← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 55

Sashe 9

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashin hankalin sa da damuwar sa bai san me zasu tattauna da mai martaba ba abinda yake sake d'aga masa hankali kenan ya kasa zaune ya kasa tsaye, Suhail ne ya shigo ganin halin da mahaifin sa yake ciki ya saka yace, "Ranka ya dad'e lafiya?."
"Asad ya fad'a maka dalilin fitar su da mai martaba?."
"A'a bai fad'a min ban ma san zasuyi tafiyar ba."
"Oh god! Laifin kane Suhail da ka bashi madarar nan jiya duk da ba haka ba, yanzu gashi sun tafi taro Kaduna ko ni ba'a nema ba matsayina na waziri a masarauta daga shi sai ni amma ya tafi daga shi sai Asad, me suke so su mayar dani ne a masarautar nan?."

Yadda yake fad'a tashin hankali ya bayyana k'arara a tare dashi Suhail ya kwantar da murya yace, "Kayi hak'uri Abba ka bani lokaci matuk'ar ina raye babu wanda zai mulki garin nan sai kai."
"Kana shirme a haka zan mulki garin?! Ka manta kane ka b'arar da damar da ya k'i shan madarar nan jiya?, kasan mahimmacin maganin da na baka kuwa Suhail?. Na baka sabida na yadda dakai amma sai ka bani kunya" Ya fad'a da fad'a sosai yana kallon sa.

"Abba indai kaine ka haife ni nayi maka alqawarin zan yi duk abinda zanyi wajan ganin bayan Asad bama shi kad'ai ba dukka su ukun a hankali kowa zai k'are, ka bar komai a hannuna barewa baza tayi gudu d'an ta yayi rarrafe ba, zan baka mamaki Abba zan tabbatar maka da Jarumi ka haifa" yana fad'a ya fita daga falon ya ya bar mahaifin nasa a tsaye yana kallon sa.

Murmushin jin dad'i yayi jin abinda Suhail yace ko babu kowa hankalin sa ya kwanta kad'an. Sai a lokacin ya samu dama da kwanciyar hankalin fita daga gidan.

A cikin gidan sarki kuwa Mama tana zaune a falon ta ita da k'awar ta kuma aminiyar ta mai suna Sadiya suna tattaunawa Mama tace, "Sadiya bana son wani tsaiko ko katanga da zata shiga tsakanin Asad da mulkin garin nan, in wani daga cikin yaran nan baiyi mulki a garin nan ba na shiga uku Sadiya."
"Baza ki shiga uku ba ranki ya dad'e, ai mulki ma kamar Asad yayi ya gama ne, in kika cire rashin son magana irin na Asad bashi da wani aibun da za'a hana shi mulki, to a tak'aice ma waye yake da qualities d'in da yake dasu kaf gidan nan da dangin mai martaban?."

Mama tace, "Babu, amma kin san akwai y'an taka haye, tsaf waziri da Sa'adatu zasu shiga su fita wajan ganin buri na bai cika ba, zasu iya ni na sani hatsabibai ne sune suka mayar min da Aliyu na haka, sune suka mayar da Hydar haka, Asad ma ya gagare su ne shiyasa suka kasa yi masa komai. In kika duba su galadima da sauran y'an uwan mai martaba basu damu da sarautar nan ba harkar gaban su kawai suke banda shi. Sadiya idan Asad baiyi mulkin nan ba zan iya mutuwa."

"Baza ki mutu ba ranki ya dad'e sai kin d'auki jikan ki d'an sarki kuma jikan sarki shima kuma sarki, Muma ai ba zuba idanu zamuyi muna kallon su muna da namu hanyoyin da zamu bi wajan ganin mun b'arar da duk wani hatsabiban cin su." Numfashi ta sauke tace, "ni bana jin wannan Sadiya, duk wani jifa da zasu yo mana su sun san nima ba kanwar lasa bace, abinda yake gabana a yanzu bai wuce Asad, baya son mulkin nan ko kad'an balle ya mayar da hankali a kai, ki duba inda yana da hankali yana kuma son abin yadda ake maganar nan da yanzu bai nemi matar aure an yi biki an gama ba?."

Jin hakan sai Sadiya ta sake gyara zama tana murmushi tace, "Abinda ya kamata kenan Ranki ya dad'e, ki tilasta masa yazo yaga Jidda ayi komai a gama tunda sai yana da aure za'a bashi mulkin nan. Kuma Jidda y'ar gida ce ba buk'atar a tsaya bincike ko wani dogon jawabi ba."
"Bari kawai Sadiya, Asad baud'ad'en hali ne dashi baya ganewa ko kad'an abinda yake gaban sa kawai shi yake yi, dole ma a dawo da maganar Jidda ko bai sani ba za'a d'aura auren sa da ita sai dai yaji labari kawai."

Sadiya tace, "A'a ranki ya dad'e sai aita magana kuma a masarautar nan ace dan a bashi mulki kika yi masa auren dole, ki bar shi ayi komai da sanin sa na tabbata ai bazai k'i zab'in ki ba." Kai take girgizawa kafin tace, "Sadiya duk wanda zai shiga tsakani na da mulkin nan sai na kawar dashi, bana son wani tsaiko ko katanga a tsakanin Asad da karagar mulkin garin nan, burina na zama uwar sarki kuma zai ta tabbata, bazan lamunci wani abu da zai b'ullo daga sama ba, ko meye shi bazan lamunta!."

