← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 55

Sashe 30

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tayi dariya tana girgiza kai jin yau Rauda ake cewa ko a cikin y'ay'an sa ita ta dabance, ita yake yiwa wannan fara'ar har yana ce mata farar haihuwa. "Allah yayi mana arzuk'i" Umma ta furta a bayyane tana sauke numfashi.

Umma ya kalla yace, "Nawa ne kud'in da aka baki?." Yana fad'ar hakan ta d'auke takardun kud'in da nata dana Rauda ta rik'e bata ce komai ba ganin hakan ya saka yace, "Ga b'arawo zan sace miki kud'i shine kika d'auke ko?." Ita dai bata furta ba ya girgiza kai.

Ranar Umma ke da girki abinda baya faruwa a gidan ranar shine ya faru, lafiyayar shinkafa da miyar kaji aka yi a gidan kowa y'an makaranta suka dawo cikin ikon Allah akayi bak'i a yayyen su mata duk suka zo aka ci aka sha kowa da farin ciki a zuciyar sa ana ta santin auren Anas da Rauda. Rauda sai taji alfahari a zuciyar ta ganin ana ta santin abinda ta dalilin ta ya samu lokaci d'aya taji Anas yana samu kyakykyawan gurbi a zuciyar ta.

*☆☆*

A jingine yake da fuskar gado idanun sa a lumshe kana kallon yanayin sa kasan bashi da cikakkiyar lafiya haka zalika baya jin k'wari a jikin sa dan fuskar sa da yanayin sa ya gwada hakan. kamar wanda aka yiwa magana ya bud'e idanun sa yana kallon d'akin kafin ya sauke numfashi ya kalli k'ofar da za'a shigo d'aki jin motsi.
Mama ya gani ta shigo ya tashi zaune sosai yana kallon ta ta k'araso da sauri ta zauna kusa dashi ta tab'a fatar kansa tana kallon sa tace, "Asad ya jikin? Tun d'azu nake zuwa kana bacci."

"Naji sauk'i, Barka da safiya."
"Ka tabbata lafiya lau ka ke?" Ta furta ba tare da ta amsa gaisuwar ba. "Naji sauk'i" ya sake fad'a yana kallon ta. Fuskar sa ta rik'e tana kallon sa tace, "ka rame Asad yanayin fuskar ka ya nuna min akwai abinda yake damun ka bayan ciwon da kake fama dashi, meye?."
"Mama kwana biyu ta daina zuwar min cikin mafarkina, ina so na ganta ban san inda take ba, ina kewar ta sosai" ya furta yana kulle idanun sa yana nuni da tsantsar abinda yake zuciyar sa kenan.

Da mamaki mai had'e da fad'uwar gaba Mama tace,  "Wacece take zuwa mafarkin ka har kake so ka ganta?." Bud'e ido yayi yaga ta kafe shi da idanuwa sai kuma ya dawo hankalin sa tunawa da wacece a zaune kusa dashi ya sauke kai k'asa baice komai ba.

"Magana nake maka wacece?."
"Margayiya Hajiya mai babban d'aki" ya furta a hankali ba tare da ya kalle ta ba. Nannauyar ajiyar zuciya tayi jin abinda yace sai ta murmusa tace, "Ka dinga mata addu'a itace zata amfane ta a yanzu. Ni har ka bani tsoro na d'auka wata ce take kutse cikin mafarkin ka." Shiru yayi bai amsa ba gaban sa mugun fad'uwa haka kawai ba tare da ya san dalilin hakan ba.

Tashi tayi ta fita jim kad'an ta dawo da abincin sa da kanta ta zauna kusa dashi ta had'a masa duk abinda zai buk'ata ta bashi tace, "maza ka cinye akwai maganin da Abie ya aiko dashi zaka sha." Bai ki ba ya ci abincin daidai yadda zai iya ya bar sauran ya sha maganin da ta cika masa a k'aramin kofi.

Kallon sa tayi bayan ya shanye maganin tace, "mahaifin ka ya dawo d'azu in ka samu lafiya sai kaje ku gaisa. Sannan na hana kowa shigowa apartment d'in nan koda Hafiz ne ko Suhail ban lamunci su zo nan ba, in suna son had'uwa da kai suje wani wajan amma banda gidan nan na lura masu son ganin bayan ka suna da yawa." Kai kawai ya girgiza dan bazai kuma iya cewa komai ba.

Fita tayi daga d'akin ya sauke ajiyar zuciya ya d'auki ruwa ya sha, "Rauda!." Ya ji bakin sa ya furta ba tare da ya shirya hakan ba ya runtse idanun sa yana hango idanun ta da goshin ta ya bud'e yana cize bakin sa ji yake kamar ya tsinke kansa da mari. Yadda yake jin begun zuciya da fad'uwar gaba abin har tsoro yake bashi ya kalli gefen k'irjin sa yaga yana d'agawa a hankali.

