← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 55

Sashe 27

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Khalil taji yace, "A unguwar Katsalle muke." Kallon ta yayi sai ya kalli Khalil yace, "Muje."
"Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni Rauda na shiga motar wanda bai san darajar d'an adam ba sai kansa kawai ya sani Allah ya kiyaye ni. kaje can ka k'arata kai kad'ai tunda ku y'ay'an manya da y'ay'an masu mulki baku san kowa ba sai y'an uwan ku masu mulki. Dan kana d'an sarkin garin nan baka isa ka saka ni nayi abinda banyi niya ba, bada hak'uri ya gagare ka akan buge ni d'in da kayi a yanzu me zai kaini shiga motar ka?" Rauda ta fad'a cikin masifa lokacin hijjabin ta yake ja baya har tabon sallar dake goshin ta ya bayyana.

A wannan lokacin suka tsallaka bai juya ya kalle ta ba bai kuma bar wajan ba amma kalaman ta sun tabbatar masa ta tab'a had'uwa da Aliyu ne yadda ta zayyano abinda ya faru yasan tabbas Aliyu ta gani take tunanin shine, katin maganin ya gani a k'asa ya d'auka yana kalla kafin ya juya sai yaga har sun b'ace masa, numfashi ya sauke ya shiga mota zuciyar sa na bugawa, kallo inda suka bi yake yi zuciyar sa na fizgar sa zuwa wani tunani daban ya runtse ido ya kunna motar ya buɗe idon sa ya ja ya bar wajan.

*tofa fan's an gamu fa.*🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️

*KWANTAN ƁAUNA*
      FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*013.*

Rai a b'ace Rauda ta shiga gida Khalil ya taimaka mata ta ajjiye sandar hannun ta ta zauna a kan farar kujerar da take tsakar gida shi kuma ya zauna a k'asa. Yanayin ta Umma ta kalla tasan an tab'o ta kuma tasan bazai wuce akan maganin ba hakan ya saka tace, "ko baki ce ba nasan ya hana ki maganin ne shiyasa kike kunbura fuska, sai kiyi hak'uri." Rauda tace, "daga neman taimako Umma sai ya zage ni? Har yana cewa da yasan halin Baba tun farko bazai bada bashi ba."

Umma ta murmusa tace, "ban ga laifin sa ba Rauda; yanzu kafin wannan kud'ad'e masu tarin yawa su fito daga hannun baban ki a shekara goma a fama. Yayi k'ok'ari fa da ya baki ma dan ba kowa ne zai bada magani mai tsada kamar naki ba, Allah yasa baki masa rashin kunya ba dan ya taimaka miki." Shiru tayi bata amsa ba Baba da yaji komai ya shigo yana fad'in,

        "In ma tayi masa rashin kunyar ita ta jiyo ai ita k'afar zata damu da ciwo sabida rashin magani bani ba." Shiru sukayi dukkan su kafin Khalil yace, "Umma wani kyakykyawa kamar balarabe ya kusa kad'e Anty yanzu har sai da ta fad'i k'asa." Umma tace, "Kuma dai?."
"Amma ai bata ji ciwo ba ai. Umma ta yi masa rashin kunya yace muzo ya kawo mu gida tak'i kuma baki ga motar ba babba" ya fad'a yana fad'ad'a hannayen sa alamun girma.

     Baba da yake alwala a durk'ushe furzar da ruwan bakin sa yace, "A koda yaushe ke ai bak'in halin ki yake ja miki alkhairi yake tsallake ki ya koma kan wanin ki. inda kin shiga motar da bai siya miki maganin ba." Umma tace, "Rauda akan me zaki masa rashin kunya? Meyasa ke baka jin kunyar yiwa babba rashin kunya ne?." Rauda tace, "Umma nifa ba rashin kunya nayi masa ba na fad'a masa abinda yake raina ne. shine wanda nace miki ya mare ni lokacin da na raka su Habiba gidan sarki shine na amayar masa da abinda yake zuciya ta a lokacin ban samu dama ba ina jin tsoron doki ya hana ni mayar masa."

Umma ta wara idanu tace, "D'an sarkin Katagum guda masu ji da kud'i da mulki kika yiwa rashin kunya Rauda?, Yaron da an masa shaida bashi da kirki ina ke ina shi?, in ya saka aka yi miki wani abun fa?." Rauda ta turo baki gaba tace, "To Umma dan yana d'an sarki sai yayi min abinda yaga dama na k'yale shi? Bafa haifata yayi ba da zai fad'a min magana na tsaya ina kallon sa, wallahi saina rama dan mutum ne shi nima mutum ce."

         "Sannu y'ar gidan dangote, nace sannu y'ar gidan shugaban masu kud'in duniya. Wato in ana neman talaka mai fad'in rai wanda aka fad'a a hadisi aka same ki Rauda an shafa Fatiha. Tunda bake ban tab'a ganin yarinya mai karanbani da nuna isa kamar y'ar wani ko y'ar wata sai ke da kanki yake rawa. D'an sarki guda kika yiwa rashin kunya, bakya jin tsoron wani abun ya same ki ke ga fitsararriya mai ji da fitsara. Har yace miki kizo ki shiga mota ya kawo ki kika ki sabida girman kai yayi miki yawa. To Allah ya isa abinda yayi niyar baki in ya kawo ki kika yi mana bak'in ciki da yau nasan kaji zamu ci mu kwanta, sakamakon rashin kunya duk abinda ya saka aka yi miki ke kika ja kar sunan Adamu ya fito a gaban sunan ki" Baba ya fad'a yana buge rigar sa ya fita.