Sadiya tace, "babu shi ranki ya dad'e, ko meye shi munfi k'arfin sa, ko aljan ne a gaba muke dasu balle mutum, haba shi d'in yasan karo da aljani ba dad'i." Kai take girgizawa ta lumshe idanu kafin tace, "Ina da buk'atar zuwa Kano."
"Kina da iko ranki ya dad'e." Cize baki take zuciyar ta nayi mata tiriri bata son duk abinda zai hana Asad yin sarauta ko meye shi.

A b'angaren waziri a zaune suke a katafaran falo na alfarma shida Hajiya uwar gidan sarki kenan sai Suhail a gefen su a zaune waziri yace, "kina da masaniya akan fitar da mai martaba yayi da Asad?."
"Ina nake da ita a gaba dai ya fad'a masa amma bai ce ga abinda zai kai su ba. Nifa na gaji a wannan tafiyar da sukayi Allah kad'ai yasan abinda suka k'ulla shiyasa ko kai ba'a nema ba, a kawar da Asad kawai shine jin dad'i na."

Numfashi waziri ya fesar yana kallon sama kafin yace, "farkawa rana d'aya tsaka a rasa Asad ba k'aramin abu bane sai dai muyi masa abinda zai bi jikin sa ta yadda koda mutuwar yayi ba wanda zai zargi komai." Tace, "to ya za'ayi kenan?." Wani abu ya jawo a gefen sa ya d'auko ya kwance ya fito da wata laya k'arama an nannad'e ta da bak'in zare ya nuna mata yace, "Wannan nake so a saka a k'asan kafitar da yake kwanciya, matuk'ar yayi kwana uku yana kwanciya a kai zance ya k'are. A hankali abin zai dinga shiga jikin sa rana d'aya kawai sai a neme shi a rasa."

Kallon sa take yi hakan ya saka yace, "babban aikin shine wanda zai saka shi a k'asan katitar tasa, kin san ko a cikin nasu d'akin sa yana da wahalar shiga." Hajiya ta kalli Suhail tace, "Suhail shine zaiyi wannan aikin domin Asad ya amince dashi koda ya shiga d'akin sa bazai kawo komai ba."
"Anya Suhail zai iya?, bana so a samu matsala ne kamar wancan lokacin" ya fad'a yana kallon Suhail d'in.

Suhail ya gyara zama yace, "a wannan karon baza'a samu wata matsala ba Abba, zanyi iya bakin k'ok'arina wajan ganin na saka masa ina da tabbacin bazai kawo komai a ransa ba." Hajiya ta girgiza kai tace, "ni nasan zaka iya kai kad'ai ne daman ya cancanci ka yi wannan aikin in ka duba ko bayi basa shiga d'akin Asad, har kawo gobe ban san wacece ko waye yake gyara masa d'aki ba."

Waziri ya girgiza kai yace, "gashi Suhail ka kula kar a samu matsala kamar wancan, ka tabbatar ka saka masa wannan layar a k'asan Katifar sa." Karb'a Suhail yayi ya juya layar a hannun sa sannan ya saka a aljihu yace, "babu damuwa an gama."
"Shikenan tashi kaje" mahaifin sa ya basa umarni ba musu ya tashi ya fita.

"Wai kana da tabbacin wannan abinda ka bayar zai yi mana abinda muke so kuwa?." Kallon ta yayi yace, "kar ki damu ni nasan abinda na bayar ai in kin amince da abinda zan iya to ki yadda."
"Allah ya bamu sa'a."
"Amin. Zan fita yanzu daga gidan daga baya sai ki fita kema." Kai ta d'aga ya fita ta bishi da kallo tana tunanin mafitar waziri ba mafita bace dole ta samo mafita da kanta.

Suhail yana barin gidan cikin gidan sarki ya tafi yana zuwa kasancewar bashi da shamaki da ko ina b'angaren mazan ya tafi, nan ya samu Aliyu baya nan sai Hydar shida abokin Asad Hafiz suna zaune duk da ba hira suke ba, da sallama ya shigo ya samu waje ya zauna yace, "Hydar barkan ku." Amsawa sukayi dukkan su daga nan kowa yayi shiru.

Can ba jimawa Suhail ya mik'e tsaye direct ya nufi k'ofar da zata kai shi d'akin Asad yana gab da shiga Hafiz yace, "Suhail Asad baya nan." Cize baki yayi tare da runtse idanun sa kafin ya juyo bayan ya daidaita fuskar sa yace, "yeah I know, zanyi amfani da toilet d'in sa ne."
"Nooo ga public a falon nan in ma ba shi ba why not kayi using dana Hydar."

Suhail ya kalle shi shima shi yake kallo kafin yace, "okay" abinda yace kenan ya juya zuwa band'akin da yake falon ya shiga badan zaiyi wani abun ba sai dan ya kawar da shakku. Babu wanda ya yi magana a cikin su har ya fito ya zauna nan ma babu wanda ya tanka kowa da abinda yake yi.

Sun jima a haka babu wanda ya motsa kafin Hydar ya tashi ya shiga d'akin sa ya barsu a falo, shi Hafiz yana so Suhail ya fita dan baya son barin sa wajan shi kad'ai shima kuma yana so ya tafi domin ya cimma k'udurin sa.
Dukkan su haushin juna suke ji babu wanda yake magana babu wanda kuma yayi yunk'urin motsawa.

Ganin Hafiz yana yi masa wani kallo na rashin gaskiya kawai sai ya tashi ya fita ya bar masa falon da sabuwar niya da kuduri a zuciyar sa.

*☆☆☆*
Chapter 9 · 0% Book details