← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 82

Sashe 74

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya ya koma ya rufe gate din. Ni kuma na kai hannuna na dafa ginin ina jin zuciyata kamar zata fashe. Tun a lagos na kudurtawa zuciyata zuwa na fada masa damuwa ba, da na yi nufin na fara sauka hotel ne washe gari na je na same shi a restaurant ko asibitinsa na fada masa, amman burin ceton yar'uwata ya saka na ji kamar idan ta kai gobe zan iya rasa rayuwarta. Na kwashe minti talatin tsaye a gurin sannan ya sake bude gate din.

“Yace a shigo da bakon”

Na cira kafa na shiga cikin gidan na fara takawa sai na hango shi tsaye a entrance yana kallona har na karaso. Ya kalli daga kasa har zuwa sama.

“Noor”

Na kalleshi ba tare da na amsa ba.

“Minene kuma wannan karon?”

“Kareem na san ina damunka ina shiga rayuwarka da yawa, amman dan Allah karka ce min aa na maka alkawari daga wannan ba za sake ba, dan Allah ka taimaka min dan girman Allah”

Na kai kasa ina rokonsa sai kallona yake ya kasa cewa komai. Na nufo shi ne saboda ina jin yana karfi na dukiya wata kila har da hanyar da zai taimaka min.

“Shigo ciki”

Ya juya.

“Matarka za....”

“Bata nan”

Na mike tsaye na bi bayansa na shiga cikin falon sai na zauna a kujera shi ma ya zauna nesa da ni yana kallona.

“Me ya faru?”

Na bude jakata na dauko takardar sakin zan tashi na kai masa sai ya taso ya karba ya zauna a dayar kujerar dake kusa da tawa. Yana gama karanta takardar ya kalleni

“Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Saki Noor mi ya faru?”

Na ciro dayar takardar da Hana ta aje min na mika masa ina hawaye. Ya karba ya fara karantawa mikewa yayi tsaye ya girgiza kai ya runtse ido, can kuma ya bude idon ya kalleni.

“Da gaske?”

Na daga mishi kai har sau uku, ya koma ya zauna na dafe kansa.

“Ko da yaushe idan ina cikin damuwa, na kan zo gareka saboda ina samun mafita kuma kana taimaka min, dan Allah ka taimaka min ta dawo, bana son Mama ta sani ko Baba domin idan Baba ya ji zai Fadawa Umma ita kuma zata yada a cikin unguwa, Mama kuma idan ta ji wata kila ba zata iya hakuri zata janyo mutuwar aurenta, bana son daya daga ciki ya faru?”

“Na ji zan taimaka miki amman dole ne iyayenki su sani Noor, me zaki fada musu a mutuwar aurenki? Kuma yanzu kamin a gano yar'uwarki me zaki fada? And idan ma an ganta amman ba a cikin hali mai kyau ba dole za su ji ba zaki iya boye wannan ba, yanzu idan kin tafi gida me zaki fada?”

“Ba gida zan tafi ba Hotel zan zauna, har sai an gane Hana sai mu tafi gida tare, na Fadawa Baba kawai mun yi fada ne ya sake ni”

“Noor yanzu kurciyata tana damunki, matsala irin wannan iyaye kadai suke iya tsayawa mutum, dole ne ki fada musu gaskiya, gidan ba zaki iya Fadawa Baba ba, to ki fadawa Mahaifiyarki, kaddara ce babu wanda ya wuce kaddara”

“Kaddarar ita ce kullum a biye da ni, aure na biyu kenan ina yi babu dadi, gashi yanzu har na janyo Hana ta gudu ta shiga duniya”

Na fada ina kuka. Mikewa yayi tsaye ya haura sama ya bar ni a falon ina ta kuka ni kadai gaba daya ma duniyar ta isheni. Be dade ba ya sauko da waya a kunnensa.

“Yeah let me ask her”

Ya kalleni.

“Ina kika saka ran zata tafi?”

“Ni da ita ba mu san kowa a Lagos ba, ban san inda zata tafi ba, bata da kawaye sai yan karantarsu ban san gurin waye zata tafi ba”

“Wai bata san kowa a lagos ba”

Can kuma na ji ya amsa da

“Okay Thank you”

Ya zauna sannan ya amsa kiran da ya shigo.

“Aaryam na kira baka daga ba”

Ya kalli agogo.

“Okay, daman wani taimako nake so dan Allah, wata yarinya ce ta gudu a Lagos nale son a nemo ta, na san kana da friends yan Lagos sosai maybe you can help”

Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya turo kofar, bana jin komai da yake fada har sai da ya gama wayar ya dawo ya zauna.

“Ina wayarki dole sai an tura hotonta”

“Na siyar na siyar da ita yanzu, suka ba ni 305”

“Wayar?”

“Eh”

“Saboda me?”

“Ba ni da kudi ne, kudin sun kare a hawan mota, shi ne na siyar da wayar saboda na yi amfani da kudin, irin wayarka ne”

Ya kalli wayar ya kalleni.

“15 pro max suka baki 305k?”

“Aa taka ta tsufe tawa da shekara daya, tawa 14pro max ce”

Na ciro kudin na zube duka a gurin.

“Wane barayo ya siye wayar?”

“Ba barawo ba ne shago ne”

“Saboda kawai sun ga baki san kan waya ba sai su siye a 305k? Dole sai an nemo hotonta da Yanzu ina layinki yake? Dole sai an nemo hotonta da sunan makaranta su”

Na yi shiru ina tunanin gurin da zamu hotonta domin ban zan tafi gida babu ita ba.

