← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 82

Sashe 11

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na tambaya ina mamaki, domin ban san na taba fada mata wani abu a game da Hafiz ba, yo ni da har yanzu ba mu taba hada shimfida ba ta ina zan fada sirrinsa? Kuma yaushe nake fada mata yadda ya raba ni da Zafeer.

“Cewa ta yi kin kura min ido kamar zaki cinye ni”

Ya ja hancina hana kallon cikin idona. Na sauke kai kasa.

“Baki jin yunwa ne? Ko kin ci abinci a gida?”

“Aa ban ci ba, kai baka ci ba?”

“Ban ci na so ki dawo ki girka, ni ma ban samu dawowa ba sai daren nan”

“Girki cikin dare akwai wahala kamin ka fada na yi bachi”

“Wa zai dafa?”

Na dan saci kallonsa na sauke ido, ba dai yana nufin ni na girka ba? Ganin na yi ya mike tsaye.

“Taso muje mu siyo wani abu a waje”

Na mike tsaye ina rike da wayata, a nan na bar jakar da na dawo da ita daga gida. Hannuna ya kama muka fita daga falon be sake ba har gurin motarsa ya bude min na shiga sannan ya zagaya ya shigo ya kunna motar sai kuma ya  kalleni.

“Bari na tambaya Madam ko za a siyo mata wani abu”

“Tohm”

Yana fita na fara daukar kaina hoto a motar, be jima ba ya dawo ya ja motar muka kama hanya. Na yi zaton zamu tafi Kareem Restaurant ne sai na ga ya faka a wani restaurant da ban sani ba, ko'ina na gurin wuta ce mai calar blue da ja daga waje. Ciki kuma farin haske ne irin wanda ko allurarka ta fadi zaka iya gani. Sai da ya fara fita sannan ni ma na fito muka jera a tare muka shiga.

“Me kike son ki ci?”

“Ice Cream”

“Ice Cream ai ba abinci ba ne”

“Ni idan na ci shi ya ishe ni, sai kuma nama”

Muna tafiya ina fada ina rabon ido, katon guri ne aka yi kowa bangare abu dabam ne, idan zaba sai ka tafi gurin biya ka biya sannan ka fice. Gurin masu pizza ya fara zuwa ya daukar mana daya, ya nufi shawarma ya dauki biyu, sannan muka nufi gurin masu kaza dake cikin gilashin tana juyawa kawar wata karuwa.

“Ba mu daya”

Ya fada sannan ya kalleni ya ciro wayarsa aljihu da hannu daya ya matsa can gefe yana amsawa. Mutumem ya gama yanka kazar ya saka a leda sai ya miko min, na waiga na kalli saitin da yake tsaye yana wayar da murmushi a fuskarsa da alama da Madam yake waya domin ita ce kadai zata iya saka shi irin wannan murmushi kuma ta dauke masa hankali. Ban bi ta kansa ba na nufi gurin masu ice cream ina duba wanda ya fi girma a jikin hoton dake gaban box din, domin sai ka zaba sannan za a dauko maka.

“Wane ya fi dadi?”

“Kowane ne yana da dadi yan mata, amman dai ki dauki vanilla ice cream mata sun fi son shi”

Na ji an fada daga gefena, na juyo na kalleshi sai ya sakar min murmushi.

“Can i pay”

Na girgiza masa kai alamar no, sai ya bata fuska kamar mai magana da yarinya.

“Why? Baki son na samu lada?”

“Kai Malam Lafiya”

Hafiz ya fada tun kamin ya karaso ni da shi muka juya kallon Hafiz din da ya daso gurin da saurinsa.

“Waye wannan? Yayanki ne?”

“Mijina ne”

Ya matsa nesa da ni ya kalli daga sama zuwa kasa.

“Duk kyaun nan naki, wannan ne mijinki”

Ban ce masa komai ba, shi ma kuma be sake cewa komai ba ya nufi gurin biya ya bar shi a gurin tsaye.

“Waye wannan?”

“Ban san shi ba, yau na fara ganinshi ni ma”

“Amman ai magana na ga kina yi da shi”

“Tambaya yayi zai iya biya na ce aa ni matar aure ce”

Hafiz ya kalli gurin da mutumen nan yake tsaye, shi ma kallonmu yake kamin ya karbi katinsa a fara saka masa kayan a babbar leda.

“Mu tafi...”

Na wuce gaba yana bayana muna isa gurin Mutumen ya karbi kayansa ya fara tafiya.

“Oga Abdull ga canjinka”

Daya daga cikin masu karbar kudi a gurin ya fada yana mika masa canjin 750.

“Keep the change”

Ya fada ba tare da ya juyo ba. Hafiz ya ciri Atm dinsa ya biya kudin aka fara saka mana a babbar leda, a nan na samu damar satar kallon mijin na wa, ni ban taba lura da yanayinsa kyau ko muni ba dress ko yanayinsa, gaba daya babu ko daya a gabana sai yau da mutumen nan yake mamakin ni din matarsa ce. Kuma gaskiya ya fada Hafiz ba shi da wani kyau na azo a gani, ba laifi dress dinsa na zamani riga da wando, kuma yana ta kamshi ba laifi ba zaka kira shi baki ba haka kuma ba fari bane.

