← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 55

Sashe 11

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ta d'aga suna tafiya suna hira sama-sama har aka zo k'ofar gidan su Rauda ta shiga su kuma suka wuce. Da Rahma suka yi karo ta dawo daga siyar da abinci tana ganin Rauda tace, "yau kin samu sake har da tafiya gidan Yaya Ummi ko?." Bata iya bata amsa ba ta wuce d'akin Umma har lokacin k'irjin ta bugawa yake.

Umma da ta ga shigowar ta tana tsaye tana gyara labule tace, "ke kuma lafiya na ganki wujuga-wujuga?." Sai da ta zauna ta sauke numfashi ta kalli Khairi tace, "Khairi bani ruwa." Bata musa ba ta tashi ta kawo mata a kofi ta sha ta dire kofin tana ajiyar zuciya.

Umma tace, "lafiya?."
"Umma gidan sarki su Habiba suka jani na raka su."
"A ina kika gansu?."
"Lokacin da na dawo daga gidan Yaya Ummi suka ce nazo muje tunda ban tab'a shiga ba."
Khairi ta fashe da dariya tace, "to Anty shine kuma kike wannan hakkin?."

Umma taja tsaki tace, "ragwanta irin ta Rauda fa." Rauda tace, "Umma dokuna fa na gani zasu biyo ni na tsorata zan gudu naje na bangaje d'an sarki." Ta bud'e baki tace, "too! Amma dai ba'a yi miki komai ba ko?."
"Marina yayi Umma ya dinga ci min mutunci wai y'ar talakawa ya saka a min hukunci Allah ya kawo Habiba ta dinga yi masa kirari sannan ya hak'ura. Wallahi bashi da Imani bai san darajar d'an Adam ba na tsane shi sam bana son sa. Kuma wallahi badan ina jin tsoron doki ba babu abinda zai hana ban mayar masa da maganar da ya fad'a min ba."

Umma ta murmusa tace, "kedai tunda kin kub'uta Alhamdulillah, batun kina son sa ko bakya son sa ai bai tashi ba daman ke meye naki da zaki so shi? Ai sai kallo daga nesa. Naji ana labarin sa ance bashi da kirki sosai gwara da Allah yasa tsoron doki ya hana ki yi masa tsiwa ai."
"Umma sai ma Habiba na baki labarin sa, nima gashi naga zahiri baya da kirki ko kad'an."

Umma tace, "tunda dai lafiya Alhamdulillah, mari kuma Allah zai saka miki." Khalil da ya shigo yake cewa, "Anty d'azu Rahma tazo tana ta fad'a wai yau baki je siyar da abinci ba." Shiru tayi bata amsa ba ta kwanta a kan katifar Umma har lokacin k'irjin ta bugawa yake fuskar Aliyu na wulga mata a idanun ta.

           *☆☆☆*

         Mai martaba basu dawo ba sai dare har lokacin babu wanda yasan me suka tattauna a hanyar su, a gajiye Asad yake koda ya raka mahaifin nasa b'angaren sa nasu b'angaren yana shiga ya tarar da Suhail a falon shi kad'ai a zaune. Yana ganin sa ya mik'e tsaye yana fad'in, "Welcome back Prince." Kai kawai ya iya d'aga masa ya shiga cikin d'akin sa ganin hakan Suhail ya murmusa zuciyar sa fal farin ciki ya fita.

Wanka Asad yayi ya canja kaya zuwa marasa nauyi a gajiye yake yana so ya huta amma kiran wayar Mama ya hana shi sukuni tun suna hanya take waya hakan ya saka shi fita ya nufi b'angaren ta. A zaune ya tarar da ita daga ita sai Suhaima ya shiga da sallama. Kallon sa take har ya zauna kusa da k'afafun ta ta kalle shi tace, "kun sha hanya." Idanun sa ya lumshe ya bud'e alamun sosai ma kuwa.

"Me kuka tattauna a hanyar taku?." Kallon Mama yayi kafin ya buɗe baki yace, "Mama bamu yi komai ba."
"K'arya bata tsarin halayyar ka Asad ka fad'a min me kuka tattauna." Juya idanun sa yayi kawai baice komai ba tace, "kafi kowa sanin bana jure wannan shirun naka kayi min magana kun tattauna game da sarautar ka?."

          Kamar zaiyi kuka ya kalle ta ya girgiza kai alamun a'a,  ta fusata tace, "magana zakayi min malam!, kun tattauna ko a'a?."
"Mama bamu tattauna akan komai ba, inda munyi mahaifiyata tasan bazan b'oye mata ba." abinda ya iya fad'a kenan yana dafe jijiyoyin kansa da suke harbawa a gajiye yake sosai ga maganar Mama tana sake d'ora masa damuwa.

          Suhaima da take kallon Mama kamar zata yiwa Yayan ta kuka tasan ya gaji gashi baya son magana ga shi sai tsawa take masa kamar ba ita ba. kallon Suhaima tayi tace, "kawo masa abinci yaci." Mik'ewa tayi ba jimawa ta kawo masa bai musu ba ya karb'a yaci abinda zaici ya bar ragowar ta kalle shi tace, "naji na k'yale ka yanzu amma gobe zaka fad'a min abinda kuka tattauna. Sannan nifa ban amince da Suhail ba mahaifin sa munafuki ne ka kula dashi bana so na gan ku tare dan komai zai iya faruwa, bana son ko meye a duniyar nan da zai kawo tangard'a a cikin sarautar da zata dawo hannun ka."

Rausayar da kai yayi a hankali yace, "Sarauta again!."
"Ehh, itace burina kuma matuk'ar ina raye sai kayi, kaje ka nutsu gobe zamu cigaba da tattaunawa."

