← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 82

Sashe 4

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zan kwanta a karshen gado kai ka kwanta a farko?”

Sai na ga kamar ransa be yi dadi ba, sai dai hakan be hana shi amincewa ba kuma be hana shi karfafa min guiwa da murmushi ba. Yadda na fada haka aka aiwatar ni na kwanta a karshen gadon shi kuma a farko da na ji ya motsa sai na tashi zaune, gashi na hana a kashe wutar dakin. Shi kuma ya tsare ni da ido sai kallona yake ya ki ya juya ya ki yayi bachi, ni kuma da zarar na fara bachin sai na kokarin kwatar kaina kar yayi min nauyi mu hade a guri daya. Dariya na ji yayi yana shafa kansa

“Kina wahalar da kanki Noor, shureshure be hana mutuwa, kuma ni idan na ce zan yi ko ba zan yi ba, ta zauna domin magana daya nake yi, so ki matso nan ki kwanta kina bukatar hug ki yi bachi mai dadi”

Na yi kamar ban ji ba, na ki na motsa ma balle har ya ga dama ta, a haka dai har bachi barawo ya sace ni, wannan karon ban sake farkawa ba sai da ni da shi muka ji karar bugun kofar falo da karfi.

“Subhanallahi Lafiya?”

Ya fada yana tashi zaune, ni ma na tashi zaune cike da tsoro jikina har rawa yake domin na ji bugun kofar ne a cikin bachi hakan kuma ya tsorata ni sosai.

“Bari na duba”

Na sauko da kafafuwansa a kasa ya nufi kofar dakin ya bude ya fice, tsoro be bar ni na tsaya jiran tsammani ba na bi bayansa na tsaya daga jikin kujerar falon dake nesa da kofar falon. Wata matashiyar yarinya ce da ba zata wuce shekaruna ba ta shigo falon da sauri tana kuka.

“Wallahi Yaya ba zan iya da Anty Aisha ba, ihu take tana makure kanta ta ki ta yi bachi, haka ta shiga dakin su Ikram tana ta dukansu cikin daren kuma ba su mata komai ba, sai zaro ido take”

hafiz ya juyo ya kalleni sai ya miko min hannunsa.

“Zo mu je?”

Na lake kafada a bata fuska alamar ba zan je ba, ahh daman idan ba cuta ba ta ina zai ce na zo muje kuma ya ji kanwarta na fadar tana makure kanta har ta doki yaranta.

“Okay Na'ima shiga ku kwanta tare, bari na je na dubata”

Yarinyar da ya kira da Na'ima ta nufo ni shi kuma ya fadada kofar ya fice.

“Sannu an tashe ku kuna bachi ko?”

“Ba komai ai, zo mu kwanta a nan shi sai ya kwana tare da ita a can”

“Tohm”

Ta shigo har cikin dakina. Ni da ita muka kwanta a kan gadon, a nan kam na samu natsuwa ni da ita muka yi bachinmu cikin aminci da kwanciyar da hankali.

KAREEM POV.

Sai da ya runtse ido ya girgiza kai sannan ya dan samu saukin jirin da yake gani, sai ciwon kai kam kamar an kara masa wani haka yake ji, ba wani uban nauyin da zuciyarsa ta yi. Cike da karfin hali ya taka ya karasa gurin da Yusura take zaune ya cire drip din dake lake ya saka mata wani sannan ya koma ya zauna ya dafe kansa. Can kuma ya dago kai ya kalli matarsa da har yanzu bata san inda hankalinta yake ba tun bayan da uwar da take kallo a matsayin tata ta kwanta dama, wata kila kaddarar ta mata nauyin dauka ne shiyasa kwakwalwarta ta rikice, domin mutuwa gaskiya ce mai tsananin daci, kuma nauyi ne da idan ya hau kai ba a iya saukewa. Ta rasa mutane masu muhimmanci a rayuwarta tun kamin girmanta ta saba da rashi, sai dai mutuwar Momy ya zo mana a wani ma'auni mai tsanananin nauyi da ya wuce sikelin awa, a yanzu jin take bata da kowa kuma bata da gata domin ta rasa macen da ita ce komai nata kuma ita ce gatanta.

Kallonta yake irin kallon da be taba samun damar yi mata ba, tun bayan da ya aureta, ashe ta zama babbar mace wasu abubuwa sun sauya daga hallitarta, sai dai kyaun da Allah yayi mata yana nan har yanzu ko da yake kyauta baya gabanshi sai dai ba zai iya karya ba matarsa tana da kyau. Dauke kansa yayi idonsa na tara kwalla tunawa da ranar da Momy ta fada masa ra'ayinta na son ya auri yar'uwarsa. Wannan karon ba bakinciki auren yake ba bakincikin rasa first love dinsa yake, be saka mata ran mutuwa nan kusa ba, yanzu da waye zai zauna yayi hira irin wadda ya saba yi da ita, wa zai tsokana wasa da wa zai yi shawara...? Shi kam dai be san zafin rashin rai ba, sai a wannan karon ganin yake kamar wata karya ce dake kokarin zame masa gaskiya tsakanin jiya zuwa yau saboda rashin saka mahaifiyarsa a ido da be yi ba. Wai Momynsa ta tafi kenan tafiyar da babu dawowa?

