Sashe 32
Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Naga kin gaji sosai ga sallah ana yi, zan koma amma in sha Allah gobe zan yiwa Baba bayanin aiki da za'ayi in sha Allah." Kai ta girgiza kafin tace, "Allah ya saka da alkhairi."
"Amin. Amma kin san wacce irin addu'a nake so kiyi min?."
Kai ta girgiza alamun a'a yace, "Ki min addu'a Allah ya mallaka min ke a matsayin matata." Murmushi tayi sai tace, "Ban d'auka zaka yi wannan fatan ba duba da irin iftila'in da ya same ni." Murmushi yayi yace, "Wai da sai na guje ki kenan?."
Ya sake yin murmushi yace, "Ni Rauda nake so ba abinda yake tare da Rauda ba, zuciyar Rauda nake so ba gangar jikin Rauda ba. Ilimi, halayya, tarbiyya, nutsuwa, iya magana, girmama na gaba, su nake so a tare da Rauda ba k'afar ta ko hannun ta ba. Rauda a yadda nake jin ki a zuciyata ba fata nake ba ko ido da k'afa da hannu kika rasa wallahil azim ni mai iya auren ki ne, soyayyar gaskiya nake miki ba soyayya dan wani abun ba. Ina fatan ki fahimta?."
Murmushi tayi mai d'auke da jin dad'in kalaman sa ko babu komai ta tabbatar da soyayyar ta ta gaskiya ce a zuciyar sa tace, "Na amince da duk abinda ka fad'a, ina kuma alfahari da hakan." shima yayi murmushi yana kallon ta yace, "A karo na farko da nake ganin murmushi a kan fuskar ki har kike min doguwar magana haka lallai addu'ar da nake ba dare ba rana Allah ya karb'a ya kuma fara biya min." Murmushi ta kuma yi ya kalli agogo yace, "Ana ta sallar i'sha zan tafi."
"Ka gaida gida da mutanen gidan."
"Zasu ji in sha Allah. A gaida Umma da kowa da kowa." Ta amsa da to kafin suyi sallama ta koma cikin gida.
Sallah Umma ta samu tana Khalil ya d'auko mata kujerar ta ta zauna dan ita ba sallar zatayi ba, bayan Umma ta idar da sallah Inna ma na zaune ita da Rahma Umma tace, "Har ya tafi?." Kai ta d'aga alamun eh.
Baba ne ya shigo da sallama suka amsa ya nemi waje ya zauna yana fad'in, "Ke Rauda Anas yace zai biya ko nawa ne ayi miki aikin k'afar ki, zuwa gobe zan nemi likitan da ya amince da aikin sa ayi komai a gama."
Umma ta kalli shi tace, "Amma malam hidimar yaron nan bata yi yawa ba? Ka duna irin abubuwan da aka kawo mana fa yanzu kuma ya kuma biyan kud'in aiki...? Bafa ayi auren nan ba kar a fara zagin mu a gari."
"Bafa rok'on sa mukayi ba shi yayi niya ya bayar."
"Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi" Umma ta fad'a kawai dan babu yadda zatayi.
Baba yace, "Abinda ya kamata kice daman kenan." Yana fad'a ya juya zai fita Inna tace, "motar kwadayi in ka hau zata sauke ka a tashar wulaqanci." Juyowa yayi ya kalle ta yace, "kinga munafurcin ki da bak'in cikin ki shine ya saka ga y'ar ki nan a zaune kusa dake babu wanda yake tayawa, kuma wallahi in baki kiyaye ni ba sai na bayar da ita sadaka a masallaci."
Bata ce komai ba ta mik'e ta shiga d'aki Rahma ma ta bi bayan ta yaja tsaki ya fita. Umma ta kalli Rauda bayan sun bar wajan tace, "Rauda kin masa godiya yadda ya kamata kuwa?."
"Nayi Umma."
"To ya kike jin sa a ranki yanzu? Nidai ina miki sha'awar auren sa badan yana da abin hannu ba sai dan yana son ki, duk da abinda ya faru dake bai guje ki ba sai ma sake bibiyar ki da yake yi wannan alamu ne na masoyin gaskiya."
Shiru Rauda tayi bata ce komai ba Umma tace, "kiyi tunani ki kuma yi addu'a in shine alkhairi Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya watsar da maganar ya kawo miki mai alkhairi." Shiru nan ma tayi bata amsa ba ta lumshe idanun ta nan take fuskar Asad ta ziyarci fuskar ta sai ta bud'e idanun ta tana tsaki.
Umma ta kalle ta ganin bata ce komai ya saka ta ja bakin ta itama tayi shiru.
*☆☆☆*
Asad yana barin wajan a mota gida ya koma dan ya samu kiran mai martaba, yana ajiiye mota b'angaren mahaifin sa ya nufa aka yi masa iso ya shiga ya same shi kad'ai kamar ko da yaushe a zaune a falo. Da sallama ya shiga yayi masa izinin zama ya zauna kafin yace, "Barka da dawowa, da fatan an dawo lafiya." Mai martaba yace, "lafiya lau, ya jikin naka?."
"Na samu lafiya."
"Amma yanayin ka bai gwada hakan ba."
Shiru Asad yayi bai ce komai ba mai martaba yace, "Asad yanayin ciwon da nake ji a jikina kullum sake gaba yake yi, bana son Allah ya d'auki raina ban bada amanar talakawana a hannun nagartaccen mutum ba, dan haka zan dawo da bara bana."
Asad yace, "Amma Takawa....." Mai martaba ya dakatar dashi yace, "Abinda za'ayi kenan Asad, kai kad'ai ne nayi istikhara akan haka yfi sau babu adadi tunda kaga ina ta maimaita maganar ka d'auka kaine alkhairin katagum. Har yanzu kana mafaran da ka fad'a min?."
