← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 82

Sashe 44

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani sabon shafin wahalar rayuwa Umma ta bude mana a idan, ni da Hana saboda sana'ar da take wai ai ba ita zata fita ta yi ba a dole hana zata soya mana wara a waje ni kuma na yi aikin cikin gida. Ta inda nake samun sauki shi ne takaba da nake bana fita, saboda haka duk wani aiki na fita ita zata fita ta yi, da safe kuma Yaya sai ya cika gidan da ruwa sannan yake fita.

Ta inda gurin da ta samu banbancin da Mama a zamanta gidan ita kam Baba yana bata abinci da cefane mai kyau, ba kamar Mama ba da wani lokacin zai ce be da shi ko kuma ya bada abinci ya hana cefane ko ma ya hana gaba daya. Wata kila saboda ita din tana da dan da sauran kurciya ba kamar Mama ba, wata kila kuma dokin amarci ne yake Allah masani.

Idan kuma aka yi girki ba a ba mu wani abun arziki Allah ma ya sa yanzu damuwa bata barina na ci na koshi kamar da, wani lokacin har ragewa nake na bawa Hana a da kam na fi kowa cin abinci a gidan, ranar da Hana ta tafi family house din Mama ta fada musu halin da ake ciki na dora mata talla, washe gari Kawu Garba ya samu Baba yana nuna masa hakan be dace ba, sai Baba yace kar wanda ya sake saka masa baki akan lamarin yaransa shi ya ga damar su yi, kuma babu mai ciyar masa da yara sai su.

A nan yake fadar ai tun kamin auren ya fada mata yaransa za su rika mata wani abun saboda ta fada masa ita fa tana sana'a kuma aure ba zai hana ta yi ba, shi kuma ba zai iya ganin matarsa da aure ta fita waje ta yi sana'ar wara ba, domin haka yarsa zata maye masa gurbi. Ni kam gaba daya na zama kamar ba ni ba duk abun da ake bana iya cewa komai sai ido, wani kalar canji ne ya same ni irin wanda ban yi zato ba.

KAREEM POV.

Da kansa ya shiryawa yaransa abun karyawa ya dauko lunch box dinsu ya raka su har gurin School bus suka shiga sannan ya juyo ya dawo, dakinsa ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito ya shiga motarsa. Family house dinsu ya wuce domin fara gaisawa da iyayensa kamin ya wuce aiki kasancewar yau Monday.

Wani abun da ya sabawa kansa da shi ne, na kin kallon mahaifiyarsa a duk lokacin da ya shiga gidan. Kai tsaye ya wuce bangaren Hajiya Hassana wadda take step mom dinsa. Karyawa ya same ta tana yi tare da Khadija da Aaryam da sauran yaransa Aneesa da Kamla. Kanensa duk suka gaishe shi ya amsa, Yusura dake zaune gefe daya ta mike tsaye ta shige dakin Hajiya Hassana sai a lokacin ma Kareem ya lura da ita. Khadija ta kwashi kayan abincin ta bi bayan Yusura Kamla da Anessa ma haka, sai ya rage daga Step Mom dinsa sai kanensa Aaryam.

“Zaka ci abincin a zuba maka?”

Hajiya ta tambaya.

“Aa”

“Baka cin abinci yanzu, tun da Momynka bata nan, shigowa nan ma sai monday Monday kake yi ka duba mu, idan Momynka bata nan ni da mahaifinka ai muna nan kuma Kanenka suna nan be kamata kana haka ba”

A hankali ya sauke ajiyar zuciya.

“Hajiya Bana jindadin shigowa ne yana yawan tuna min da Momy kuma ina jin babu dadi”

“Tohm ya za'ayi haka tsarin Allah yake, kai kanka mutuwa zaka yi balle kuma wasu, sai hakuri rayuwa ta gaji haka, ni kaina yanzu gidan ba dadi yake min ba Wallahi, amman a haka nake daurewa saboda Khadija da Aaryam da kuma Aneesah, dole na yi walwala idan ba haka ba dukanmu sai mu taru mu takura mu yi ta bakinciki da kuka”

Yayi shiru be ce komai ba. Hajiya ta dauki tissue ta goge hannunta.

“Likita..”

Ta kira shi sai ya kalleta daman haka take kiransa tun Momy na gidan.

“Ni fa ba zan boye maka ba, ban gane manufar abun da ka yi ba, kuma ban gane inda kuka dosa ba”

“Na miye ba Hajiya?”

“Kai da Yusura mana, ta dawo gida kawai tace mana ka sake ta, saki daya biyu ko uku ba mu sani ba, Daddy ka ma fushi yake da kai shiyasa be maka maganar ba har yau, Khadija da Aaryam ma gashi a zaune kullum haushinka suke ji saboda haka”

Kareem ya juya ya kalli Aaryam kyakkyawan saurayi mai jini a jika, sai yayi murmushi.

“Saboda Yusura?”