“A dp dinta na whatsapp akwai hotonta kuma sunan makarantar su Victory College Of Health”

“Yanzu ina line ki?”

Na saka hannu jaka na dauko layi na mika masa, sai ya karba ya haura sama sai gashi ya sauko rike da wata wayar touching amman ba iPhone ba. Ya saka line da na bashi ya dade yana taba wayar ban sa me yake dubawa ba kamin ya miko min wayar.

“Saka number ta”

Na karba sakon karta kwane ya rubuta a messager wayar.

“Dan Allah Hana ki dawo, tafiyarki ta haifar min da matsaloli da yawa, na bar Lagos na dawo Kano, amman na kasa tafiya gidanmu saboda ban san me zan fada musu ba, bana son na fadawa kowa matsalarki, na miki alkawari babu wanda zai ji, dan Allah ki dawo na yafe miki kuma na fahimce a yanzu, Abdull ya sake ni, Hana kuma kin sani ina da ciki zan iya rayuwa zan iya mutuwa, idan baki dawo gida ba, ni ma zan koma ba, zan tafi na bar garin Kano ne, domin rashin izurin da na yi miki ya hana ni sukuni, ina kaunarki yar'uwata dan Allaj ki dawo, na miki alkawarin babu wanda zai ji”

Na saka number ya na dago na mika masa wayar ina kallonsa. Kwarjinsa da kirmarsa sun cika min ido, Kareem mutum har da rabin mutum, shi din mai tsayawa ne akan damuwata mai kokarin ganin bayan abun da ya hana ni farinciki.

“Na gode...”

Na furta ina hawaye.

“kwashe kudin ki tafi gida”

“Toh”

Na kwashe kudin na saka a jaka sai ya miko min wayar.

“Indai yar'uwarki tana sonki da gaske zata dawo ko ta kira ki tsakanin yau zuwa gobe, idan kuma bata kira ba, zamu yi amfani da line mu gano inda take, amman dai zata dawo na miki wannan alkawari ki kwantar da hankalinki”

Na daga mishi kai sannan ya karbi wayar na mike tsaye da cikina.

“Noor Zauna"

Na koma na zauna sai ya tashi ya nufi kitchen be dade ba ya fito rike sandwich da lemu ya janyo karamin lebur ya dora min a kai.

“Zaki iya cin wannan? Ko wani abun kike so a kawo miki? Jikina na rawa akwai yunwa a tare da ke”

Ban tsaya ba shi amsar zan iya ci ko aa ba na dauka na fara ci.

“Kar matarka ta dawo ta same mu a nan”

“Ba zata dawo ba. Yaushe rabonki da abinci?”

“Rabona da abinci tun jiya bana iya cin komai sai ruwa, gaba daya maza ba su da kirki, Zafeer be fahimce ni yanzu yana can yana cewa na ci amanarsa, na auri Hafiz ban jidadi ba, yanzu kuma wannan”

Ajiyar zuciya ya sauke ya bata rai sosai yana kallona.

“Wannan duk ya fi su zama dan iska, ni mana ban so aurenki da shi ba, kawai babu yadda zaka hana abun da Allah ya tsara faruwarsa ne, taya zai aikata duk wannan kuma ya sake ki? Ga cikin shi a jikinki”

“Ni na ce ya sake ni, ba zan iya zama da shi ba, ba zan iya zama da mazinaci ba”

Ina maganar ina kuka har na cinye duka sandwich din na shanye lemu na aje kofi, na mike tsaye Kareem be sake cewa komai ba. Ya dauki cups din ya kai kitchen ya kawo min tissue ma karba ina tsaka da goge hannuna ya jefa min tambaya.

“Noor ko da ya tuba?”

“Eh, ba zan taba iya zama da namiji mai neman mata ba”

“Kina da gaskiya, abu mai kyau na mai kyau ne, go ahead and live your life”

Na aje masa tissue a gurin na nufi kofar fita.

“Noor, kin san bana baki shawarar da zata cutar da ke ko?”

Na juyo na kalleshi.

“Daga gidan nan ki tafi gurin Mahaifiyarki kuma ki fada mata komai karki boye mata, ba zaki iya handle wannan ke kadai ba, you're too young for this”

Ban ji ina iya musa masa ba, saboda haka na amsa masa da kai sannan na juya na fice daga falon. Mai gadin ne ya bude min gate sai na nuna masa akwatina ya dauko ya ba ni na fara ja har na isa babbar titi na tari Napep na hau na fada masa umguwar da zai kai ni. A daidai gate din gidan Mama ya aje ni na ciro kudinsa na bashi ina jin marata na ciwo sosai.

Na fita ina jan akwatin na shiga cikin gidan, hankali be tashi ba sai da na shiga falonta, Mama tana cikin jindadi da kwanciyar hankali, rayuwar da bata samu ba a gidan mahaifinmu gashi a nan ta same ta, anya zan iya zuwa mata da wannan tsarabar? Kaddara ta shafi Hana, yanzu kuma ta shafi Mama...!! Na juya na fara tafiya bana son na zama silar mutuwar auren Mama, ta fada min jikinta be dauki mace a baki komai ba, face rigar da zai iya sakawa ko ya cire.

“Subhanallahi”

Na juyo jiki babu karfi na kalleta da kumburarrin idanuwana, wani tsadadden green lace ne a jikinta har kyalli yake.

“Noor...”
Chapter 74 · 0% Book details