← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 55

Sashe 52

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice Mama ta kalle shi tace, "A lalata shi ta k'arfi, a saka k'arfin da yafi nasu k'arfin a tarwatsa shibana son hakan ta kasance ne ko a mafarki." Malam ya jinjina kai kafin Mum tace, "A yiwa yarinyar asirin da zata ji ta tsane shi gabad'aya taji bata son ganin sa ko kad'an, kaga koda tayi niyar amincewa dashi zata fasa." Malam ya sake dubawa kana yace, "Yiwa yarinyar aiki ba abu bane mai sauk'i, tana da rik'o da ibada fiye da tunanin ki Hajiya Sadiya." Mama ta dafe kai cikin takaici tana cizan yatsa zuciyar ta na tafasa sabida b'acin rai jikin ta har zafi ya d'auka kamar mai zazzaɓi, bata k'aunar talaka ya rage ta balle kuma y'ay'an ta.

Mum tace, "A kashe ta ko a haukata ta!." Malam ya yi murmushi yace, "Kar ayi gaggawa ranki ya dad'e, shawara a nan aje a same ta a tsoratar da ita har a cusa mata tsanar auren tak'i amsawa zata aure shi, a fitar mata da sha'awar auren jinin sarauta a zuciyar ta. A ganina wannan itace kawai hanya mai sauk'i in tak'i sai a dauki mataki." Mum tace, "Kenan mune zamu same ta?."
"Kwarai ku da kanku zaku same ta in akayi sa'a hakan zaiyi aiki, domin indai ba ita tace bata so ba Asad bazai fasa auren ta ba haka mai martaba bazai fasa bashi ita ba."

Mama ta sauke numfashi tace, "ya batun sarautar sa?." Malam ya bincika kana yace, "Tana nan, kamar yadda na sha fad'a miki shine zai mulki katagum har gobe maganar haka take; amma kamar koda yaushe akwai qalubale manya ma wanda suka fi na baya yawa. Na farko maganar auren nan zata sake dagula komai, na biyu wad'annan wanda nake fad'a miki suna aiki a kansa sun sake zage dantse sun k'aro makaman yak'in yak'ar ku, na uku suna gab da yin nasara a kanki da kuma kan Asad d'in." Mama ta sauke ajiyar kana ta sassauta murya tace, "ya batun tsarin jikin sa?."

"Ranki ya dad'e komai lafiya yana k'ok'ari wajan ibada da rok'on Allah shiyasa suka kasa nasara akan sa har yanzu." Kai ta girgiza kafin ta mik'e tsaye tace, "Zamuyi waya, muje" ta fad'a tana yin gaba tare da sakin niqab d'in fuskar ta. Mum ta kalle shi bayan ta tashi tace, "Akwai maganar da zamuyi ma tattauna a waya" ta fad'a tana fita daga d'akin tabi bayan Mama da sauri. Suna shiga motar Mama ta kalle Mum tace, "muje gidan su yarinyar."

Zaro idanu Mum tayi tace, "muje muyi me? Kin manta rashin kunyar ta dana baki labari?; marina fa tayi."
"Zamu je mu gyara komai ne yanzu."
"Kamar ya mu gyara Fulani? Kema in ta maren ki fa?."
"Ko uban uban ubanta bai isa ya tab'ani ba balle ita; dalilin da Malam ya fad'a shine zai kai mu wajan ta."
"Amma fulani......?" Dakatar da ita Mama tayi ta hanyar cewa, "Muje kawai. Zan nuna miki gidan da suka koma."

Shiru Mum tayi zuciyar ta a wuya take tuk'in har suka zo k'ofar gidan su Rauda Mama ta fita daga motar tana kallon gidan ta tabbatar nan ne inda aka binciko mata ta nufi zuwa cikin gidan, juyowa tayi taga Mum bata fito ba ganin tana kallon ta ya saka ta fitowa suka shiga cikin gidan.

K'ofa biyu suka gani suka tsaya suna kallon k'ofar cikin tunanin waccw zasu bi a ciki, bud'e d'aya akayi aka fito hakan ya saka suka kalli wacce ta bud'e k'ofar ta kalle su tace, "Bayin Allah daga ina?" Inna ta fad'a tana kallon su. Mum ta kawar da kanta gefe da alama baza ta bada amsa hakan ya saka Mama tace, "Muna neman wajan su Rauda."

"Gashi nan" ta fad'a tana nuna musu d'aya k'ofar suka wuce ba tare da sun kuma kallon ta ba. Da sallama suka bud'e k'ofar sai gasu a falo Rauda na zaune ita da Umma da kuma Yaya Ummi suka amsa suna kallon su, ido Rauda suka had'a da Mum ta bita da kallo kana tace, "tofa kice shugabar y'an daba ce da kanta ta kuma dawowa, to yau kuma da me kika zo mana...? zauna ki bamu labari" ta fad'a tana kallon Mum cikin sigar rashin mutunci.

Mama ta zauna ta d'age nikaq d'in fuskar ta ta kalli Umma tace, "Sannu ya jikin?." Umma tace, "lafiya lau Alhamdulillah. Amma ban sanki ba." Mama ta murmusa tace, "Sunana Fulani Rabi'atu mata a wajan sarki katagum ya a wajan sarkin Kano, jika wajan sarkin Kano, uwa a wajan sarkin Katagum mai jiran gado" ta fad'a tana kallon su. Yaya Ummi tace, "Allah sarki! To sannu." Mama ta kalli Rauda tace, "wajan ki nazo." Rauda da mamaki ta kalle ta tace, "gani ai kin ganni."

