← Book details Second Chance Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 128

Sashe 62

Second Chance Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amira tana fita wasu na shigowa gidan, a daidsita ya ajiyesu, kallon ta sukayi ta matsa suka wuce sai magana suke,
"Wallahi itace..." Taji days ta fada duk sai suka juyo suka kalleta, bata kou juya ba ta shjga motar dake jiranta, tana kallon su suka fashe da dariya sosai, she felt it but just brush it off kaman nothing happened.
.
After like 30 minutes drive suka iso family how dinsu, it was her mom only a gida, tana sallama hajiya dake zaune ta leko, there's one thing about amiras visit, mum dinta don't feel comfortable at all with her visit, sai ta tabbatar da ba wata matsala ya kawota ba take samun sukuni, tana jin sallama amira ta fito ta kalleta from head to toe ta kalli face dinta don tabbatar babu wata damuwa
"Lafiyar?..." Was abinda hajiya ta fara fada mata tana kallon ta, amira was not happy at all Amma what will she do
"Lafiya mummy..."ta amsa mata kanta kasa,
"Lafiya lau kuma baki je office ba...why are you at home amira..." Hajiya ta sake asking dinta sounding so inquisitive
"Mummy I just came to see you..."bata karasa ba hajiya tace
"Duka yaushe Kika bar gidan nan...why not ki kirani..." Amira waje ta samu ta zauna sannan tace
"Mummy in daina zuwa gidan nan?..." Ta fada sounding so calm
"Yes... except if it's important..." Ta amsa kai tsaye, amira kallon ta tayi ta Kura mata idanuwa said hawaye suka ciko mata idanuwa, sauke kanta tayi ta dab saki murmushi
"Mummy ki yafemin kinji.. dan Allah ki yafemin ki daina stigmatizing Dina..."ta fada sounding calm
"Am not stigmatizing you...kawaii I want the best for you...baki ganin you're very lucky...duk da tsiyar da kika aikata Allah ya baki miji dan gayu...irin mijin da yanmata sukeso...irin mijin da ba kowa ke samun irinshi ba... anything I do is for your own good.. nothing more..." Ta hajia ta fada tana zama kusa da amira, murmushi amira ta saki
"Nagode mummy..." Ta amsa mata sanna ta bude bag dinta ta fiddo kudin,
"Mummy gashi...zakka na fidda...sai ki bawa wayanda kuke bawa naku..." Amira ta fada tana mika mata kudin,
"Masha Allah..." Hajiya ta fada tana amsar kudin,
"Ya akayi Kika samu kudi haka...tunda this money determine you have millions.." inji hajiya
"Zinarai na na sayar...I want to start a new life..." Idanuwa hajiya ta zaro tana cewa
"Amira kina hauka?...why will you sell your gold. Zinarin da ya zama hot cake yanzun..." Hajiya ta fada sounding so angry, amira da kanta ke kasa cewa tayi
"Mummy I want to start a new life..." Ta sake maimaitawa, sam hajiya bata Gane Inda ta dosa ba instead she's thinking maybe sabuwar business zata sake da sauran su,
"Amma gaskiya baki da hankali...what sort of starting a new life...baki san gold is a huge investment ba...ya zaayi ki saidasu..." Kara wayar amira yayi, she didn't take it out of her bag instead sai ta cigaba da sauraran mum dinta
"You didn't even bother to tell me anything thing...kin girma da baki bukatar shawarar kowa..." Hajiya ta fada sounding so angry at her, amira shuru tayi not knowing what to say but one thing is she wants to see the message they sent her, she's someone who doesn't leave a single message on her phone, duk wanda ya shigo kou na mtn ne sai ta bude kou da kuwa bata karanta ba unlike faiz dake da tones of messages wanda bai bude ba,
"Gaskiya in na fada maki naji dadin abinda nayi karya...sam banji dadi ba...yanzun in zaki koma ki sayi gold din da kika sayar said kinji irin kudin da zaa saka masu..."hajiya ta fafa still sounding angry, ita dai amiss bata xe komai ba,sai da hajiya ta gama fadarta sannan ta amshi kudin hannun amira ta Mike ta shiga ciki, tana shigewa ciki amira ta fiddo wayarta tare da vude message dinta, the heading shows it's another insult from her enemies
