← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 82

Sashe 5

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusura ta mike tsaye ta rakata har kofar falon da gaisa da mijinta sannan ta dawo falon tana tafiya kamar zata fadi, domin ita ma lafiyar bata wadace ba, mutuwar Momy ta taba ta sosai. Gurin da ta tashi dazun ta sake zaunawa idanuwanta suka cigaba da hasko mata hoton suna Safeena da ta yi arba da shi a wayar Kareem, wani abun da bata saba ji ko sha'awar aikatawa sai shi ne sanin dalilin Kareem na aje number Safeena har yanzu. Cike da son sani me sakon ya kunsa ta juya kanta sama ta kalli upstairs. Tsohuwar budurwarsa ce zai iya ajewa saboda tunawa da ita, waya sani ko suna gaisawa ma. Wata zuciyar ta fada mata. Amman fa tana da aure ko dai auren nata ya mutu ne? Saboda me zai aje Number matar aure a wayarsa, ita ai tana yin aure ta goge number tsohon saurayinta ta toshe duk wata hanya da zai iya jinta ko ta ganshi. Ko da yake ita ai mace ce shi kuma Kareem namiji ne, akwai banbanci koma dai miye su suka sani hakan be dame ta ba. Ta daga kafadunta sannan ta mike tsaye ta kashe wutar falon ta haura sama zuwa dakinta.

KAREEM POV.

Ya farka a makare gajiya da kuma bukatar da bachin yake da shi a jikinsa, ya hana shi sanin safiya ta waye har sai da rana ta fito misalin Bakwai da rabi. Shi da Yusura ba su saba tashin juna da asuba ba, balle ta shigo ta tashe she ko ta duba lafiyarsa, kara shi wani lokacin ya kan duba lafiyarta idan ya san ta kwanta da ciwo ko kuma aka wuni be ga alamar motsinta ba, domin ya san hakki nw da ya rataya a wuyansa kula da lafiyarta cinta shanta tufatarwa da kuma kwanciya. Ya farka cike da nauyin jiki da kuma zafin zuciya as well as na idanuwa, because he had a dream last night Momy zata tafi Ummara ta bar shi yana ta kuka yana hugging dinta yana rokon kar ta tafi ta bar shi. And when he wake-up he realized ta tafi kenan tafiyar da babu dawowa no more Momy Alive. Sai dai a mafarki ko a tunani ko hoto, he lost her forever.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un...”

Ya fada cike da bakinciki biyu, bakincikin rashin Momy da kuma na rasa sallah asuba da yayi gashi yau friday. Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya runtse ido ya girgiza kansa dake ciwo. It take him 20 seconds kamin ya sauko ya shiga bandaki yayi wanka yayi alwala ya fito ya gabatar da sallah. The second thing da yayi shi ne daukar qur'ane ya karanta. Yayi ta karatun har tara na safe sannan yayi addu'a yayi ma mahaifiyarsa, a nan ya ji ya samu relief na kuncin dake zuciyarsa even though ba zai tana fita kunci rashin uwa ba har abada. Gefen gadon ya nufa ya zauna, ya dauki wayarsa miss calls din Daddy ya fara cin karo da shi sannan na Safeena ga kuma sakonta na jiya da dare da kuma na yau da safe kamar yadda ta saba aiko masa na safe dare rana amman be tana bata amsa ba, kuma be taba amsa kiran da take masa ba, tun Momy na ciwon har ta rasu.

“Kareem ka ki ka kula ni, damuwarka ta haifa min da damuwa, na san rasa uwa akwai ciwo shiyasa nake kira na sanyaya maka zuciya”

This is the first time da ya ji he don't need her in his life irin totally, domin mahaifiyarsa ta shiga tsakaninsa da ita lokacin da take raye, yanzu ta tafi ba zai iya cigaba da kula ta ba, and maganar da suka yi na karshe ya gama fahimtar rayuwarta da kuma waccece ita. Goge sakon yayi sannan ya kira mahaifinsa suka gaisa.

“Yaya kake Kareem?”

“Ina lafiya Baba”

“Alhamdullahi, Allah ya kara sanyaya maka zuciya, i know it hurts alot amman ka yi hakuri haka rayuwa ta gada, kuma mu ma can zamu tafi sooner or later...”

“Haka ne Baba Allah kasa mu yi kyakkyawan karshe”

“Ameen Allah ya maka albarka”

“Ameen thank you”

Ya sauke wayar ya mike tsaye sai ga kiran Safeena ya shigo wayarsa. Saka wayar yayi aljihu ba tare da ya amsa ba ya dauki abubuwan bukata ya nufi madubi ya fesa turare ya fice daga dakin. Yana karewa falon kallo ya sauko kasa wutar falon a kashe dinning babu abinci, kitchen din ya leka sai ya samu wutar a kashe komai a watse da alamar yau bata shiga sauko ba. Kofa ya nufa har ya murda ya bude sai kuma ya rufe ya sake komawa sama wannan karon dakin Yusura ya tura ya shiga sai ya samu wutar dakin a kunne amman bata cikin dakin. Bathroom ya nufa ya bude ya leka sai ya hango ta zaune a kasa hawaye na mata zuba idonta sun kumbura.

“Baki da lafiya ne?”

Ta ki ta kalleshi.

“Lafiya kalau”

“Ina Tine?”

“Sun tafi school, na ba su kudi su siya wani abu school”

“Kukan na minene?”

Na yi shiru.