“Muje”

Ya rika duka ledodin gaba ya saka ni sai da na fara fita sannan ya fito. Kamin mu isa motar na hango yarinyar nan da Zafeer yake yi ma gyaran mota tana doso gurin, ita ma kallona take kamar yadda nake kallonsa da alama ita ma dai ta gane ni kamar yadda na wayance ta.

“Noor ko?”

Ta fada yana nuna ni a lokacin da ta karaso kusa da ni. Na daga mata kai ina murmushi Hafiz ya kalleta.

“Wacece wannan?”

“Waye wannan Yayanki ne?”

Ita da shi kusan a lokaci daya suka yi tambayar kowanensu yana kokarin sanin abun da ke tsakanina da daya.

“Mijina ne”

Na fara amsa mata jiki a sanyeye ina jin babu dadi domin ta san alakata da Zafeer. A take na ga yanayinta ya sauya kamar mai mamaki kamar kuma bata jidadin amsar tawa ba.

“Zafeer...”

Sai kuma ta yi shiru...

“Allah be yi da shi ba, Noor shiga mota mu tafi”

Hafiz ya fada rai a bace yana ba ni umarni. Na nufi motar ina jin wani abu marar dadi ya tokare min zuciya. Kamin na isa gurin motar hawaye ya cika idona har ya fara zubo domin ta tuna da abun da nake kokarin mantawa da shi a kankanen lokaci, mutumen da ba ya kunyar nuna soyayyata a gaban kowa. Tsaye ta yi tana kallonmu har sai da muka bace mata. Kaina a kasa yake har muka isa gida na ki yarda na dago dan kar Hafiz ya ga hawayen dake min zuba, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuncin dake zuciyata ba, domin yanayina ya sauka ba kamar yadda muka fita ba.

“Mutumen nan kamata yayi ki fada masa kina da miji tun farkon da yayi miki magana, kin san kina burge maza for no reason me ya ba zaki kama kanki ba? Ke komai sai an fada miki sannan zaki yi? Aisha tana da gaskiya be kamata na baki wayar nan a yanzu”

Ban ce masa komai fadansa sai kara min zafin hawaye yake.

“Ba ni wayar...”

Ya miko min hannunsa yana kashe motar. Sai da na hade yawu sannan na mika masa wayar.

“Zan baki amman sai nan gaba idan kin yi hankali, yanzu ko na barki da ita hankali ba zai kwanta ba, ai na ga darasi gurin abokina mata ba ku da amana if not taya kina tare da ni zaki zubar da hawaye saboda da wani da ba zai iya zaman aure da ke ba, ba zai iya miki rabin abun da na yi miki ba”

Na kalleshi.

“Amman zai ba ni farinciki, irin wanda ba zan taba samu a gidanka ba, da baka bar ni tsaye ba ka je kana waya da munafukar matarka ta ya wani zai min magana? Ko kuma an rubuta a goshina na ne cewar ni matar aure ce? Wayarka kuma ka aje bana so ko da nan da tsufa ne, idan ba ka yarda da ni a yanzu ba ba zaka taba yarda da ni ba har abada”

Na bude motar na fita a fusace na bar masa kofar a bude ba tare da na rufe ba. Falon na shiga na zauna kan kujera gaba daya na rasa me ke min dadi. A kan kujerar da nake zaune ya watsar siyayyar da muka yi.

“Noor For the very last time karki sake kiran Aisha munafuka, ko ba komai ta girme ki, ta cancanci girmama daga gurinki, balle kuma tana matata, ba zan yarda ki shigo gidana ki rainata ba, babu kalar soyayyar da bata nuna miki ba, idan baki gode ba karki zage ta ba zan yarda a raina min uwargidana ba uwar yayana, ki tsaya matsayinki...”

Uffan ban ce masa ba na tashi na shiga daki na kwanta kan gadona ina kallon OPO dake dakin hawaye na zubo, haduwata da matar a nan ya tuna min da waye Zafeer a gurina, abu da duk wanda ya san alakarmu zai yi mamakin ace ba shi na aura ba.

“Miye wannan?”

Ya tambaya a tsawace dagowar da zan yi ya watso min wani abu mai kamar magani a fuska da wata roba. Na tashi zaune na dauki maganin mai kananan yaya na duba, sai wata roba da ban gama sanin ta miye ba guda biyu, roba na fi duba domin ta yi min kama da balloon sai dai ta banbanta da ballon sosai, ba kuma zan iya fadar ko ta miye ba domin ban san amfaninta ba. Na sake duba maganin shi ma wani kalar magani ne mai 2 colors da ban taba ganin irinsa ba.

“Miye wannan.?”

Ya daka min tsawa har sai da hankalina ya tashi, gaba daya fuskarsa da hallitarsa sun canja jikinsa har rawa yake kamar zai doke ni.

“Ban san ko miye ba...”

“Karya kike munafuka, a jakarki na ganshi yanzu waya baki ina kika siya?”

Na girgiza kai amman na kasa magana domin tsoron fushinsa da nakr gani a yanzu ya cika zuciyata. Furta cewar a jakata ya gani ya saka na sauka da sauri da zimmar na tafi na duba jakar tawa da na bari a falon sai na ji ya fisgoni iyakar karfinsa na wulgar da ni kan gadon.

“Ina zaki je? Ba zaki fada min ba? Uban waye ya baki wannan maganin? Ina kika siya? Mi ya kawo condoms a jakarki?”
Chapter 11 · 0% Book details