"Shegiya mai gida ta dawo...mai waje ta dawo dole ki nade tabarmar karuwancin ki kiyi gaba...wallahi ke kinyi kadan kiyi zamam kishi da h
Yar halak...karuwa mara kunya asararra...tunds kinki ki bar gidan sai munyi maki wanka da acid da uwarki..." Zagi dai mara dadi, kullum it's as if she's compelled to read to the end, kullum sai ta karanta har karshe sannan take ajiye wayar, tana cikin karantawa hawaye na gangaro mata, she"s never getting use to this, she's never getting strong for this, each insult hit differently, Daman da message ya shjga cikin wayarta sai gabanta ya mugun Fadi sosai saboda fargaban abinda zata Gani, most of the messages these days are from them. Tana jin motsin mum dinsu da ta sake fitowa tayi saurin goge face dinta, hajiya saw her nan ta fara asking dinta what's the problem tace ba komai
"Ba komai sai kiyi min zaune kina Kuka kice ha komai?...Daman nasan da Akwai dalilin zuwa nan... yanzun kou ki fadamin kou kuma ki tashi ki bani waje..." Hajiya ta daka mata tsawa, nan ta dauki wayarta ta mika mata massage din yau, hajiya amsa tayi ta karanta halfway tace
"Ai sai hakuri amira... above all is you're very lucky you're married...Kar ki damu duk zasu manta da wannan abun komai zai wuce..." Ta fada mata in I don't care manners, amira kallon ta tayi as new tears na fita daga idanuwanta, ahankali ta bude another one tace
"Mummy...kalli wannan..."ta fada hawaye na gangarowa daga cikin eyes dinta hajiya kin amsa tayi tace
"Aa..ba sai na gani ba...kawai kije ki cigaba da hakuri wata rana sai labari..." Inji hajiya
"Mummy na gaji..." Amira ta fada tana hawaye
"Ya zaayi ki gaji tunda har Kika samu ciki kika boyemin ai you have to leave with it... just keep thanking God for giving you a loving husband..." Ta amsa mata, kou kadan babu sympathy at all, she feels she deserves whatever she's going through right now, amira maida wayarta cikin bag dinta tana goge face dinta da bayan hannunta, she looks so calm dukda she just cried, tana da gentle nature wanda haka yasa cikin datayi ya zama abun mamaki ga mutane da yawa da suka ki tun daga farko da kuma wayanda sukaji daga baya, ahankali ta mike ta kama hanyar ciki hajiya ta kalleta tace
"Ina Zaki kuma?..." hajiya ta tambayeta
"Ciki zan shjga..." Amira ta fada kanta kasa
"Why?..me zakiyi ciki Kuma.." hajiya tambayeta
"Ai mummy yace daya tashi office zai biyo ta nan ya daukeni..."
"Ok..." Hajiya ta amsa mata atakaice amira juyawa tayi tana tunanin she wishes her mum can see what's coming right now, da zata gan how she's going to miss her da kilan ta dinga treating dinta with more kindness, tamkar bakuwa haka ta koma a gidan ubanta, he mother doesn't want her to have any breathing space a gidan at all,. Old dakinta ta shiga ta bude datanta ta gan new more messages, nan kuma ta hau saving number mutane tanayi ta rubutawa faiz message ta whatsapp dinshi, ta rubutawa I love you ya kai sau ashirin Amma har yazo gidansu bai bude message din ba, she replied as much as she can before he came, har ciki ya shigo suka gaisa da mum dinta da seeing fajz makes her happy, bayan sun gama gaisawa ya fita amira tayi bankwana da mum dinta har da hugging dinta before ta fito suka kaman hanyar gida da faiz, hannunshi cikin nata ya dinga tuki da hannu daya har suka isa gida.

Bintu kan an fada mata zata dinga bata noni bayan duk hours biyu kuma an bata dan container da zata dinga bata nonon a ciki, it's very tiny, da akwai abinda take matsa nono dashi sannan da Akwai avent da zata zuba ciki wanda will keep the breast milk warm, kou kadan baa taba baby, da sukayi hour biyu aka bata kuma tana bude tiny mouth dinta tana sha kadan kadan, bintu wanka tasha sannan tasha lace mai tsada gaske, she looks so beautiful as a nursing mum, breast dinta sunyi kumburi sosai, tasha sarka da yan kunne na zinari, she looks so beautiful and elegant as always.
Chapter 62 · 0% Book details