← Book details Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 82

Sashe 49

Taki Zaman Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amman wannan sirrina ne, na fada miki ne saboda na yarda dake and i need someone to talk to, taya zaki aikata abun da zai iya janyo matsala ya janyo miki?”

Zan yi magana ya daga min hannu ya nuna min yatsa.

“Look Noor ina da yara, mahaifina yana raye ina da yan'uwa da abokaina, ko kadan bana son abun da zai zubar min da mutunci, na fada miki damuwata ne saboda na yarda dake, kuma ina jin kusanci da zuciyata, ba dan ki bayyana ma duniya ba, na san na aikata abun a lokacin da idanuwa suka rufe shekaru suka tsirewa tunani, and now i realize na yi wa kaina babbar barna and i regret it, you shouldn't discuss this with anyone!!”

Ya bude motarsa ya shiga ya bar ni a tsaye ina kallonsa hawaye na sauko min, domin be taba rufe da fada irin na yau ba. Har yayi baya sai kuma yayi gaba ya faka a inda ya faka dazun ya sake bude motar ya fito ya tsaya kusa da ni.

“I'm sorry, Na san na kaurara amman Noor ban ji dadin abun da kika yi ba, wannan sirrina ne, be kamata kowa ya ji ba ”

“Bana hira da kowa, ban taba fadawa kowa ba, kuma ita wanda ta ji daman ai ita abun ya shafa”

Na bashi amsa cikin sautin kuka. Idonsa ya sauke kasa yana sake fuskarsa.

“Bana nufin sakaki kuka ko kara miki damuwa akan wanda kike ciki, amman ni abun da kika aikata yanzu zai daga min hankali ya saka ni a damuwa, waya sani ko zaki sake fadawa wani? Kuma Safeena ba zata zura miki ido hakan nan kawai ki cigaba da rayuwa a free ba, bayan kin san sirrinta, ni da ita duk muna da iyali, ki rika duba wannan kamin ki aikatawa wani abun Noor”

Na share hawayena.

“Ta je ta bata ni gurinka ko?”

Ya rufe ido yana murmushi sai dai hakan be hana ni fahimtar damuwar dake shimfide a fuskarsa ba. Bude ido yayi yana min magana a hankali.

“Bata iya wannan, babu wanda zai iya wannan ma, just be careful yanzu Safaeena tana kiyayya dake ta kofa uku ne, Allah ya tsareki kuma ya baki zaman lafiya, amman Bestyna Noor ina son ki sani ko mutuwa na yi bana son na tafi na barwa ƴaƴana abun kunya”

“Ni ma ba zan so haka ba, kuma na maka alkawari daga wannan ba zan kara ba, kuma babu wanda zai ji”

Yayi tattausan murmushi da ya kara masa kyau.

“Thank You, Allah ya tabbatar miki da alheri”

“Ameen”

Ya sake Bude motarsa zai shiga.

“Shikenan tafiya zaka yi?”

Ya juyo

“Ko kina da bukatar wani abun ne?”

Na girgiza kai.

“I will miss you alot”

Yayi murmushi ya sauka kansa.

“Akwai abun da kike bukata na auren Noor? Akwai abun da Baba be miki ba?”

Na girgiza masa kai alamar aa. A ganina kamar be kamata na dora masa nauyin komai ba, kuma ai da kunya na bukaci kayan daki a gurinsa, domin su ne kawai nake saka ran Baba ba zai yi min ba, shi ma kuma ba ni da tabbaci.

“An yi komai”

Yayi murmushin dake nuna kamar be aminta da ni ba.

“Sai wata rana”

Wannan karon be sake kallona ba ya shiga motarsa yayi mata key ina tsaye ina kallonsa har na daina hango shi. Wata kila shi kam ba zai yi marmarina ba kamar yadda anke jin kewarsa tun a yanzu, ba mu wani dade a tare ba amman shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da shi.
Bayan tafiyarsa ne fahimci na yi katobara na bayyana ma Safeena na san komai a tsakaninsu ba dan ita ba, sai dan shi wata kila hakan zai iya haifar masa da matsala, sai dai iya abun da na sani shi ne, Safeena ba zata yarda asirinta ya tonu ba, domin tana da aure da yara kamar yadda ya fada, ni kuma ba zan sake tattaunawa da kowa akan matsalar ba.

Hakan da na yi ya saka na samu yanci gurin Safeena, mijinta ma ya samu kwanciyar hankali domin ana sauran kwana biyu a daura aure nake tambayarsa ya Safeena sai yake cin yanzu ai ta fahimci, tashin hankalinta ba zai hana aurenmu ba ta shafa masa lafiya. A raina na ce ko dai ta fahimci Ni din ba kanwar lasa ba ce ta bawa kanta lafiya da ni.

A daren ne yayi ta damuna da maganganu da be sana yi min ba, hakan kuma ya raunata yarda ta ya haifar min da tsoro akansa, sai dai na lura shi kam sam baya kunyar fadar haka, wata kila saboda ya taba auren ne, ko kuma yayi zaton a aurena na farko na san komai kamar shi. A yadda na lura Abdull irin mutanen nan masu masara kunyar ido da furta komai a take. Ni dai bana iya cewa komai idan ya jefeni da wani kalamin, na kan ji kaina yayi girma kunya ta rufe ni.