      Umma ta girgiza kai tace, "Wai Allah ya isa, Malam har ya saka a ran sa ma za'a bashi wani abun bama illar shiga motar tasa yake hangowa ba kawai a bashi kud'i koma me yayi miki in kin shiga motar ke kika jiyo. Kai Allah ya kyauta" Umma ta fad'a tana murmushin takaici kafin ta kalli Rauda tace, "Kinga Rauda na raba ki da y'ay'an masu kud'in nan babu ruwan ki dasu in ba so kike ki jawo mana matsala muna zaune lafiya ba. Ina ke ina yi masa rashin kunya? In yaso a batar dake yana da damar yin hakan babu wanda yasan shine yayi, ki dawo hankalin ki dan Allah bana son wannan fitsarar taki." Rauda bata ce komai ba tayi shiru k'afar ta na ciwo rashin shan maganin da batayi ba.

*☆☆☆*

         Tun a mota yake tunani har ya isa guest house d'in mai martaba ya shiga kamar yadda ya saba shi kad'ai ya zauna a akan kujera yana sauke ajiyar zuciya. kallon katin yake yana kallon sunan ta kamar a jikin sunan yana so ya gano wani abun.  _Sa'ar ka guda nasan darajar d'an adam da babu abinda zai hana ban wanke maka taka fuskar da mari kamar yadda ka mari tawa._ kalaman ta suka fad'o masa a rai ya runtse ido jin abinda bai tab'a ji ba yana kawo barazana ga kunnen sa.

     "Ta tab'a had'uwa da Aliyu" ya furta a hankali idanun sa har lokacin a kulle zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri. "Wacece ita?" Ya tambayi kansa yana dafe kansa da duka hannayen sa idanun ta da goshin ta na sake dawowa masa cikin kansa da idanun sa a hankali.
Sake kallon katin yake maganar Khalil na sake dawo masa zuciyar sa ya kai idanun sa sunan asibitin da aka rubuta mata maganin. Mik'ewa  zaune yayi sosai mamaki ya kama shi ya wara idanun sa ganin sunan asibitin su ne ya tafi k'aramin tunani kafin ya d'auko waya daga aljihun sa da azama.

        Sai da ya danna number Dr Yasir ta shiga sai kuma yaji haushi ma akan me ma ya saka shi ya kira Dr, "Assalamu Alaikum, Ranka ya dad'e" muryar Dr ta katse tunani ya kalli wayar kamar bazai yi magana ba sai yace, "ehemmm Hydar" sai kuma yayi shiru jin hakan Dr yace, "Jikin sa ana samun ci gaba saura kiris ma ya farfad'o domin ana samun cigaba fiye da baya."
"About yarinyar da ya buge fa?." Gaban Dr ya Fad'i jin abinda yace yayi shiru Asad yace, "tana ina?."

            Dr yace, "Prince Mama ta saka an sallame ta tun kwanakin baya." Asad yayi shiru cike da mamaki yasan tsaf Mama zata aikata abinda yafi haka ma hakan ya saka shi yin shirun kafin yace, "meye sunan ta?." A sama Dr yaji maganar hakan ya saka shi yin shiru kafin yace, "na manta ne prince abubuwan da yawa marasa lafiyar da yawa babu lallai na rik'e." Shiru dukka sukayi kafin Dr yace, "Na tuna, sunan ta Rauda sunan mahaifin ne dai na manta."

       Asad baice komai ba ya yanke wayar ya sake kallon katin yaga sunan da ya fad'a masa ya ajjiye katin a gefe yana kallo, _Mama meyasa?, ga yarinya yanzu a cikin yanayi mara dad'i, babu kud'in magani gashi har tana yawo da sanda a silar Hydar._ ya fad'a a zuciyar sa yana sauke numfashi shi jikin sa duka babu dad'i.

        Kiran magrib ya tashe shi yayi alwala ya fita masallacin estate d'in yayi sallah sannan ya dawo ya  d'auki motar sa zuwa gida. Wajan Mama ya wuce kai tsaye bai same ta a falo ba ya shiga d'akin da Hydar yake a nan ya ganta a zaune kusa dashi kamar koda yaushe. Da sallama ya shiga ta kalle shi ta d'auke kai ya tsaya a kan Hydar yana kallon sa.  Har zai mata magana sai kuma ya fasa ya d'auke kansa itama kuma bata ce masa komai ba. Ganin bata kallon sa ya saka yace, "Mama ko meyasa aka sallami yarinyar da Hydar ya buge daga asibiti?" Ya fad'a a tausahe kamar ko yaushe. Kallon sa tayi ta harde hannun ta a k'irji tana kallon sa alamun bazata yi magana ba kenan.

"Na saka an sallame ta d'in sabida bata dace da zaman wannan asibitin ba akwai abinda za'a yi min ne?. kuma ahir naji kaje wajan ta da niyar wani abun, shima Hydar nice na dakatar dashi kar ka jawo abinda raina zai b'aci a kanta iya abinda aka yi mata a asibiti ya ishe ta" ta fad'a a kausashe tana kallon sa.  Ajiyar zuciya yayi yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ban fad'a dan ranki ya b'aci ba." Kai ta kawar gefe tayi masa alama da ya bata waje ya kuwa fita kamar yadda tace.
Chapter 27 · 0% Book details