“Magana nake miki fa”

“Ba komai”

Ta amsa tana matse kwalla, a tsawon rayuwarta bata san samu ba sai dai rashi, ta rasa uba tun tana ciki, ta rasa uwa bayan ta zo duniya ta rasa wanda take tsakanin kauna a matsayin miji, yanzu kuma rasa Momy macen da ita kadaice gatanta a duniyar nan, duk wani shiri da kudiri da take da shi da take jiran mutuwar Momy. Shiga yayi bandakin ya kamata ya mikar da ita tsaye ya fito da ita ya zaunar da ita kan gadonta, a kan madubin dakinta ya aje keys da mini boxes din dake hannunsa ya fita, kasa ya sauka ya hada mata tea domin ya san ita bata shan coffee, ya hado mata da ruwa ya sake haurowa ya shiga dakin ya aje mata tare da cup.

“Ki sha zaki samu sauki”

Ta kalleshi tana jin wani irin tsanarsa a zuciyarta fiye da kullum.

“Me yasa muka yi ma Momy karya? Me yasa muka rayu akan karya? Yau ina bakinciki ina jin ciwon yadda na boyewa Momy irin zamantakewar auren da muke yi”

Kareem ya dauki keys dinsa.

“Ko ba komai ta tafi tana farinciki da aurenmu, ta tafi cikin kwanciyar hankali da jin cewar ta yi abun da ya dace”

Ya juyo ya kalleta.

“Ko yanzu lokaci be kure ba Yusura, zaki iya samun farinciki zaki iya auren wanda kike so ko da kuwa kin haifi yara dari, ki daina jin cewar Momy ta tafi ta barki tare da ni zaki dauwwama a bakinciki na har abada, Ba ni da matsala Yusura ko kadan, ki dan ba ni lokaci Bana son mutane su fara tunanin na fara cutar da ke bayan rasuwar Momy, be kamata aji cewar wani abun ya taso a tsakaninmu ba a yanzu”

Ta kai hannu ta share hawayenta wasu na zuba.

“Kullum cutar da ni kake Kareem, mafi munin abun da a yanzu na gano, shi ne rayuwar auren da muke yi a karya, rayuwa da kai a karkashin gida daya, yana tauye ni, ganinka a kullum yana kara min bakinciki, Yanzu taya zamu fuskanci duniya mu fadawa kowa gaskiyar da muke boyewa? Waye zai fahimta? Wane za a dauka gaskiyarmu ko karya?”

“Zan sama miki yanci Yusura, zan wanke ki a idon duniya, za a jinjina miki a san kin yi ma Momy kawaici, Kareem ba zai sake zame miki matsala ba na miki alkwari...!!!”

Yana kaiwa nan ya dauki boxes din ya fice daga dakin ta bishi da kallo tana jin wani sabon kuka yana baibaiyeta. Ta sani Kareem yakai ko wace mace ta yi fatan kasancewar da shi a miji, idan har za a so shi dan kyau ko kudi ko asali ko mutunci, sai dai ita bata duba wannan a so, bata taba jin kaunarsa ba, kuma bata taba fatan kasancewa da shi ba har abada. Saboda tana jin shi ne silar rabuwarta wanda take tsananin kauna ido rufe, domin shi ya fara amsawa Momy cewar yana sonta alhalin ya san a kasan zuciyarsa baya son ta, ita kuma da aka waiwaya ta gefenta sai ta kasa musawa saboda gudun kar duniya ta zage ta, Momy kuma ta ga kamar ta yi mata butulci. Idan har so gaskiya ne! Haka ma kiyayyah gaskiya ce! Kareem ya kai namiji amman bata sha'awarsa a matsayin miji ko nan da can, ko da ba zata sake auren kowa a duniya ba tana fatan Kareem ya rabu da ita, tana bukatar ta yi rayuwarta ita kadai ba tare da Kareem ba.

KAREEM POV.

A lokacin da ya isa gurin aikinsa just few people ya duba ya shiga office dinsa ya zauna, gaba daya ya rasa me ke masa dadi a rayuwar duniya, abubuwa sun tsarke masa, idan ya rabu da Yusura ko nan da shekara ne mutane za su ce saboda Momy bata raye ne, sai dai rabuwa da ita shi ne mafi a'ala domin sama mata yancin da take ta dakon zuwansa, sai dai yaransa fa? Ya makomarsu? Me zai fada musu ya makomarsu, and ta ya zai fahimtar da mahaifinsa da Hajiya Hassana Step mother dinsa da sauran yan'uwa na kusa cewar yana son rabuwa da Yusura ko nan gaba ne? Tunani be bar shi ya ji yunwar safe da rana ba har sai da ya bar asibitin ya isa restaurant dinsa domin baya sha'awar komawa gidansa a yanzu. Yana faka motarsa harabar kiran Safeena ya shigo wayarsa rejecting yayi ya saka ta a blacklist for the second time, sannan ya fito motar yana kallon motar Hafiz dake fake, rufe motar yayi ya nufi reception din. A office dinsa ya samu Barrister yana waya da wani akan wani case da ya shige musu duhu, ya zauna fuska ba yabo ba fallasa ya aje keys dinsa ya kwanta jikin kujerar kana kallonsa zaka san akwai damuwa a tattare da shi. Barrister ya sauke wayar yana kallon abokinsa cike da kulawa.

“Doctor dan Allah ka sassautawa zuciyarka, na san akwai matukar zafi da radadi na rasa mahaifiya, amman na daure kai namiji ne, namiji kuma ya saba daukar abubuwa irin wannan, Momy yanzu addu'a take bukata”
Chapter 5 · 0% Book details