“Eh mana, Daddynka cewa yayi ba zai maka magana ba, kuma kar wanda yayi maka a saka maka ido kawai, ita kuma ta so barin gidan ni na hana, saboda na san idan Momynku tana raye Yusura bata da gurin zama sai gidan nan, a nan ta girma nan ta saba yanzu kuma dan Momy bata nan babu wanda zan bari ya dauketa ko kuma ita ta tafi ta bar mu, sai idan na mutu, kai ma dan kana ganin Momy bata nan ya saka kake son ka wulakanta amanar da ta baka, to ka sani Yusura ta fika gata a gidan nan, kuma matukar ina raye ni ce gatanta ba kuma zata wulakanta ba”

Kareem yayi gutun murmushi ya girgiza kai, kana ya sake juyawa ya kalli Saurayin Kanensa ya ce.

“Fushi kuke ta yi da ni akan abun da Baku san komai a kai ba”

Aaryam ya ce.

“Haba Big Bro ko dai minene ai be kamata ace ta kai ga haka ba, kai fa Namiji ne, kuma ga yara tsakaninku, kawai dai ban maka magana ba ne saboda Daddy yace kowa ya saka maka ido, kuma ina kasa da kai be kamata na tsuma baki a irin wannan ba sai idan ka bukata”

“Gaskiya ne”

Kareem ya fada tare da aje numfashi sannan ya mike tsaye ya nufi bangaren mahaifinsu, sai a yanzu ya fahimci dalilin da ya saka har yau da suke wata biyu da sati biyu da rabuwa Daddy be taba kiransa ya tambaye shi miye ya faru ba, kuma be taba yi masa maganar ba a duk shigowar da yake gaishe shi a gidan.
A natse ya shiga bangaren kamar yadda ya saba sai bayan da ya zauna sannan ya gaishe da Daddy dake sanye da gilashi yana duba newspaper.

“Lafiya Kalau, Kareem ya gidan ya yaran?”

“Lafiya kalau Daddy”

“Maa Shaa Allah, yau Monday ko akwai aiki”

“Haka ne Daddy”

“Allah ya taimaka ya bada nasara”

“Ameen”

Kareem ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Daddy. Daddyn ma ya kalleshi

“Allah yasa lafiya, akwai wata matsala ne?”

Kareem ya hade wani abun da ya tsaya masa a makoshi sannan ya ce.

“Daddy, ban ji kace komai akan dawowa Yusura gidan nan ba”

Daddy ya aje newspaper dake hannunsa.

“Oh wai Yusura, Mijinta ne ya sake ta kasan kuma bata da wani gidan da ya wuce nan, bata da gata a duniyar nan sai mu, zamanta a nan ya takura maka ne? So kake a koreta?”

Kareem yayi murmushi jin yadda Daddy yake fadar mijinta ne ya saketa kamar be san Kareem din ne mijinta ba.

“Aa Daddy ai ban isa na ce a koreta ba”

“Good kara dai da kasan haka”

Ya sake yin murmushi, a yanzu ne ya kara tabbatar Daddy fushi yake da shi.

“Kawai dai na yi zaton ko zaka bincike abun da ya faru ne”

“Abun da ya faru, tsohuwar budurwarka tana zuwan nemanka, amaryar abokinka tana zuwan nemanka ta yi magana sai ka mareta ka ce ka saketa”

Dif Kareem ya dauke wuta kamin ya kalli Daddy ya ce.

“Haka ta fada maka?”

“Ba gaskiya ba ne Daddy, Safeena ta zo gaisuwar Momy ne, kuma na gargade kar ta sake zuwa domin babu wata alaka tsakanina da ita, Noor kuma tana zuwa ne saboda tsabanin da suke samu da Hafiz a lokacin”

“Zan yarda da wannan, domin ban san ka da wani aiki na assha ba, shi ma wannan saboda Hassana ta matsa ne ya saka ta fadi wannan dalilin, amman bayan haka bata fada mana komai ba, ni kuma na auna abun a ma'aunin kishi ne, sai dai kai kuma ka yi kuskure na aikata saki a take”

Kareem yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Daddy ya cigaba.

“Shiyasa na yi shiru na zuba maka ido na gani shin kana da hankali kansan ya kamata ko baka sani baKareem ya sauke numfashi mai nauyi.

“Daddy, akwai abubuwan da ni da ita muka boye ba mu bar kowa ya sani ba, ban san ya zaka fahimta ba gaskiya ce mai matukar nauyi da daure kai, Daddy ni da Yusura ba mu taba son junanmu ba, ban taba jin ina sonta ba ita ma bata taba jin tana so na, wannan sakin ma ta dade tana bukatar na yi mata shi, saboda da nisanta da ni”

Daddy yayi murmushi mai sauki ya cire gilashin idonsa.

“Kareem karka maida karamin yaro mana, baka sonta bata sonka aka yi muku aure kuka zauna lafiya har kuka haihu ba a taba jin kanku ba sai yanzu da Mahaifiyarka bata raye zaka ce wai baka sonta? Wannan ba hujja ba ce”

Cikin tsananin damuwa Kareem ya ce.

“Wallahi Daddy bana son Yusura ita ma bata so na, kawai dai mun amsawa Momy ne kuma mun zauna saboda ita, ni da ita ba za mu iya bijirewa umarninta ba”
Chapter 44 · 0% Book details