Washe gari gidanmu ya cika da yan'uwa mahaifina wadanda suka zo shirye shiryen abubuwan da za'ayi, ta hirar da Baba yake da su ne na ji yana fadar mai gidan Nabil wato Kareem yana da kirki da mutumci sosai.

“Yanzu bayan daukar nauyin karatun yaron nan da yayi, auren nan da za'ayi sai da ya same ni a majalisa ya damka min kudi mai yawa wai na kara na yi hidima, Allah dai yayi masa albarka ya yara masa yaransa, wutar nan ma da ta taso tsakanina da yan'uwan Hafizu shi ya kashe ta”

“Ai wasu masu gida haka suke da taimako da kirki, musamman idan sun san baka da shi, wasu kuma suna bakincikin abun da zaka samu ma”

Cewar Baba Garba.

“Haka ne, ni farko ma na dauka shi zai ce yana son Noor ne, kuma na ga kamar ba haka ba ne, ai ba dan kar ta ba ni kunya irin na wacan karon ba, Wallahi da sai na aura masa ita saboda kunyar abun da yake min, ya rike amanar abota”

Jin hakan a gurin Baba ya saka na ji Kareem ya kara kima a idona, tabbas shi din mutumen kirki mai son taimako, babu ruwansa da duba matsayi ko girma. Haka dai na yi ta jin suna ta hirarsu ta yan'uwa yana fadin mutanen da suka taimaka masa a yanzu da kuma aurena na farko. A lokacin da suka dauko zancen abubuwan da zai kai na ji Baba Garba yana tambayar Baba.

“Toh yanzu kai Magaji ka siyo mata kayan dakin ne?”

“Ni babu abun da na siya kuma babu abun da zan siya, ai ya fada mana da zarar an daura aure za su wuce can Lagos din da ita, to taya za a tsaya wani siyen kaya nan tun da nan za su zauna ba? Dubu hansin zan bashi a cikin kudin sadakinta idan sun je can ya siya mata abun da ya kamata”

Anty Larai ta ce

“Aa gaskiya be dace ka yi haka ba, ai ana son ka siyama yarka girma, ko dai ba mai tsada ba kowa ya san karfi ba daya ba, sai ka mata na iya karfinka saboda Allah magaji”

“To wai me za'a siya ma? Uwarta ta aiko mata da kaya, kuma ba a nan za su zauna ba, ai kayan sun isheta komai”

“Kayan da ta aiko mata kayan kitchen ne, kai kuma naka kayan daki ne da dan wani abu da za aka bawa ango”

“Aa aa aa karya haram ba zan iya kashe kaina ba, yarinya suka ce suna so ita za a ba su, ita da Allah yayi jininta jinin masu kudi me zai kai ni wahalar da kai na siye wasu kayan daki? Hafizu ma Allah ya masa rahama da kansa yace ba zai na yi komai ba ya dauke min komai”

“Toh shi wannan ai be ce ba, gaskiy...”

Bata karasa ba Baba ta tari numfashinta.

“Ni fa dan abun da na samu, gyaran gidana zan yi na kuna kallon yadda gidan nan gaba daya ya canja babu wani taimako da na samu, sauran kuma sai na bude shago na zuba kayan masarufi”

Jin cewar Baba ba zai yi min furniture ba ya disashe farinciki dake zuciyata, wata kila shi din ba kamar Hafiz ba ne da zai ce ya yafe komai, hakan kuma wani abun gori ne a gurina da danginsa da ma kishiyata. A ranar aka yi min kunshi mai kyau mai ja sosai, da dare kuma Hana da kawata Zainab suka raka ni na tafi gurin gyaran gashi domin ni ba mace ce ma'abociyar son kitso ba. A nan na samu damar fada musu damuwata, Hana ta nuna damuwata da jin cewar Baba ba zai siya min komai ba har ma take cewa.

“Yanzu da ace Mama bata aiko da wannan ba haka za'a kai ki ko spoon din aiki ba ki da shi?”

Na sake jin babu dadi domin Baba baya kyautata min a rayuwa, wasu hakokan da ya kamata uba ya saukewa yarsa shi baya sauke min su.

“Noor kar hakan ya daga miki hankali, Baba ya fadi gaskiya idan ba nan za su zauna ba, babu amfanin siyen kaya, daukar kaya daga Kano zuwa Lagos wani aiki ne babba, kuma kin ga yace ba a nan za su tare ba”

Zainab ta shiga kwantar min da hankali, na dube ta na ce.

“Amman wasu ko ba a garin za su zauna ba, ana yi komai Zainab a garin da miji yake, saboda can aiki yake yi ai, wata rana zai iya dawowa mahaifarsa”

“Ki gode Allah Noor, idan mijinki mai sonki ne duk ba zai ga wannan ba, kuma zai rike ki amana, idan ma Baba bai miki ba ke zaki iya yi ma kanki ko kuma shi mijinki yayi miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki Noor”
Chapter 49 · 0% Book details