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Ya furta a hankali yana saka hannunsa ya dafe kansa. Hajiya Hassana ce ta shigo dakin dauke kofin fura.

“Kareem karbi ka sha, tun jiya na lura baka ci komai ba, tun shekaranjiya ba idonka har ya fada”

Ba dabi'arsa ba ce yi ma na gaba da shi musu dan haka na karba ya sha rabi kofin ya aje yana amsa mata.

“Eh ni ma na yi wannan tunanin idan har bata samu sauki ba yau dole na kaita asibiti”

“Dole kam, Allah dai ya sauwake mutuwa ai ba ku kadai kuka ji ba, ni ma na rasa abokiyar zama mai kirki mai hali na gari”

Hajiya Hassana na fadar haka ta fashe da kuka, daman tun rasuwar Momy take ta kuka har ta bawa mutane tausayi. Kareem ya mike tsaye ya fice daga dakin, harabar gidan ya fita gurin da maza suke zama ya zauna kusa da Hafiz yana amsa gaisuwar da ake masa. Kadan daga cikin dabi'u na mutuwa shi ne bata manta gidan kowa, kuma idan ta ziyarta, sai ta bar tabon da ba zai goge ba kuma ba za'a manta da ita ba, mussaman washe garin sadakar uku a ranar kuka yake sosai, daga ranar kewa zata fara domin mutanen dake bada hakuri idan ana kuka sun watse mutum kadai za a bari da kuncinsa a zuciya.

Ranar da Momy ta cika kwana hudu da rasuwa, Yusura ta samu karfi jiki a yayinda Kareem kuma ya rasa nasa saboda garkuwar jikinsa dake yin kasa tana son kwantar da shi. Har suka dawo gida wasu ba su daina kira suna masa gaisuwa ba, wasu kuma da kansu suke zuwa su yi masa gaisuwar da ba su samu zuwa yi ba a lokacin da ake zaman makokin. Yau ma kamar shekaranjiya da jiya yana sauke wayar a kunnensa ya mike tsaye ya nufi hanyar kitchen coffee ya hada ma kansa ya fito nufi sama, yana hawa ya shiga dakinsa kansa na tsananin ciwo, zaunawa yayi bakin gadon ya sha coffee kadan ya aje ragowar ya kwanta ko zai samu ciwon kan yayi masa sauki. Few minutes bachi mai nauyi yayi gaba da shi, bachi irin mai tsanannin nauyin nan da ka dade baka samu yi ba, domin har Yusura ta turo kofar dakin ta shigo be ji ba tana fadin.

“Makota mu sun shigo, mijinsu yana son yi maka gaisuwa”

Jin shiru ya saka ta shiga cikin dakin abun da bata saba ba idan yana cikin, kamar mai shirin yin sata haka ta karasa gurin gadonsa ta so take ta gani bachi yake ko kuma dai ya shareta ne ya ki ya amsa mata. Sai ta same shi a takure ya rumgume hannayensa a kirji kamar wani karamin yaro marar gata sai numfashi yake da karfi. Dillll sakon kar ta kwana ya shigo wayarsa karkata kanta ta yi ta kalli gurin da wayarsa take aje kusa da kofin Coffee. Ta saman screen din wayar ta fara hango sunan Safeena hakan kuma yana nufin sakon ya fito ne daga gurinta... Sosai ta kura ido tana son me sakon ya kunsa sai dao babu dama domin rubutun be fito sama ba sai suna kawai... Dauke kai ta yi ta juya ta fice daga dakin a hankali.

Daman har yanzu Kareem yana da number wayar Safeena a wayarsa? Ta tambayi kanta sai dai abun da ta manta zuciyarta bata da amsar tambayarta.....

#KhadeejaCandyPAID PAGE 3️⃣

©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....

You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153

_______•••_______

“Wallahi Bachi yake kusan tun da aka yi rasuwar nan baya samun bachi, yanzu yanzu ya shiga amman har bachin ya dauke shi”

Ta fada bayan ta zauna, cike da tausayawa Neighbor din ta ce.

“Ayyah ai kara da kika bar shi ya samu bachinsa kam, an kwana biyu ba a runtsa ba saboda damuwa, idan dai ya tashi ki fada masa mun zo yana bachi muna masa gaisuwa”

“Okay an gode ki fadawa Baban Ammar din Bachi yake”

“Zan fada masa, Allah ya jikanta da rahama kun yi rashi babba”

“Sosai haka Allah ya so, sai hakuri”
Chapter 4 · 0% Book details