Asad yace, "Na kwana biyu banyi ba." Kai ya girgiza kafin yace, "ka cigaba da addu'a ka kuma cigaba da kula ba komai zaka yarda dashi ba, mak'iyan ka na kewanye da kai. wanda kake d'auka masoyin kanewani lokacin shine mak'iyin ka, wanda kake d'auka makiyin ka wani lokacin shine masoyin ka."
Asad cikin gamsuwa yace, "in sha Allah za'a kiyaye."
"Mahaifiyar ka ta sanar dani tayi maka mata za'a gaggauta maganar auren ka ana gama shagalin bikin zan sauka daga karaga na baka." Shi dai Asad bai iya cewa komai ba dan ba wannan ne a zuciyar sa ba, zuciyar sa bugawa take yi da sauri har sautin ta yana ji a kunnen sa.
Mai martaba yace, "zaka iya tafiya."
"Godiya nake, a tashi lafiya" ya fad'a da girmamawa ya fita mai martaba ya bishi da kallon burgewa da kuma sha'awa.
Sai da akayi sallah ya shiga wajan Mama ya samu bata nan ya k'arasa ciki inda Hydar yake yana nan kwance kamar koda yaushe.
Yana fitowa daga d'akin ya ganta a zaune a kan kujera tana waya yadda take maganar ya tabbatar da k'anwar ta take waya, zama yayi a gefen ta yana sauraron ta kammala wayar. Bata jima sosai tana wayar ba ta yanke ta kalle shi tace, "lafiya na ganka wani iri?"
"An nemi a k'asar Dubai zanyi....." ganin yadda ta d'aure fuska sai ya kasa k'arasa maganar yayi shiru tare da sunkuyar da kansa.
Fuska a d'aure tace"kalle ni." Ba musu ya kalle ta tace, "ko k'asar Dubai zasu d'auka su mallaka maka baza kayi ba Asad, zaman ka a nan shine burina ba barin ka k'asar ba. Akwai abinda ka nema ka rasa ne a nan d'in?." Kai ya girgiza alamun a'a tace, "to kar na sake jin irin wannan maganar a bakin ka, hukunci ne na yanke babu kai babu wani aiki sai na mulkin garin nan."
"Toh. Allah ya wuci zuciyar ki." ya amsa a tak'aice.
"Ya kuka yi da mahaifin ka?."
"Babu komai." Ta d'auke kanta daga kansa kafin tace, "kaji sauk'i, yaushe zaka je wajan Jidda?." Shiru babu amsa hakan ya saka ta kalle shi kamar zaiyi kuka yace, "san da kika ce."
"Gobe."
"Allah ya kaimu" ya furta a sanyaye.
Da hannu tayi masa alamar ya tashi ya bata waje kamar jira yake ya mik'e ya fita. B'angaren su ya tafi ya samu babu koma an k'ara masu tsaron k'ofa harda jami'an tsaro Mama ta ajjiye a wajan ya shiga d'akin sa yana mamaki a ransa yana aiyanawa tsoro bashi zai hana wani abun ya same shi ba, wanka yayi da alwala ya fito yayi sallah ya kwanta. Kasa jin dad'in kwanciyar yayi a kan gadon ya tashi ya jefa pillow a kan tiles ya kwanta yana kallon saman d'akin.
_Sabida Hydar ta zama gurguwa_ zuciyar sa ta cillo masa wannan tunanin ya lumshe idanu a hankali ya bud'e, juyawa yayi ya d'ora kansa a kan hannayen sa yana kallon sama yana tuno yanayin fuskar ta da yadda take masifa akan laifin da ba nasa ba, a bayyane yace, "A ina suke had'uwa da Aliyu? Ya akayi ta san shi?, me ya had'a ta dashi haka?. Ta kira shi mazinaci ya akayi ta sani?."
_ka sani ko itama ya neme ta? Kad'an daga aikin Aliyu zai iya zama dalilin yi masa rashin kunyar kenan._ zuciyar sa ta tambaye shi gaban sa yayi mugun fad'uwa ya mik'e zaune yana girgiza kansa yace, "nooo! In sha Allah hakan bai faru ba."
K'irjin sa yaji yana duka a hankali ya saka hannu ya dafe b'angaren zuciyar sa ya lumshe idanun sa, "What!" Ya furta a bayyane jin abinda yake ji a zuciyar sa da gangar jikin sa mai kama da tsaninin kishi. Tsaki yayi ya koma ya kwanta ya fara k'ok'arin mantawa da tunanin amma ya kasa ko ya ya kulle idon sa sai ta fad'o masa a zuciyar sa, duk yadda yaso kawar da tunanin abin bai yu ba dak'yar bacci ya d'auke shi.
Washe gari.
Karyawa ake da shayi mai madara har da budori a gidan su Rauda bayan y'an makaranta sun ci nasu kowa ya tafi gidan daga Rauda sai Rahma da iyayen su ana karyawa, Umma ta kalli Rauda da take shan tea a hankali kamar an mata dole tace, "Rauda lafiya dai?."
"Lafiya lau Umma" ta bata amsa tana kallon ta.
"In kin gama ki daure ki lek'a gidan Alhaji Musa ki yiwa matar sa gaisuwa babban yaron ta ya rasu d'azu, har akayi jana'iza kina bacci shiyasa baki sani ba." Rauda ta zaro idanu tace, "Ishaq d'an tane ya rasu Umma?." Ta fad'a tana dafe k'irji.
"Shi fa Rauda. Ki daure in kin gama kije tana son ki matar."
"To Umma in sha Allah, ai ka gaida mai gaishe ka tana sona. Allah ya gafarta masa."
"Amin, maza ki gama kije kafin rana ta bud'e sosai."