← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 82

Sashe 15

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sauke wayar kamin Samira da ta kasance cousin dinta ta turo mata mumber Aisha har ta matsu. Sakon mumber na shigowa ta bude da sauri ta taba Number ta kira sai daf da zata yanke Aisha ta daga.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikusalam Aisha ya gida?”

“Lafiya kalau ya yaran?”

“Alhamdullahi kin gane mai magana?”

“Na so dai na gane, amman ban gane ba”

Yusura ta yi murmushin karfin hali.

“Yusura ce Maman Tine”

“Kawai ki ce min Mrs Kareem zan fi ganewa, uwargida ran gida”

“Oh oh toh ke ma ai uwargidance, ko da yake yanzu nake jin cewar Hafiz ya kara aure”

“Wallahi haka ne, kika ji ko dai Kareem ya fada miki, ai ke ma auna arziki kika yi da yanzu ke za a kawowa ita”

“Ban gane ba”

Yusura ta fada daman abun da take nema kenan. Aisha ta sauke numfashi.

“Hmmm ai mijinki ya so aurenta shi yayi sonta sosai, sai dai ban san miya hana shi aurenta ba, kwatsam Hafiz ya zo min da zancen auren, wai zai rufa mata asiri ya aureta saboda wanda zata aura an fasa auren sanadin Kareem shi kuma Kareem din yace ba zai aure ta ba, kin san mazajen na mu da hadin kai ko ma dai miye Allah kadai ya sani”

“Amman kika yarda Aisha?”

“au hanawa zan yi? Kin ji Yusura da wata magana, namiji da zai yi aure zaka iya hana shi ne? Ai idan namiji zai kara aure baya ji baya gani, shiyasa na nuna masa na fi shi tausayinta, na san waye Hafiz na gama karantar mijina daman kuma idan ka fahimci waye mijinki zaman aure ba zai yi ma mace wahala ba, shiyasa na goya masa baya dari bisa dubu aka yi komai aka gama cikin mutunci lefen ma ni na hadawa kaina na hada mata, yadda na san Hafiz ina daga hankalin na daga na shi zuciya zata iya dibarsa ya sallame ni gidanmu, amman hakan da na yi sai na siye zuciyarsa da ta yan'uwansa gashi muna zaune lafiya ni gani nake kamar ma ya fi so na yanzu sama da lokacin da be auri yarinyar ba, domin na kara value a idonsa”

“Toh Allah yasa yar gidan mutunci aka dauko miki kin san yan matan yanzu”

“Waya sani ance dai ubanta dai shegen kwadayi ne da shi ko kashe rai zai iya yi akan kudi, ita kuma gaskiya ance bata tsayawa kanta ba, kawai dai maza ne mace daya bata isarsu sun maida karin aure rayuwa, kuma basa tsayawa su duba yar gidan mutunci daukowa kawai suke, saboda tana da kyau”

“Oh Allah ya kyauta, matan zamanin nan sai a hankali”

“Ameen kedai ina nan ina lallabawa karta kashe min aure, ga yara ga ciki na tafi ina? Samun miji irin Hafiz a wannan mazanin ai sai an tona is rare gaskiya”

“Allah ya tsare miki aurenki, ni ai be fada min ba sai yanzu, na ce dole na kira na miki jaje”

“Hmmm na gode, zan yi saving number ki ai a rika gaisawa”

“Toh sai anjima”

Yusura ta kashe wayar gabanta na bugawa da karfi. What her husband got into? Ko shiyasa ta zo nemansa har cikin gidan kamar yadda Safeena ta zo? Me yake kokarin zama ne? Matan aure yake nema? Ta mike tsaye ta fara tafiya tana daga kanta. Amman ita miye nata a ciki idan ma neman matan yake yi? Kabarinsa dabam nata dabam, kuma bata fatan zama da shi har abada.

“Saboda yaranki...”

Wata zuciyar ta fada mata. domin saboda su ta dawo tana kokarin kyautata masa tun daga lokacin da Safeena ta leko gidan. Ji take indai tana raye ba zata iya bari Kareem ya auri Safeena ba ko da kuwa bata da aure domin Momy bata son Safeena ko kadan, mutuwarta kuma zai iya saka Safeena ta yi tunanin sake kulla alaka da Kareem. Gashi yanzu babu Momy babu mai masa fada idan yayi ba daidai ba.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Gaba daya ta rasa me ke mata dadi, ta rasa ina zata kama abun ya daure mata kai, wai saboda be sonta yake bin mata ko kuma dai wani sabon hali ne ya kirkirarwa kansa? Tunaninta ya kasa tsayawa guri daya.

KAREEM POV.

@4:11pm suka fito daga massalacin dake cikin restaurant din, Kareem na gyara hannun rigarsa ya ce.

“Ni dai da zaka dauki shawarata Barrister karka karbi case din nan, case ne mai matukar hadari kasan yadda yan siyasa suke”

“Amman za a samu kudi mai kyau fa Doctor”

“Rayuwa ta fi kudi muhimmanci, duk kudin da zaka samu idan ba zaka samu rayuwa ba ba su da amfani”

“Kusan kowane aiki akwai risk ciki, kawai dai ka taya ni da addu'a”

“Allah ya tsare, amman ni ban yarda ka karba ba gaskiya”

Hafiz ya tura kofar office din ya fara shiga yana fadin.

