← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 55

Sashe 6

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can b'angaren ya sauke numfashi yace, "kawar da Asad abu ne mai sauk'in gaske a waje na, amma bazan yi yanzu ba zamu bari a d'an kwana biyu sai mu kawar dashi bayan shi sai a kawar da mahaifin sa mu siye kwamnatin Bauchi ta yadda dole mu za'a bawa mulki koda bamu cancanta ba."
"Meyasa sai an kwana biyu?, meyasa baza'a yi yanzu ba?, a kawar dasu duka biyun meye amfanin mai martaban?."
"Bana son yin gaggawa domin za'a iya gano mu."
"Babu wanda zai gano mu, kayi kawai mulki ya dawo hannun ka, tunda d'ana namiji ya kasance yaro k'arami banga d'an wacce zaiyi mulki a cikin mu ba, dan haka a kashe su duka mulkin ya koma hannun ka sai me!."

Murmushi yayi mai sauti kafin yace, "kwantar da hankalin ki uwar gidan mai martaba sarki komai zai zo yadda muka tsara, ki cigaba da jan Asad jikin ki kina nuna masa so da k'auna a gaban mahaifin sa ki ture mahaifiyar sa kome zakiyi baza ta gani ba, tasan sarauta tasan makircin dake cikin gidan sarauta, a hankali zamu saka bakin nasa ma ya kulle duka ya daina maganar gabad'aya kowa ya huta, kinga ai baza'a bawa kurma ragamar al'umma ba. Kashe shi ba mafita bace mu bar shi a raye ta yadda Rabi'atu tana ji tana gani y'ay'an ta maza uku zasu zama hoto basu da wani amfani."

Numfashi ta sauke ta lumshe ido ta bud'e tace, "Haka ne, bana so a d'auki lokaci a fara gabatar da komai domin ko wanne lokaci mai martaba zai iya canja shawara."
"Kar ki damu yanzu aka fara wasan ai."
"Sai na jika" tana fad'a ta yanke wayar tana wuci ita kad'ai kafin ta dai-daita kanta ta fito ta koma b'angaren mai martaba.

        A can b'angaren Waziri bayan ya yanke wayar da suke yi da ita ya kalli d'an sa Suhail da yake zaune yana kallon sa shima yace, "kana jin duk abinda yake faruwa, meyasa kayi wasa da maganin da na baka har bai sha madarar nan ba?." Suhail da ya fi mahaifin sa jin takaicin hakan yace, "Na bashi har zai sha abokin sa ya shigo sai ya fasa sha ya ajjiye, kasan kuma yana da basira ina na matsa akan yasha zai gano ni shiyasa na fito na barshi. Ka k'yale ni dashi Abbah ya riga ya amince dani a hankali zan shiga jikin sa na lalata duk wata garkuwar jikin nasa."

Dogon tsaki yaja yace, "aikin banza, inda ka san daga inda aka kawo wannan maganin da baka yi wasa dashi ba, yanzu kafin a sake samo shi sai an kwana biyu sabida hatsarin sa ya saka ba'a bayar dashi ko yaushe. Ka lalata komai Suhail."

Suhail ya cize bakin sa yace, "Abba zan gyara komai kada ka damu indai ina da rai mulki ya bar gidan su Asad ya dawo gidan nan, sai ka yi sarkin garin nan nima kuma sai nayi, burina kenan burin ka kenan, kada ka damu Abba alqawari na d'aukar maka sai naga bayan Asad, bai isa ya mulki garin nan ina numfashi a duniya ba, zan kawar dashi, zai zama bashi da amfani kamar y'an uwan sa. Asad zai zama tahiri sai dai a tuna shi ace Allah sarki." Murmushi mahaifin nasa yayi  cikin jin dad'i yace, "Ina alfahari da kasancewar ka jinina Suhail, nasan zaka iya Allah ya bada sa'a." Mik'ewa tsaye yayi kafin yace, "Amin Abba, ka zuba idanu zaka yi kallo" yana fad'ar hakan ya mik'e zai fita Waziri yace, "Suhail."

Ya juyo ya kalle shi yace, "Kar kaji tsoro, kar kaji tausayi, kar kaji d'ar a zuciyar ka. Ka manta dani da mahaifin Asad uwa d'aya uba d'aya muke, ka manta da kai da Asad y'an uwane ka d'auka baka tab'a sanin sa ba a wannan lokacin aikin ka zai tafi yadda kake so." Suhail ya girgiza kai cikin gamsuwa da maganar ya fita daga falon mahaifin nasa zuciyar sa na k'ullawa masa abinda ya kamata yayi a kan Asad domin cikar burin sa.

*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023.

©️ *Nana Haleema.*

*003.*

Asad da ya bar wajan mahaifin sa wajan mahaifiyar sa ya wuce duk da dare ya fara yi amma yasan bata yi bacci ba,kamar koda yaushe a hankali yake takawa ma'aikatan dare na ta kai gaisuwa wasu yayi murmushi wasu ya d'aga musu hannu wasu ma ya share dan baya son takura. Lokacin da ya shiga ya tarar da Aliyu a zaune a kan kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa ga ma'aikata a zagaye dashi ya bar su a tsaye bai sallame su ba yana aikin danna wayar sa.

Sallamar da yayi suka amsa duk suka duk'a suka gaishe shi ya d'aga musu hannu bai kalli inda Aliyu yake ba kai tsaye d'akin mahaifiyar sa ya shiga, Jim kad'an ya fito samun da yayi tana wanka ya zauna shima a kan kujerar da ta kasance suna zama in bata wajan bai magana ba. "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri bana jurewa tsayuwa kayi min wani hukuncin dan Allah" wani daga cikin ma'aikatan da suke zagaye dashi ya fad'a k'afar sa na rawa sosai.

