← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 82

Sashe 62

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da cikina ya shiga wata bakwai na samu sauki abubuwa da yawa na daina amai da kwadayin sosai, ko zabar abinci. Har ta kai ni nake shirya abun karyawa da safe da kaina. Domin yanzu Hana ce mai tsananin bachin safe idan ta gama sallah ta koma ta kwana sai kace ba yar makaranta ba. Kullum sai ta buga latti saboda bachi, har tausayi take ba ni domin na san wahala ce ta yi mata yawa, na aikin gida da take ga kuma karatu da basa daga kafa.

Abun sai ya zame mana kamar duty ni ce mai saurin bachin dare ita kuma ta yi rankon na safe. Domin da zarar na gama sallah Isha'i Abdull ya kawo lemun juice da yake hada min a kullum, domin likita yace na rika cin yayan itatuwa sosai a yanzu fiye da kayan zafi ko kwadayi irin su madara da danginsu. Saboda kina yana ta girma ne a yanzu, ban yi kasa a guiwa ba na rumgumi kayan marmari, kullum sai na ci da dare kuma sai Abdull ya hada min lemun juice da juicer da ya siya gurin Khadeeja Candy Store, zallar ruwan fruit take matsewa sai dan sukari kadan da yake kasa min ko kuma abar da bana so wato zuma, wani lokacin saboda bakin nawa ya saba da zaki idan babu ba zan sha ba. Da zarar ya hada min na sha sai bachi yayi gaba da ni, ko motsi ba zan yi ba sai safe.

Ina tsaka da shafa face cream ya shigo dakin ya aje min cup din natural orange juice. Sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko kayan bachinsa ya saka.

“Kina bukatar wani abu?”

Na kalleshi kamar na ce ina da bukatar ka, yau wata shida kenan ban hada shimfida da mijina ba, tun cikina na wata daya da yan kwanaki ya nade sha'awata ya jefar saboda kawai na ki yarda a zubar da cikin. Sai kuma wata zuciyar tace na daure mana na zuba masa ido tun da haka ya zaba.

“Aa”

“Okay to zaki yi kallo?”

“Aa bachi zan yi”

“Yanzu ai kin lalace da bachin dare, da dare yayi sai bachi kamin tara na dare ta yi har kin kai Morocco, Allah yasa ba raguwa ko rago zaki haifa ba, wannan lalaci yayi yawa”

Na yi dariya mai sauti ina masa gwalo.

“Bachin yana min dadi, da na kwanta bana sanin me duniya take ciki sai na farka”

“Asha bachi lafiya Mom Unborn”

Ya fice ya bar ni na cigaba da shafa face cream din, sai da na gama sannan na dauki lemun juice din na sha kadan sai na ji zakin zumar yayi min yawa gashi ba son zuma nake sosai ba, haka na saka dole na tashi na shiga bathroom na kunna tap na tara lemun na kara ruwa kadan, na kashe juyowar da zan yi santsin tile ya kwashe ni, aiko ba shiri na saki kofin na rike tab din sai kofin ya fadi kasa lemun ya zube.

“Allah ya tsare na auna arziki yau kai...”

Na fada ina hakki, da na fadi gurin ba karamin ciwo zan ji ba, waya sani ma ko na karye tun da jikin babu karfi. Ruwa na saka na wanke lemun da ya zube na dauke kofin da ya tsaga na fito na aje shi a inda na saba ajewa na hau gadon na yi addu'a na kwanta, nan da nan kuwa bachi yace wa yake jira ba ni ba, kamar na mutu haka na fara bachin ban san shigowar Abdull dakin ba, kashe wuta da yayi ma duk ban sani ba. Daman bana sanin komai sai safe.

Ina tunanin shan lemun yana taimaka min sosai gurin samun bachi mai dadi kuma mai nauyi da tsayi, domin yau da ban shanye shi gaba daya ba na farka sai dai ban kai ga motsawa ba na ji saukar Abdull daga kan gadon ya nufi bathroom, yana shiga na ji kararar ruwa be jima ba ya fito ina kallonsa ya rufe kofar a hankali ba tare da ya kashe ruwan ba. Mamaki ya cika kwakwalwata ashe har yanzu be daina wannan abun ba, domin tun a wacan lokacin zuciyata take raya min yana biyawa kansa bukata ne a bandakin.

Ina ganin ya dauki wayarsa sai na rufe idona, na yi zaton bandakin zai koma sai gashi ya kunna fitilar wayar ya haska fuskata. Ni kuma na yi kamar bachin nake da gaske har sai da ya kauce sannan na bude ido. Ga mamaki na sai na ga ya nufi kofar fita ya bude a hankali ya fice. Zumut na tashi zaune kamar ledar da iska ya dauka. Na zauna gurin da tsawon minti biyar ban ji ya dawo ba, sai na sauko daga kan gadon na bude bandakin na kunna guluf na duba sannan na kashe na janyo kofar na rufe a yadda take.