“Su suka neme ni fa, kuma saboda cancanta suka neme ni, ba zan oya watsa musu kasa a ido ba, abu na biyu ba a nan za'ayi ba a Kaduna ne”

Kareem ya daga kafadunsa.

“Indai ka nace sai ka yi ai babu mai hanaka, haka shi ne kawai matsalata da kai”

Yayi murmushi yana gyara zamansa a kujerar da ya zauna. Kareem yayi shiru na yan mintuna sannan ya kalli Hafiz cikin karfin hali ya ce.

“Hafiz ya iyalinka?”

Wani kallo Hafiz yayi masa a cikin kallon da yake masa idan yana tuhumarsa da wani abun.

“Lafiya?”

“Ka tabbata?”

Hafiz ya gyara zamansa.

“Akwai abun da kake son mu tattauna?”

Kareem yayi murmushi domin shi da abokinsa kowa ya san halin kowa, da zarar dayan ya fuskaci wani canja ko da na magana ne zai fahimci akwai manufar aikata hakan.

“Amm... Ban san ya zaka dauki abun ba, na so na bar maganar sai kuma nake ganin kamar zaka kone kanka ka cutar da iyalinka, be kamata na shiga cikin maganar ba amman dole ce ta saka”

Hafiz ya mika masa duka hankalinsa yana kallonsa.

“Lokuta da yawa idan ka ga In aikata wani abu da be dace ba kana yawan jan hankali kuma ka lurar da ni gurin da illar abun take”

“Ka wuce duk wannan Kareem fada min kawai”

Kareem ya zauna da kyau.

“Hafiz akwai wata matsala tsakaninka da Noor ne?”

Hafiz ya kalli wani gafen alamar tunani sannan ya kalli Kareem.

“Ta zo nan ne?”

A madadin Kareem ya amsa masa sai ya dora da abun da yake jin kamar shi ne matsalar.

“Hafiz ka rika bincike kamin ka yi fushi ko yanke hukunci”

“Kareem ta fada maka abun da ta yi?”

“I don't think Noor zata yi abun da kake tunani, she's very innocent, Hafiz bata ma san amfanin abun da ka gani a jakarta ba bata san me ake yi da shi ba, kuma abun mamaki ne ace ta san wannan a yanda take da kananan shekaru, she's too young for that ita ba karuwa ba ba matar da ta shekara hudu gidan miji ba”

Hafiz ya nade hannayensa.

“Idan bata sani ba taya suka zo a jakarta? Kasan dai ba za su kawo kansu ba ko? Idan ba ta siya ba maybe wani ya bata wani like Zafeer amman ta ki yarda ta fada wanda ya bata, ko kuma ya fada mata ta siya, ranar da na kaita gidansu ta wuni a ranar da ta dawo ne na karbi wayar da na bata kawai wata zuciyar ta raya min na bude jakarta and i did na ga abun a ciki”

“Taya zata amsa laifin da ba nata ba, bata san ya aka yi ya zo jakanta ba”

“Kai kuma ka yarda da ita?”

Kareem ya kasa cewa komai wannan babin saboda baya son ya janyo mata laifi gurin Hafiz.

“Ya kamata dai ka yi bincike, ta rantse bayan aurenta bata hadu da Zafeer ba ko ta yi magana da shi”

Hafiz ya kwanta jikin kujerar.

“Wa kake zargi? Aisha saboda ta fada maka Aisha, shiyasa na kirata ai lokacin da ta zarge ta kuma ta rantse a gaban Noor ba ta saka ba, sai me?”

“Maybe the way you confront her zai iya sakawa ta rantse ko da akan karya ne saboda ta wanke kanta”

“Me yasa ka yarda zata aikata amman baka yarda Noor zata aikata ba?”

“Saboda Noor bata waye duniya, da zaka ce min ta shiga gidan mutane ta yi arba da nama ta sata ko ta dauki wani abun dadi ta boye a jakarta zan fi yarda, amman ko kudi bana saka ran Noor zata dauka a dan fahimtar da na yi mata na kankanen lokaci Noor ba zata san miye abun da ke jakarta ba, kuma mace makira ce Hafiz na ga hakan a zaman da na yi da Safeena da Yusura, baka iya ganewa kansu, yanzu idan ka ga yadda Yusura take min a gaban mutane ba zaka tana tunanin akwai wani abu na rashin so ko zaman lafiya a tsakaninmu ba, yanzu kuma har wani hali ta kirkira saboda Safeena ta zo gidan har dakina take kawo min abinci idan zan fita tace Allah ya tsare idan na dawo tace min sannu da zuwa, na fara tsorata da lamarin matar nan”

Hafiz yayi murmushi.

“Safeena ta zo gidan fa ka ce Kareem? Amman ban taba ganin mutumen da ya raina matarsa ba irinka”

“Ba zuwa na yi da ita ba, kuma na gayyato ta na yi ba saboda na daina daukar wayarta ne ya saka ta zo da sunan ta zo min gaisuwa, amman dai na taka mata burki. So ni ina ganin ya kamata ka yi bincike ko kuma ka yafe mata ka rufe maganar kawai ba wai ka dauke mata kafa ba, kuma ka daina magana da ita a halin da take karkashin kulawarka. Ka ga duk yadda nake da Yusura bata so na bana sonta ba ma zaman dadi amman a haka idan na ga ta wuni bata fito shiryawa yara abu ba, ko kuma ban ji motsinta ba na kan leka na duba lafiyarta domin hakkinta ne da ya rataya a wuyana, please ka gyara”
Chapter 15 · 0% Book details