Kallon sa Aliyu bai yi ba balle ya bashi amsa cigaba yake da abinda yake yi, gumi ne yake ketowa daga dukkan kafofin tsohon k'afafun sa sai rawa suke haka jikin sa idanun sa yayi ja sabida wahala, baya yayi zai fad'i Aliyu da yake danna waya yace, "in ka fad'i k'asa ka tabbata yau a tsaye zaka kwana." Dafa kujera yayi jikin sa na cigaba da rawa hawaye na zuba daga idanun sa.

Dukka sauran ma'aikatan jikin su yayi sanyi dan ya fisu shekaru a cikin su kowa yasan bashi da lafiyar k'afa balle ya iya tsayawa, Asad da ya ke jin komai yaso ya basar sabida ba shiri suke da Aliyu ba amma ganin abin yayi yawa ne sosai ya saka shi ya kalli tsohon yace, "Zauna!." A sama dukka suka ji maganar tasa Aliyu ya juyo ya kalle shi amma kamar ba shine yace na hankalin sa ma baya wajan su.

Tsohon ya kalli Asad suka had'a ido da idanu yayi masa alama da ya zauna, kallon Aliyu yayi yaga shi yake kallo ya kuma kallon Asad yaga shima shi yake kallo duk sai ya rud'e ya rasa abinda zaiyi, maganar wa zaibi a cikin su duk sai ya diririce. Aliyu yace, "ka sake ka zauna wallahi gobe sai na saka an zane k'afafun ka an ji musu ciwo yadda zaka jima baka taka ba."

Asad ya mik'e tsam ya k'araso inda tsohon yake ya kama kafad'un sa ya zaunar dashi a k'asa kafin ya kalli Aliyu su had'a idanu ko wanne fuska a d'aure zaiyi magana Asad ya d'aga masa hannu yace, "Bana son hayaniya pls." Kallon ma'aikatan Asad yayi da hannu ya musu alamun me suke a wajan, d'aya daga ciki yace, "muna jiran ya bamu umarnin abinda zamuyi ne ranka ya dad'e" ya fad'a cikin girmamawa yana kallon Asad.

Da hannu yayi musu alamun duk su fita daman sun gaji babu b'ata lokaci suka fita tsohon da ya zaunar ya mik'e ya tafi kamar zai fad'i yayi saurin rik'o hannun sa ya tsaya cak sannan ya sake shi tsohon ya duk'a yace, "Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kariya daga duk ka masu nufin ka da sharri, ya sanya ka zamo sarki a wannan gidan. Allah ya taimake ka ya biya maka dukkan buk'atun ka mai zuciyar alkhairi." Kai kawai ya d'aga masa ya fita da sha'awar rayuwar Asad duk da sarautar da izzar ta ratsa shi amma baya wulak'anta na k'asa dashi.

Kamar jira Aliyu yake su fita ya mik'e yana nuna Asad yace, "Kaga Asad ka fita daga rayuwata tun kafin ka tunzura ni nayi maka abinda har ka mutu baza ka manta dashi ba, me kake ji dashi har da zan kira ma'aikata ka saka su fita?, kawai rainin hankali kake ji dashi ko kuma tsabar raini ne?" Ya fad'a a fusace yana kallon sa.
Bai ce komai ba sai ma waje da ya samu ya zauna ya cigaba da danna wayar sa dan shi baya son hargagin Aliyu ko kad'an.

Hakan da yayi ba k'aramin sake harzuk'a Aliyu yayi ba ya koma gefe yana jan wuci yana k'arewa Asad kallo yana hasashen irin abinda ya kamata yayi masa wanda zai saka ya wuce takaicin da yake ji a zuciyar sa. Sallamar Hydar ta katse su Asad ne ya iya amsawa kawai banda Aliyu Hydar ya k'arasa ya xauna kusa da Asad kafin yace, "Our king how far."

Kai ya d'aga masa kawai baice komai ba ganin hakan shima sai ya share ya kalli Aliyu da yake wuce yace, "Ya dai bro?." Ji yayi kamar ya make Hydar ganin rainin hankalin da yayi masa, a gaban idanun sa ya kira Asad sarkin su sannan shi kuma ya kalle shi ya ce masa wai bro, k'wafa yayi yana jijjiga kansa dai-dai nan mahaifiyar su ta fito.

"Ya dai triples" ta fad'a tana kallon su ganin haka duk suka mik'e tsaye ta k'araso ta zauna a kan kujera suka zauna a kan carpet ta kalli Aliyu dashi bai zauna ba tace, "Aliyu wai me yake damun ka haka ne?."
"Ranki ya dad'e Asad shine yake damuna, har yana da ikon da zan kira ma'aikata zan saka su aiki ya ce su tafi?, me yake tak'ama dashi wanda bana tak'ama dashi?, ki ja masa kunne har ya harzuk'a ni nayi masa abinda bazai manta ba"

Kallon Asad tayi tace, "Ina ruwan ka da ma'aikatan sa? Asad Aliyu fa yayan kane why zaka dinga masa halaye irin wad'annan kamar ba jini ka ba?, meyasa bakwa shiri ne?." Asad ya kalli Mama yace, "wulak'anta su yake Mama, bana jure ganin ana wulaƙanta na k'asa dani."
"To ina ruwan ka dan na wulak'anta su?, kai na wulak'anta ko wani naka?, kai lallai mai zuciyar tausayi da Imani wa kafi a cikin mu!?" Aliyu ya fad'a da ihu yana kallon sa.
Chapter 6 · 0% Book details