← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 55

Sashe 16

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga idanun sa ya sauka a cikin na Rauda da take kallon wanda ya shigo, bai d'auke idanun sa daga cikin nata ba ganin yadda idanun ta sukayi ja duk da bai san su a yadda suke a baya ba amma yadda ya gan su ya san sun canja.  Kwarjini da fad'uwar gaban da ta ziyarci k'irjin ta ya saka ta janye idanun ta ta saukar k'asa duk da tsananin azabar da take ciki.

Babu kowa a d'akin sai ita kad'ai ya k'araso yana yatsine fuska sabida kansa ba k'aramin sarawa yake yi ba, ko takawa yayi sai yaji takun har kwakwalwa sa. Kallon ta yake yi ganin yadda take juya kanta kana gani kasan tana cikin azaba jikin ta har rawa yake ga k'afar tata a d'aure goshin ta manne da flasta, k'arewa fuskar ta kallo yake a karon farko k'irjin sa ya cigaba da bugawa yayi saurin d'auke fuskar sa yana kallon gefe guda.

Bud'e k'ofar akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Dr ne da kuma mahaifin ta ganin sa ya saka Dr k'araso yace, "barka da zuwa." Idanun sa ya lumshe ya bud'e kafin ya kalli Baba kafin yayi magana Baba yace, "Barka da safiya, da fatan an tashi lafiya."
"Ya mai jiki?" Ya furta a nutse yana kallon Baba.

"Mai jiki da sauk'i" Baba ya bashi amsa jikin sa har rawa yake yi. Hydar ya kalli Dr baiyi magana ba hakan ya sake yace, "Komai zai tafi dai-dai in sha Allah." Kai kawai ya girgiza ya juya zai fita cikin takun isa sai kuma ya tsaya cak ya juyo yana kallon Baba kafin yace, "ba wani damuwa?."
Sai kuwa Baba ya gyara tsayuwa yace, "To Alhaji kasan lamarin abubuwan sai a hankali, ga gida ba abinci ga kud'in motar zuwa asibiti ga kuma......." hannu Hydar ya d'aga kawai baice komai ba ya saka hannun a aljihu ya d'auko d'aurin dari biyar guda biyu ya mik'awa Baba ya k'araso jikin sa har yana rawa ya karb'a baice komai ba bai kuma bari Baban yace komai ba ya fita.

Baba yabi kud'in da kallo yayi murmushi yana shafa fuskar sa yace, "To ke Rauda ai sai ayi fatan ki ta zama a asibiti wannan abin arzuk'i haka?, tunda nake na d'auka zan rik'e kud'i manya haka nawa na kaina ni kad'ai? Ai ban tab'a ba sai silar kwanciyar nan taki. Yo ba sai nayi ta addu'a kita zama ba indai irin wannan zasu zo hannu."

Rauda kallon Baba take yi duk da ciwon da take ciki hakan bai hana jin takaici da bak'in ciki a zuciyar ta ba, ji ta kud'i ma yake bata lafiyar ta ba gashi da ya shigo ko ya jiki bai mata ba dan ta fahimci shine ya buge ta.
Hydar dak'yar ya iya zuwa office d'in Dr ya zauna kansa yana juyawa a ya saka duka hannayen sa biyun ya dafe kansa, ganin hakan hankalin Dr ya tashi dan masomin tashin ciwon Hydar kenan hakan ya saka shi ya rud'e yace, "Prince lafiya? Me yake damun ka?."

Kansa yake nuna masa jikin sa har rawa yake hankalin Dr ya tashi ya kalle shi yace, "Prince kana buk'atar drip." Kai ya girgiza alamun a'a kafin kuma ya ja dogon numfashi jin yadda kansa yayi mugun sarawa daga nan idanun sa duhu ya mamaye su amma duk da haka yak'i kulle idanun nasa.
"Prince! Prince!! Kana jina?, Prince!!!" Dr ya fad'a hankali a tashe amma lokacin idanun Hydar ya rufe ruf yana zaune idanun sa a kulle jikin sa ya saki duka.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abinda Dr yake maimaitawa kenan jikin sa na mugun rawa ya bud'e k'ofar Office d'in sa yana fad'in, "Nurse!, Ashiir kana ina?!" Ya fad'a da k'arfin gaske wanda yake kira ya tawo a guje. "Zo ka taimaka min" ya fad'a yana komawa ciki suka shiga tare suka d'aga Hydar da jikin sa yake a sake kamar gawa  suka d'ora shi akan gado Dr hankalin sa tashe suka tura gadon Hydar zuwa babban d'aki na musamman.

Ta underground aka shiga babu wanda zaice akwai wani d'aki ko hanya a wajan aka shiga da Hydar aka jona masa ruwa na'urori sai da ya tabbatar yayi masa abinda ya kamata sannan ya fito da sauri yana kiran wayar Mama amma bata d'aukar wayar.

Dafe kansa yayi hannun na rawa ya rika number Asad kamar yadda yayi zato bazai d'auka ba bai kuma d'auka d'in ba, "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta yana danna layin Aliyu shima bai d'auka ba har kira biyu.
Suhaima ya kira na farko bata d'auka ba sai a na biyun yana ganin ta d'auka da sauri yace, "Princess where are you?."
"At home."
"Ina Mama?."
"Lafiya?."
"Ki sanar da ita Hydar yazo nan wajan yarinyar da ya kad'e kuma ciwon sa ya tashi yanzu haka yana kwance."