Mama tazo wuya jin amsar da ta bata amma ta jure tace, "d'ana Asad ya furta kalmar so a gare ki a lokacin da ban shiryawa hakan ba, ya nuna ke yake yi kuma na riga da nayi masa mata tun ba yanzu ba, gidan sarauta gida ne na rikita-rikita kanki bazai d'auki abinda yake faruwa a cikin sa ba koda an baki labari, duk inda kike tunanin abun ya wuce haka gwara ki zauna a gefe hakan zaifi miki alkhairi. Nasan halin mahaifin sa tunda yace amsar ki ake jira ita ake jira indai kika amsa zance ya k'are in kuma kika yi akasin haka za'a fasa shiyasa nazo na shawarce ki akan karki kai kanki ga halaka matsayin da kike k'okarin takawa yafi k'arfin ki akwai mata sosai a gaban ki." Kallon Umma tayi kana tace, "Ke uwa ce baza kiso ki rasa d'iyar ki ba ki bata shawarar kar ta amsa batun Asad domin kuwa tana niyar shiga wuta ne da k'afar ta."

Umma tace, "banda abin ki kinji ance y'ar mu zata auri d'anki ne?." Mama ta tab'e baki tace, "ko d'aya nasan baza tak'i tayin ba ai shiyasa nake fad'a mata gaskiya."
"Ai kuwa sai muce a kai kasuwa domin kuwa tana da wanda yafi Asad d'in" Yaya Ummi ta fad'a tana kallon ta. Kyakykyawan murmushi Mama tayi tace, "tana da daidai ita dai amma bawai wanda yafi Asad ba ko yarinya..? Ta samawa kanta lafiya da kuma zaman lafiya."

Rauda da take gefe tace, "in kuma na amince masa fa?." Mama ta kalle ta tace, "abinda ma bazai yu ba kenan, keda shi sai dai taimako amma yafi k'arfin ya zama mijin ki har Allah ya tashi duniya, Rauda sunan ki ko?" Ta fad'a tana kallon ta cikin k'ask'anci da rainin hankali Rauda tayi dariya tace, "kodai nafi k'arfin sa ba tunda shine yake jiran amsa ta bani nake jiran tasa ba, shi ya gani ya mato yace yana so har kika kasa dakatar dashi kinga kenan nice nafi k'arfin sa bashi yafi k'arfi na ba. Ki rike d'anki daman bana sha'awar auren kuramen maza ni."

"Ke yarinya ki iya bakin ki! Ki san da wacce kike magana" Mum ta fad'a a fusace tana kallon ta Rauda tace, "in kuma nak'i fa akwai abinda za'ayi min ne?." Mama tace, "Naga alama kanki yana rawa sosai kina ji da y'an matanci, ki saita harshen ki tun kafin ya kai ki ya baro ki" ta fad'a tana nuna ta da yatsa. Umma tace, "Rauda ya isa haka." Mama tace, "ya kamata dai kija mata kunne ta san da wacce take magana."
Rauda tace, "Ke kika tako k'afar ki kika zo har inda muke dan haka baki isa ki fad'a mana maganar da batayi mana ba kuma nayi miki shiru ba."

Mama tayi k'wafa tace, "Ba wannan ne a gabana ba abinda na fad'a miki shi ya kamata kiyi, maganar auren Asad ki d'auka a mafarki kika tab'a ji ba a gaske ba" ta fad'a a kausashe. Rauda ta tab'e baki tace, "Umarni ne ko shawara?."
"Umarni ne!" Ta fad'a a fusace tana kallon ta.
"Dalili?" Rauda ta fad'a tana binta da kallon raini. Mama tace, "ke banzo wajan nan dan na fad'a ki fad'a ba, ina so kisan badan Jan kunnen da zan miki ba uban ki ma bai isa na fad'a ya fada ba balle ke y'ar k'aramar tsakuwa. naga alama baza kiji maganar a nutse ba sai an fad'a miki da yaren da talaka yafi ganewa wato duka. Ki samarwa kanki lafiya ki bar Asad in baso kike wani abun ya same ki ba."

Rauda tace, "babu abinda zai same ni sai abinda Allah ya nufa. Sannan babu wanda ya isa ya saka ni yin abinda banyi niya ba, in naga dama kuma zan iya cewa ina sonsa na aure shi kodan naga yadda zaki koma a lokacin."

A fusace Mama ta mik'e tace, "Kee! Kar ki sake hasashen wannan ranar a rayuwar ki domin baza tazo ba har abada. Ke wacece da zaki zama matar d'an sarki jikan sarki kuma sarkin gobe? Wacece ke? Banza kike, bak'a, mummuna, matsiyaciya, gurguwa mai tallan abinci a titi. Ke ko a mafarki akace zaki zama matar sa sai ki amince?."
Murmushin rainin hankali Rauda tayi tace, "Da alama sirikata kina wasa da ikon Allah kinga ta inda muka samu banbanci kenan ni nasan duk wahalar abu a wajan Allah mai sauk'i ne." ta fad'a tana kallon ta itama tana kallon ta.

Mum tace, "kul kar ki sake kiran ta da wnanan sunan bai dace a bakin mace irin ki ba, ki sani akwai matan da suka amsa sunan su mata sama da d'ari da suke son su furta wannan suna amma yafi k'arfin su." Rauda tace, "ba tsoron ta kar na amsawa Asad zan sa aure ba? To ina so ku sani da zarar lokacin da aka d'iba yayi zan tabbatarwa da mai martaba ina son Asad kuma zan aure shi kodan naga ya zakuyi a lokacin da Bak'a, mummuna, gurguwa, y'ar talaka, mai tallan abinci ta zama matar sarki Asad; kuma sirikar y'ar sarkin Kano babar sarkin jibi. Kunga sai ku d'auki bindiga ku harbe kan ku" ta fad'a tana kallon su one by one.
Chapter 52 · 0% Book details