← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 55

Sashe 54

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma da take zaune tace, "tun a yanzu ya fara bayyana kansa dan mahaifiyar yaron bata jima da fita daga gidan nan ba tayi b'adda kama ta shigo tana yi mata gargad'! akan auren d'anta, har da ikirarin in ta aure shi sai ta b'atar da ita daga duniya, ina dalili d'an sarki ai ba d'an wani annabin bane da za'a so a aure shi. Kuma shi yaron ita dashi bai ma ce yana son ta balle yace zai aure ta, haka zasuyi zaman auren?." Kawu Lawan yace, "sai a bar maganar in mai martaban ya nemi jin ra'ayin ta ace bata amince ba ai ba dukan mu za'ayi ba."

Baba yace, "A'a bafa za'ayi haka ba zata amince ma in sha Allah, meyasa kuke haka ne ku? Alkhairi ya biyo mu kuna k'okarin saka mu guje masa?. Ni ina goyan bayan auren d'ari bisa d'ari kuma in sha Allah sai ta aure shi." Umma tayi murmushi tace, "Daman Malam ai baza ka k'i ba kai." Kawu Badamasi yace, "Muma bamu k'i ba muna fatan abinda yafi alkhairi Allah ya zab'a, in shine alkhairin Allah ya tabbatar da arzuk'i a gidan wasu ai gwara a gidan ku, kuma kowa yana so yaga nasa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, abin alfaharin mu ne gabad'aya ace Rauda ta auri d'an sarki dan kaf dangin mu ba'a tab'a ba sai a kanta. In kuma babu alkhairi Allah ya watsa lamarin waje duk kud'i ko mulki bazai saka mu kaita inda zamu zo muna dana sani ba."

Baba yace, "Da alkhairi ma in Allah ya amince." Shiru sukayi dukkan su kafin suyi sallama su wuce. Baya fitar su Yaya Ummi ta kalli Rauda tace, "to kinji yanzu babu batun maganar Anas sai ki dawo da hankalin ki kan Asad." Rauda ta murmusa tace, "Wallahi Yaya sai nake jin zuciyata tayi min nauyi da akace ya fasa aurena, ashe shiyasa ya kasa nema na a waya."

Umma tace, "Ni kaina zuciyata babu dad'i Rauda balle ke, Anas ya cancanci aso shi kodan soyayyar da ya nuna miki ashe Allah bai rubuta zai mallake ki matsayin matar sa ba, Allah sarki! Allah ya zab'a masa abinda yafi alkhairi ya basu zaman lafiya shida wacce aka zab'a masa." Rauda tayi shiru tana jin babu dad'i a zuciyar ta.

*☆☆*

Gudu yake sosai a motar yadda Mama ta kira shi a wayar tana kuka ta d'aga masa hankali sosai hakan ya saka yake gudu kamar zai tashi sama burin sa yaje yaji kiran da take masa. Ko gama faka motar baiyi ba ya fita da sauri zuwa wajan ta yana shiga falon farko bata nan ya shiga ciki ya tarar da ita ita da Mum a zaune sunyi jugum-jugum kamar an musu rasuwa. Hankalin sa tashe yace, "Mama lafiya?." Kallon sa tayi da jajayen idanun sa ta yafito shi da hannu ya k'arasa kusa da ita ya zauna ta rik'e hannun sa tace, "Asad dan Allah ka janye batun maganar auren yarinyar nan, bata da tarbiyya ko kad'an bata da kirki."

Juya idanun sa yayi ya rik'e hannun ta da yake cikin nasa yace, "meya faru?." Mum da take gefe tace, "zuwa gidan su yarinyar mukayi da niyar ta rok'e ta kar ta amince maka; yarinyar ta dinga zazzaga masa rashin kunya har da k'okarin dukan mahaifiyar ka tana fad'in bata ga wanda ya isa ya raba ku ba. Bata da tarbiyya gabad'aya yarinyar in kaji cin mutuncin da tayi mata baza ka d'auka tana da hankali bama."

Asad da yake jinsu yayi shiru kawai baice komai ba jin yayi shiru ya saka Mama tace, "Asad dan Allah ka fasa auren ta, ka aure ta zan iya mutuwa dan zuciya ta zata iya fashewa ko wanne lokaci." Asad sanyaye yace, "Mamana bazata mutu ba, Allah ya wuci zuciyar ki, I'm sorry" ya furta a hankali yana kallon ta.

"Ka fasa d'in?" Ta tambaya tana kallon idanun sa. Kasa magana yayi dan bai san me zaice mata ba hakan ya saka shi yin shiru kana yace, "zan fad'a sanar da mamana in anjima, ina zuwa yanzu" ya fad'a yana tashi ya fita daga falon zuciyar sa duk babu dad'i.

Mum ta kalli Mama tace, "bafa zai amince ba an riga an juyar masa da tunani daga kanki, in badan haka ba Asad ne kike rok'on abu a wajan sa amma yake cewa ki jira ya dawo anjima, yaron da kince zo kayi yake cewa to in ba asiri ba meye?." Mama sabida abinda take ji bata ce komai ba amma ta amince da asiri aka yi masa dan ga zahiri ta gani.

Mum tace, "Ai hanya ta biyu dole zamu bi, ko a kashe yarinyar, ko a haukata ta. Cikin biyu zamuyi guda d'aya." Mama tace, "Kisan yafi haukan, ta b'ace bat daga duniyar yafi ace tana cikin duniyar hankali ne babu. Kije ayi duk abinda za'ayi aga bayan ta tsakanin yau zuwa gobe kin san bana son b'ata lokaci, sai dai bana so a samu matsala, bana so sunana na ya fito, bana so ayi mata kisan da za'a fahimci kashe ta akayi." Mum ta tashi tsaye tace, "Baki da matsala Fulani wannan ki d'auka an gama." Ta d'auki jakar ta da makullin mota kana tace, "Sai kin jini" tana fad'a ta fice daga cikin falon.