Kallon ta yayi ta wara idanun ta a cikin nasa ya sauke nasa k'asa tace, "Asad ko kai baka isa kace baza kayi mulkin nan ba matuk'ar na isa da kai, in kaga baka yi wannan sarautar ba ka tabbatar bana raye ne." Kai ya jijjaga kawai yayi mata sallama mik'e ya kalli Suhaima da take kallon sa ya d'auke kansa ya fita.

            Suhaima ma bata ce komai ba ta mik'e ta shige ciki itama Maman mik'ewa tayi ta shirya tsaf sai b'angaren mai martaba. Lokacin da ta isa yana zaune a gefe guda yana duba littafai kamar koda yaushe ta shiga da sallama ya amsa mata ta k'arasa ta zauna tace, "kun sha hanya, barka da dawowa."
"Barkan ki, ya daren?."
"Alhamdulillah, ya k'arfin jikin naka?."
"Mun gode Allah."
Shiru ya biyo baya babu mai magana kafin yace, "Aliyu baya gidan nan ko?."

"Ban gan shi ba." Ya ajjiye littafin hannun sa yace, "ban san meyasa Aliyu yake halayya irin wannan ba, meye ribar abinda yake?, shi ko gudun zagi ma baya yi?. Ace yana daga cikin manyan y'ay'a na ace shine kuma wanda yafi kowa gurb'acewa?." Ajiyar zuciya tayi tace, "ban san meyasa Aliyu yake haka ba, kuma takawa kafi kowa sanin yadda aka sha wahala lokacin suna yara wajan kare su daga mugayen sihirin da ake musu. ni nafi tunanin akwai sihiri a jikin sa."
"Koda yaushe ke Aliyu baya laifi asiri ne a jikin sa bakya duba yanayin dabi'un sa. Meyasa Asad shi baya yin  abinda yake?, wanda suka yi asirin Aliyu kawai suka tsana?."

Shiru tayi bata amsa ba ya kuma cewa, "Dabi'un Aliyu suna daga cikin abinda yake sake tayar min da hankali, da kunya ace d'an da na haifa a cikina shine yake irin wad'annan halayen mara sa kyau da dad'in ji, kuma a haka yake burin kasancewa sarki a garin nan."
"To ya za'ayi sai hak'uri ai." Shiru ya biyo baya dan ita dai bata san maganar shiyasa ta katse ta kafin tace, "ya batun ajjiye sarautar taka?."

"Na jinkirta zuwa nan da wani lokaci, ina so komai ya zama dai-dai kar a bar baya da k'ura. In kuma kafin lokacin na bar duniya shikenan." Nan ma shiru tayi bata ce komai ba zuciyar ta na cigaba da fad'a mata k'arya da gaskiya a kan komai da ya shafi lamarin gidan sarautar da take ciki.

                Washe gari.

*☆☆☆*
             Rauda ko aikin gida bata samu ta tashi tayi ba duk da daman gyaran gidan Rahma ne ciwon kai ya mata mugun kamu dak'yar take iya juya kanta, har su Khairi suka tafi makaranta bata sani ba tana bacci sai goma na safe ta tashi tayi mamakin baccin dan bata saba jimawa haka ba. Sosai taji dad'in ciwon kan tayi wanka ta karya ta zauna a kusa da mahaifiyar ta suna hira. Har akayi Azahar babu inda taje tana kusa da ita duk da tana so ta fita taje gidan da take karb'o sarin alawar madara amma ta kasa fita.

"Ke Rauda! Ke Rauda!!, maza fito" Baba ya fad'a daga waje. Mik'ewa tayi ta fito ta ganshi da kular da ta saba fita siyar da abinci tace, "Baba gani." Kallon ta yayi yace, "To maza a tafi, na dubu biyu da dari uku ne ki lisaafa dakyau in zaki bawa mutane."
Kallon sa take yi da mamaki a fuskar ta ganin hakan ya saka shi yace, "Wai ke a tunanin ki dan jiya baki fita ba yau ma baza ki fita ba?, yo ko saurayin naki ya kawo min abinda yafi keke ai siyar da abinci yanzu kuka fara Rauda. Maza d'auki ki tafi bana son b'ata lokaci."

Khairi da ta dawo daga makaranta ta fito daga d'aki tace, "Baba kanta ciwo yake." Ya harare ta yace, "ta sha magani kafin ta k'arasa zai warke, d'auko hijjabi ki maza ki wuce ki tafi." Jikin ta a sanyaye ta shiga suka had'a idanu da mahaifiyar ta da take jin su bata ce komai ba ta d'auko hijjjabin ta fito ta saka takalmi.

"Kina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki in baki hanzarta ba Rahma ta dawo ta barki wallahi ranki ne zai b'aci. In bakya son zuwa ai jiya saurayin ki ya baki kud'i d'auko su yanzu ki siye abincin ki bani kud'in kiga in baki zauna a gida ba." Bata ce kanzil ba ta sukunya ta d'auki kular ta fita daga gidan gabanta yana fad'uwa.
Tsaki yayi ya fice babu wacce ta tanka cikin matan nasa kowa yasan halin sa shiyasa ko wacce taja bakin ta ta tsuke.

        Ko a can inda suke zama suna siyar da abincin Rauda ranar gabad'aya bata da walwala kana ganin ta kasan bata da lafiya duk da daman ba magana take da mutane ba, tana nan zaune Khairi tazo wajan ta tace, "Anty kije gida ni zan cigaba da siyarwa." Girgiza kai tayi tana kallon ta tace, "ya akayi baki je islamiyya ba?."
"Yau alhamis ai babu shiyasa ban je ba."
"Ki koma gida Khairi nima yanzu zan tawo."
Chapter 11 · 0% Book details