata”

Na amsa mata da tohm domin kawai na takaita zancen sannan na mike tsaye rike da wayar da kuma jata na fice daga bangaren. Ina shiga bangarena na tare a kujera ina ta kallon wayar bude nan taba nan hotunan da na yi kuma sun fi a shirin a zama daya. Ima tsaya da daukar wani hoton sai hango Hafiz na yi ta cikin hoton ya leko kansa. Na juya na kalleshi ina dariya shi ma dariyar yayi ya matso kusa da ni ya zauna.

“Daukin wayar ne har yanzu”

“Eh na gode Hafiz”

“Ki daina cewa Hafiz Noor”

“Tohm Yallabai”

A bakin gaskiya ta na fada sai dai na lura kuma hakan dariya ya saka shi domin dariyar yake kamar na fadi wani joke.

“Ur Welcome..”

Ya kama hannuna na rike ya juyo da kafadata daya na fuskance shi da kyau.

“Noor, please karki ba ni kunya i trust you, kar na ji ko na ga abun da zai bata min rai wayar nan, ba ma waya kadai ba a komai ma, kin ga Aisha ta fada min abubuwa da kika fara fada mata akan zamantakewar duka duka kuma yaushe muka fara zaman auren? Sirrin dake tsakanina da ke na mu ne mu kadai kawaye iyeye ko abokiyar zama babu wanda zai sani, wanda ke tsakanina da ita kuma ita ma zata rike babu wanda zai sani, kin ga da farko na ji haushi amman daga baya na yi tunani hankalinki da tunaninki ba irin nata ba shi, saboda shekarun ba daya ba, amman ina son na ja kunnenki karki fadawa kowa sirrinmu kin ji? Kuma zancen baki so na kika aure ni na san wannan ita ma ta san wannan ba sai kin yi ta nanata mata ba kina fada mata yadda na raba ki da saurayinki, yan'uwana ba su san irin auren da muka yi ba, so bana bukatar su san cewar wai baki so na kika aureni kinji”

Na daga mishi kai.

“Me tace na ce”
Chapter 10 · 0% Book details