Asad da ya fita daga wajan Mama daga gidan ya fice gabad'aya dan bazai iya jure abinda yake ji ba ya hau mota ya tafi gidan da ya saba keb'e kansa, yana zaune a falon gidan ya zubawa waje d'aya ido yana kallo zuciyar sa na bugawa da gudu ko ya ya kulle idanun sa Rauda yake gani. 'Ina sonta sosai, amma nafi son Mama da ita bazan iya ganin Mama cikin wani hali sabida ita ba, zan cire komai a raina.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan gabad'aya ransa a jagule yake.

Motsi yaji a bayan sa ya juya suka had'a ido da Hydar ya k'araso kusa dashi ya zauna yana kallon sa kana yace, "Deaf indai zaka biyewa Mama baza ka tab'a samun farin ciki ba." Da sauri Asad ya kalle shi Hydar yace, "yeah sabida duk hanyar da ka biyo ta neman farin cikin ka sai Mama ta toshe ta, ka bar abubuwa da yawa sabida ita ya kamata zuwa yanzu kaima ka samu abinda kake so a karona farko, farin cikin ta kawai ta sani banda naka."
"She's my mother tana da ikon zab'a min duk abinda take so, bana son rasa ta a cikin rayuwata" Asad ya fad'a a raunace yana kallon k'asa.

"Even me i love her because itace ta haife mu bamu da wata kamar ta a kaf dunitar nan, but tana son kanta da yawa ne Asad musamman akan abinda ya shafe ka, tana tauye maka hakki ka always abinda take so kake yi meyasa wannan baza ta baka dama ba?."
"I can leave anythings because of her" ya sake furtawa yana lumshe idanun sa.

"I know Asad but ka aikata hakan zaka cutar da kanka ne fiye da lokacin baya, Sabida you loves Rauda so much itace ta farko da ka fara yiwa wannan son, lokaci d'aya Allah ya d'ora maka k'aunar ta a zuciyar ka cire ta ba abu bane mai sauk'i. Try to understand soyayya ba irin aiki da mukaman da ta saka ka bari a baya bane, wannan rayuwar kace domin soyayyar ta ta riga ta kama ka barin ta illa ce a gare ka." Asad ya furzar da iska ya kalli Hydar da idanun sa yace, "Meye mafita?."
"Addu'a. Nasan kana yi but ka k'ara a kan wacce kake yi, in Rauda alkhairi ce a rayuwar ka Allah ya baka ita in ba alkhairi bace ya fitar da ita daga ranka."

Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa da maganar Hydar kafin Hydar ya kuma cewa, "then yana da kyau ko number yarinyar ne ka nema sabida ku dinga gaisawa, hakan zai rage maka wani abun a zuciyar ka." Asad ya girgiza kai alamun a'a kafin yace, "I can't."
"U can" ya bashi amsa shima yana kallon sa.  Murmushi Asad yayi har hak'oran sa suka bayyana fuskar sa ta washe sosai annurin ta ya fito kyau da zatin da Allah yayi mata ya fito k'arara ba tare da ya shirya ba. Ganin hakan ya saka Hydar yayi murmushin shima yace, "Kayi murmushi mana nasan zaka iya sabida kana sonta."

Baice komai ba Hydar daman yasan bazai ce ba sai yace, "Deaf nifa ina ganin rashin gaskiya a tare da Aliyu cikin kwanakin nan, bana amincewa da yanayin sa gabad'aya." Tab'e baki Asad yayi kawai baice komai ba dan shima ya fahimta musamman ma halayya da shiga da ya canja ya koma sak irin nasa kafin ya d'auki wayar sa ya fara dannawa. Haka suka zauna shiru babu mai magana a cikin su sai daga baya suka tafi suka bar gidan.

*☆☆*

Mum ce a zaune a gaban wani malamin daban ba wanda suka je wajan sa da Mama ba yana ta dube-duben sa kafin ya d'ago ya kalle ta yace, "Auren nasu yana da wahalar rabuwa amma za'a raba shi." Mum ta girgiza kai tace, "haka nake so naji Malam, so nake a raba auren a saka masa tsanar yarinyar itama a saka mata tsanar sa ta har abada." Malam yace, "wannan baki da matsala Hajiya Sadiya, sai dai za'a kashe kud'i."
"Kud'i ba matsala ta bane ba Malam ayi kawai."

Malam yace, "Zaki ga aiki kuwa nan bada jimawa ba." Gyara zama tayi tace, "Aiki na biyu so nake a saka masa k'aunar Jidda a ransa fiye da yadda yake k'aunar ita gurguwar, ya manta da kowa da komai Jidda kawai yake gani. Hatta uwar sa Rabi'atu ya manta da ita gabad'aya ya zama Jidda ce zata juya shi yadda take so duk abinda tace shi zaiyi." Girgiza kai tare da yin dariya kad'an yace, "Za'ayi hakan tabbas. Amma yana da wahala kasancewar sa mai ibada da zama cikin alwala muna buk'atar lokacin da ya kasance babu tsarki a jikin sa a sannan aikin mu zai tafi yadda muke so. Dan aikin da zamuyi masa akan Jidda ba k'arami bane ba gaskiya."
Chapter 54 · 0% Book details