      "What!" Ta fad'a a firgice tana dirowa daga kan gado ta fito daga d'akin ta cikin sauri, bata yi tafiya mai nisa ba ta iso babban falon mahaifiyar tata bata same ta a shi ba ta nufi ciki ta ganta a tsaye tana amsa waya, "Mama ciwon Yaya Hydar ya tashi" ta fad'a a firgice bata jira ta gama wayar ba ma. Ba shiri ta sauke wayar daga kunnen ta ta zaro idsnu tace, "me kika ce? Ciwon Hydar? Yana ina?."
"Dr Yasir ne ya kira ni yake sanar dani yanzu haka ma yana asibiti."
"Oh my god!" Mama ta fad'a tana yin ciki da sauri.

Ita da sauri ta koma ta canja kayan jikinta da sauri ta dawo ta tarar Mama har ta fita tabi bayan ta da saurin gaske, a mota ta samu Mama da sauri ta shiga kusa da ita aka ja motar aka fita da motar da saurin gaske.

Hajiya tana tsaye jakadiyar ta ta shigo a guje tana haki ta zube a gaban ta, da sauri ta juyo ta kalle ts tana fad'in, "ke kuma lafiya zaki fad'o min ko sallama babu."
"Tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ki."
"Lafiya?."
"Wato ranki ya dad'e ciwon yarima Hydar ne ya tashi yanzu zancen da nake miki gimbiya ta tafi asibiti wajan sa." Waje Hajiya ta samu ta zauna tace, "yanzu kenan abin ya faru?."
"Yanzun nan ranki ya dad'e dan yanzu ta fita a gigice da ta shirya tafiya Kano amma a halin yanzu tafiyar ta watse."

Kyakykyawan murmushi tayi tana cize baki tace, "jeki."
"Na gode ranki ya dad'e, ki huta lafiya" ta fad'a tana fita jiki na rawa ta bita da kallo tana murmushi.

"Master planer!" Ta furta a bayyane tana murmushi ganin duk abinda ta tsara ya tafi nan take taji farin ciki yana mamaye mata zuciyar ta. Y'arta Khaleesat sa'ar Suhaima ce ta shigo ta kalle ta itama ita take kallo tace, "Khaleesat kin san me nake so dake?." Kai ta girgiza kai Hajiya tace, "Jeki ki samo min zogale yanzun nan."
Wara idanu tayi tace, "zogale? Hajiya a ina zan samo zogale yanzu?."
Tsaki taja ta shige ciki ita ma tabi bayan ta da sauri.

B'angaren Mama a gigice suka isa asibitin b'angaren da aka ajjiye shi shiru wajan babu motsin komai tsittt ko tsuntsu baya bi ta wajan ta shiga inda Hydar yake kwance, yana kwance sanb'al kamar koda yaushe ko ina na jikin sa baya motsi an jona masa na'ura a kan sa idanun sa a kulle ko wanne lokaci. Kallon Dr tayi ta kalli Suhaima da take gefen ta ta dawo da kallon ta ga Dr tace, "me yazo yi asibitin nan?."
"Ranki ya dad'e yazo duba yarinyar da ya buge ne."
"Yarinyar da ya buge? Kana so kace min a wannan asibitin ya ajjiye y'ar talakawar da ya kad'e?."

Suhaima tace, "Mama muje waje kin san ba'a yi masa hayaniya." Ba musu duka suka fito ta kalli Dr tace, "Kai nake sauraro."
"A nan ya ajjiye ta ranki ya dad'e, yau d'in ma yazo duba ta ne."
"Ita wacece da zai zo duba ta da safe ko wajena bai shiga na gansa ba?, me take dashi?."

Dr yace, "Bata da komai ranki ya dad'e." A fusace tace, "a kan me za'a ajjiye ta a nan? Meya zo yi wajan ta ko wajena bai shiga ba?, me yake nufi da yarinyar nan?." Shiru Dr yayi ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba tace, "akan ta Hydar ya kwanta rashin lafiya, yasan ba'a son ya cika zirga-zirga mussmman da safe amma sabida ita yake fitowa har hakan ya kai shi ga kwanciya, y'ar gidan uban wacece?."

Dr yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ba y'ar kowa bace hasalima iyayen ta talakawa ne." Dogon tsaki taja takaici da bak'in ciki na damalmale mata zuciya tace, "Ayi gaggawar sallamar su daga asibitin nan su koma asibitin gwamnati suje can su k'arata, bazai yu yana kwance a nan itama tana nan ba matsayin su ba d'aya bane ka gane ko?." Kai ya girgiza alamun eh cikin girmamawa tace, "a shirya komai zai tafi da Hydar gida" ta fad'a tana niyar komawa d'akin Suhaima tace, "But Mama zaman sa a nan zaifi samu kulawar da ake nema." Hararar ta tayi hakan ya saka ta yin shiru bata ce komai ba domin an gama magana ta shiga ciki.

Suhaima ta kalli Dr tace, "please Dr ka bar yarinyar ta samu sauk'i in yaso sai ku sallame ta, a bata kulawar da ya kamata please" tana gama fad'a tabi bayan maman ta shima ya bisu da kallo. K'irji ya dafe yana fad'in, "Allah ya fidda ni lafiya" ya Fad'a shima yana bin bayan ta.

Yana shiga ta kalle shi tace, "a had'a komai zamu tafi dashi gida." Kai ya girgiza da sauri ya fita aka had'a mota nan da nan aka turo gadon da yake kai aka saka shi a mota ita da Suhaima suka shiga bayan wata motar ta kalli Dr tace, "a tabbatar yarinyar nan ta bar asibitin nan."
"In Allah ya amince ranki ya dad'e." Daga haka aka ja motar aka tafi.
Chapter 16 · 0% Book details