Takawa na yi na fita dakin, a tunanin yana falo ne, sai dai kuma ban same shi a falon ba, domin wutar falon ma a kashe take ban ga hasken wayarsa ba kuma ban ga alamar mutum ba ta dan hasken waje da yake shigowa. Na nufi ma kunnun wutar kamar zan kunna sai kuma na fasa na nufi kitchen na leka nan ma baya nan. Na juyowa na nufo dakina da mamaki domin ko kadan zuciyata ba ta raya min abun da kunnuwa za su ji ba. Daf da zan shiga dakina ne na ji karar rufe kofar dakin Hana wata kila kuma na bandakinta ne yayi kara har na ji saboda dare ne, hakan ya saka hankalina ya karkata can, to daman idan baya falo baya kitchen baya dakina ina zai je? Waje? A tsakar daren nan ba zai fita waje ba sai idan da wani babban dalili.

Na taka cikin faduwar gaba na doshi kofar dakin, na kai hannu zan murda da nufin na bude na shiga sai kuma dauke hannuna na matsa kusa na dora kunne na a kofar dakin. Shiruuuu ban ji wani motsi ba, na sauke ajiyar zuciya ina jin kamar hankali ya kwanta, ashe dan'uwansa ne ke tafe da gumurzunsa irin tafiyar da ban yi tsammani ba.

“Sai yaushe za a zubar to?”

Na ji muryarta, hakan ya sakan ni kwantar da kunne a jikin kofar sosai na natsu numfashi ma daker nake fitarwa saboda na ji me take fada.

“Kina da matsala ne ke Wallahi, na fada miki ni ai na san lokacin da ya kamata a zubar ko?”

“Tsoro nake kar ya girma, kuma ina tsoron na sha wahala”

Ta fada cikin muryar kuka.

“Ai na sani idan ban ja lokaci haka ba, ba zan samu hadin kanki ba, yanzu ana zubarwa kuma ba zaki sake yarda da ni ba”

Rarararararsssssssaaaa. Gabana ya bugawar da mai sauraren tsawa dake tafe da ruwa.

“Zan yarda, ni dai dan Allah a zubar”

“Kin yi alkawari?”

“Eh, dan Allah a zubar”

“Ki kwantar da hankalinki mana, na san abun da zan yi, kin san ina sonki sosai ai, ina son ki Hana, amman ki yi ta wahalar da ni, Wallahi da ace ke na fara gani ba zan auri yayarki ba...”

Ban sake jin komai ba sai shesshekar kukanta kadan kadan. Tashin hankali ne be bari na sake jin komai ba ko kuma dai ba su sake cewa ba din. Na dauke kunne na shafa wuyana ina lalaben sarkar da babu ita a wuyana. Jikina ya fara rawa hawaye suka yi ambaliya a idona. Na shiga na same su a ciki na nuna musu na sa komai, ko dai wai ban ji daidai ba, ko dai gizo kunnuwa suke min. Na bar kofar na fara takawa na nufi dakina na shiga na hau gadona na kwanta na rufe ido na tsawon min biyu sannan na bude.

Wai ko zan ji cewar mafarki, amman ban ga alamar haka ba. Na mari kaina sai na ji zafin na tsara kunci na, tabbas gaske ne ba mafarki nake ba. Amman taya? Kanwata ce fa uwa daya uba daya, kanwata da mijina? Kanwata ta jini mai bina, kanwata da muka kwanta a mahaifa daya ciki daya uwa daya ta kawo mu duniya? Kuma mijina mijin da nake aure auren sunna! Mijin da nake dauke da cikin dansa ko diyarsa. Tun yaushe haka take faruwa?

Na mike tsaye na nufi madubi na sai kuma na zauna a kasa. Me na yi da na cancanci haka? Why me? Why? Kanwata? Jinina?

“Wayyo Allah na”

Na dafa zuciyata sai wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya ya zo min. Wannan abun yayi min muni ina ji a wasu gurare amman ban dauka abun zai zo kusa ni ba. Na tashi daker na koma saman gadon na kwanta jikina na rawa na takure guri daya na rumgume fillo, a wannan daren bachi be samu damar ziyarta idona ba, kunci be bar ni, kamin safe zazzabi ya rufe ni, filon da na rumgume kuma ya jike da hawaye na. Abdull be dawo dakin ba sai asuba, ina jin shigowarsa da lokacin da ya kwanta saman gadon ya lulluba...

Littafin nan ba kyauta ba ne. Biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0

Washe Gari na tashi da wuri saboda zan tafi asibiti, dan haka na gyara da wuri na fito falo, ina jin motsin Hana na nufi kitchen din na dan rikawa mata aiki.
Ina tsaka da kashe socket ta yi min wata magana da ta saka na kalleta.

“Noor ina son na tafi gida”

“Me yasa Baba ya sake magana ne?”

“Aa kawai dai ina son gida yanzu, na fi jindadin zama gida sama da nan”

Na juyo da kyau na fuskance.

“Hana wani abu na yi miki ba daidai ba ko Abdull yayi miki?”

“Aa ba ko daya, kawai dai na fi sha'awar tafiya gida ne”

Na dan jimm ina mamakin dalilinta na fadar haka a yanzu, daman na lura yanayinta gaba daya ya canja.

“Hana mafarki kika yi marar kyau ko me?”

“Ba komai ni dai kawai ina son na tafi gida”

“To kije ki dawo ko kuma ki koma gidan gaba daya?”

“Gaba daya dai nake son na koma”
Chapter 62 · 0% Book details