← Book details Second Chance Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 128

Sashe 24

Second Chance Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iyami Kuma tana ganin alhaji bazai tafi daita ba ta Shiga bangaren ta da gudu ta dauko key dinta itama ta bishi, alhaji da ya Shiga  damuwa sosai Bai San taba biye dashi ba har saida suka isa hospital, tana parking ta fita da sauri tana neman wajen Dr, lokacin har a sakawa faiz Karin ruwa, Nan alhaji ya shjga inda Dr yake sukayi magana
'"Allah ne ya rufa asiri Bai shiga Kan titi ba da ba karamin damuwa zaa Shiga ba,...Amma sir...Yana da wata damuwa ne da zuciyar shi ke neman samun matsala.. " Dr da in yayi gudun tsiya yayi 30 ya Tambayi alhaji, alhaji da duk hankalin shi ya tashj kasa magana yayi, he is just feeling this boys pain
"I want to take him out...kana ganin he can travel..." da Sauri Dr din yace.
"Ai ba traveling bane matsalar shi...the only problem is happiness...in kunsan abinda ke neman lalata mashi zuciya kuyi mashi Kar kuyi loosing dinshi....duk inda zaa Kai shi yanzun the only thing da zaa Yi mashi shine a faranta mashi Rai..." Ya ya sake fadawa alhaji, their plan is really working don alhaji fita yayi ya Kira alhaji shamsu, kaman zaiyi kuka ya fara cewa
"Yaya...Dan Allah ka janye maganar Nan...ance in har Bai samu farin ciki ba Yana iya rasa ranshi...Dan Allah Yaya..." Alhaji haruna ya fadawa alhaji shamsu kaman zaiyi kuka
"Nifa Kar ka ja min sharri...daga fadin gaskiya sai ka Nemi ja min sharri kace Zan kasheshi...nidai in Kan wannan zancen ne daga yau Babu abinda ya shafeni Allah na ganin nayi iya kokarin ingan na gyara family a matsayina na babba.. " alhaji shamsu ya fada Yana kame kame ba don Komai ba sai don shima tunda yaji maganar faiz Yana hospital ya shjga damuwa don Kar ace sanadiyar rabasu da yazo Yi yasa ya mutu, kashe wayarshi yayi shi Kuna alhaji ya Shiga dakin da faiz yake kwance looking really sick drip na Shiga jikinshi Yana bacci saboda maganin da aka saka a drip din, hajiya na zaune ta Kama hannunshi sai kuka kawai take, sai da taga ran alhaji zai bace tayi shuru, kusa da faiz alhaji ya tsaya Yana kallon shi, ahankali ya Fara cewa
"If it's because of Amira kake neman swallowing zuciyar ka pls don't...daga yau Babu Kara shjga tsakanin ku..." Ya fada mashi kaman his eyes are open, hajiya Bata San alhaji really cares about faiZ sosai ba sai yau, sai shafa goshinshi yake yana magana in a very calm voice, Basu bar hospital ba har sai 12 na dare, wasu cousins Dinshi biyu suka zo zasu kwana dashi a hospital.
Family dinsu faiz is a very big one, suna da yawa sosai that in kana hidima kou baka Kira na waje ba sai ayi hidima lafiya, wace gari if you see how the hospital was so full tun wajen karfe 8, faiz look sick sosai don Daya farka cikin dare sai da yayi hawaye ba don komai ba sai don he feels if his plans fail then zaa raba Shi da Amira, Yana da damuwa cikin rashin sosai.

Amira Kam kou bacci batayi ba, sometimes in tana cikin damuwa takan samu tayi bacci at last Amma yau yanda taga Rana Haka taga dare, kou da kadan vaccu Bai dauketa ba, tana sallah ta kwanta thinking of what to cook for him, sai karfe bakwai ta tashi ta shjga kitchen tana hada ruwan tea sannan tayi Dan soye soyenta ta jera cikin basket, wanka ta shjga ta fito ta shirya, Bata bar Gidan ba sai karfe Tara saura, she's in a haste that kou kadan Bata lura motar bintu ba ta fice daga Gidan walking tana aduar ta samu abinda zai kaita hospital din, bata San wajen ba but she still holds the name of the hospital Daya fada mata sai da tayi tafiya sosai sannan ta samu Mai adaidaita ya dauketa bayab ta fada mashj inda zai kaita.

Itama bintu Bata samu baccin kirki ba ta Kira iyami jiya sosai Bata daga ba sai yau da safe ta kirata suka gaisa, dukda iyami is angry at her Bata nuna Mata ba, she asked her ya fajz ta amsa Mata da Yana lafiya
"Am sorry.. " bintu ta fda Tana kuka
'"it's ok..." Iyami ta amsa Mata
"Iyami pls wane hospital yake...' ta tambayeta, Nan iyami ta fada sunan hospital din,
"Iyami Dan Allah ki bashi hakuri... sharrin shaidan ne.. " ta fada tana Kik e
"Kina Ina ne?.." inji iyami
"Ina gidana. Na dawo jiya da daddare. " Ta amsa mata
"Well let peace reign...kece babba just let peace reign...har fada maki nayi in yayi maki ha daidai ba ki Fada min Amma dayake Baki daukeni uwa ba. Kou kilan ni ba yarenku bace..'"
"No iyami ba Haka bane...am sorry pls...ban karawa. " Ta fada cikin kuka
"Shikenan.. "
"Nagode iyami Bari in dafa abinci in kai mashi..."
"Ok..." Ta amsa Mata, sallama sukayi daita taji normal because she was thinking iyami will be so furious at her ba don komai sai don taga miscalls dinta da yawa, kitchen ta Shiga itama ta hada abinci Mai Rai da lafiya Sosai.

Sanda Amira ta isa hospital tna rike da basket, motoci cike da compound din hospital, duk yawanci family dinsu faiz ne, duk bai San sun zo ba because he is asleep again, wasu yanmata su uku gefe guda suna ganin amira Suka Fara magana, Daya daga cikinsu was like
"Wannan itace matar da Yaya faiz ya aura...wacce take da yaro din..." Ta Fada tana nuna Amira da Baki, duk kallon ta suka Fara Yi suna magana kasa kasa suna Dariya, some of the girls are not upto her age don in sunyi gudun tsiya suyi tsarar nazifa, duk jikinta babu Dadi ba don komai ba sai don she knows maganar ta kawai suke, tambayar wata nurse inda faiz take tayi aka nuna Mata Dakin, tana Shiga duk aka daga Kai Ana kallon ta, sallama tayi Amma duk babu wacce ta amsa sai wata kanwar faiz, ai the attitude alone make her want to run fast from the premises,
"Itace kou..." Taji Daya daga cikin su ta fada,
"Eh..." Wata amsa Mata, ji tayi kaman kasa ya tsage ta shige ciki saboda tsoro da Kuma kunya
"Ashe itace Yar iskar.... chabdin.. anji haushi..." Taji wata ta fada, the thing is Bata San masu magana ba, she have never seen any them dukda ha kallon su take ba, wasu ma dake gefe guda a wajen magana Suka dingayi kasa kasa sai suka fashe da Dariya, Amira tasan there's no way that she will sit between those people, ahankali ta juya rike da basket din data Shigo dashi, tana fita ta samu waje ya zauna tare da Ajiye basket din, dafe goshinta tayi tana boye face dinta Kar aga hawayen da take, she have never faced public humiliation kaman na yau, abun is so insulting, wato now she knows she's scarred for life, tasan this is never going to end
"Ke..." Taji an fada Mata kaman daga sama, da sauri ta daga kanta with wet face
"Sunana Maryam..nice yayar faiz.. nazo gidan faiz sau biyu Baki Nan...now you're here... abinda nake son fada maki is in kinsan abinda yayi daidai...in kin San ciwon kanki...ki tattara second hand body dinki ki bar gidan Nan... wallahi kou mutuwa wancan tsinanne zaiyi sai kin bar family din Nan... Kar kice ban fada Maki ba... wallahi ba buguwar zuciya ba kou buguwar rai ne sai kin bar family din Nan...ba zamu hada jini da karuwa ba...mu Yan gidan mutunci ne.... you're not welcome here. " Ta Fada Mata voice dinta very loud that wayanda suke dakin da fajz yake da Kuma wasu dakunan suka fito suna Kallon abinda ke faruwa, Amira dake zaune sai kuka kawai take at this point she feels she's never getting married again.. never!!! Mikewa tayi da sauri ta bar wajen leaving her basket a wajen, sauran kadan su ci Karo da bintu, kou kallon inda bintu take batayi ba ta bar hospital din Tana kuka,

Alhamdullilah
1/3/22, 21:38 - Sadiya Mika'il: 11

Zuwairat ummumaryam

1️⃣1️⃣
Chapter 24 · 0% Book details