Tashi tsaye yayi yana dafe da kansa sa ya kalli agogo inda ya nuna masa k'arfe hud'u na yamma ya sauke numfashi a karo na babu adadi ya shiga band'aki, bai jima sosai ba ya fito ya shirya cikin manyan kaya kamar koda yaushe yayi kyau sosai duk da ya rame amma kyawun sa bai b'uya ba.

K'ofa aka bud'e aka shigo bai kalli wanda ya shigo ba dan yasan bazai wuce jinin sa Aliyu ba shi kad'ai ne zai shigo babu izinin sa, "ya jikin ma?" Aliyu ya tambaya yana kallon sa. Juyowa yayi ya kalle shi da niyar bashi amsa sai maganar ta tsaya ganin abinda bai tab'a gani ba tun bayan girman su shi ya gani a tare dashi. kayan da yake jikin Asad irin sa Aliyu ya saka hatta hular kan su iri d'aya ce kamar su ta fito sak babu wanda zai banbance Aliyu babu wanda zai banbance Asad.

"I'm fine, thanks you" ya furta a tak'aice bai kuma kallon sa ba. Aliyu bai damu ba bai kuma kallon sa ba shima ya fita daga d'akin. Sosai Asad yake cikin mamakin canjawar da Aliyu yayi ya koma sak irin sa, hatta yadda yake magana shima ya mayar da tasa hakan babu ta yadda zaka ce ba shi bane in kaga Aliyu a canjin da ya samu abin yana d'aure masa kai. Waya da key na mota ya d'auko duk da baya jin k'arfi a jikin sa ga jiri da yake ji amma baya son zaman gidan ya fito falo. Babu kowa a falon ya wuce ya fita zuwa harabar apartment d'in nasu.

A sannu yake takawa sabida yadda kan yake masa ciwo cikin nutsuwa yake giftawa khamshi yana tashi. ganin yadda ake gaishe shi jiki yana rawa ya fahimci d'auka suke Aliyu ne dan shi ya fara fitowa sun gane kayan jikin sa hakan ya saka shi fita daga gidan da sassarfa.

*☆☆☆.*

"Khalil! Khalil!!, baka ji ina yi maka magana ne?" Umma ta fad'a daga d'aki tana fitowa amma babu Khalil babu dalilin sa. "Lallai ma yaron nan nace ya jira ni zan aike sa sai ya fice?." Rauda da take zaune tace, "yammar tayi ai ya tafi ball balle yau da garin yake a rufe ba rana" ta fad'a tana cigaba da karanta azkar.
"Ina Khairi?."
"Ta tafi kara Yaya Ummi bakin titi."
"Rahma kuma basa nan?."
"Duka sun fita" Rauda ta sake bata amsa tana kallon ta.

Umma tayi k'wafa tana girgiza kai Rauda tace, "A kira miki shi ne?." Umma tace, "k'yale ni bara na fita da kaina na kira shi."
Da sauri ta ajjiye littafin hannun ta ta mik'e tace, "Haba Umma bana so kina fita irin haka wallahi, bara na kira miki shi da kaina." Umma tace, "in yayi nisa ki k'yale shi kar ki yi nisa kema." Da to ta amsa ta saka hijjabi ta fita tana dora sandinan ta.

Batayi nisa ba ta hango yara ana ta ball ta kalle su tace, "Ina Khalil?." D'aya daga cikin yaran yace, "Yanzun nan yayi titi." Rauda ta girgiza kai ta bi hanyar titin dan ta kira shi kar ayi magariba yana ball. Titi ta fito amma dai bata ganshi ba, ta dinga kallon titin amma baya nan taja tsaki ta juya da niyar komawa taji kamar tayi karo da mutum.

Gaban ta yayi muguwar fad'uwa shakar khamshin turaren da bazata manta dashi ba tayi saurin d'agowa ta kalle wanda ta buge. dogon tsaki Aliyu ya ja ya saka hannu biyu ya bangaje ta ta fad'i k'asa ya cize bakin sa cikin takaici da tunanin irin hukuncin da ya kamata yayi mata. kallon ta ya kuma yi itama shi take kallo haushi da tsanar sa take ji a zuciyar ta yace, "Mahaukaciya!" Abinda ya furta kenan ya wuce ya bar wajan zuciyar sa cike da jin haushin zuwan sa ma wajan, in badan mai martaba ba mai zai kawo shi unguwar talakawa kamar wannan, badan mutane da suke kai kawo ba babu abinda zai hana bai sake b'alla mata k'afa ba.

Kafin Rauda ta farga bata kuma ganin sa ba sai k'urar motar sa ta gani ta kyad'a kai tana jin zafi a hannun ta ta furta, "kaine dai mahaukaci bani ba, wanda bai san darajar na gaba dashi ba. Na tsane ka wallahi naso kuma ka tsyaa dana tabbatar maka da kaine mahaukaci bani ba." ta fad'a tana k'okarin Mik'ewa.

A hankalin motar Asad kirar range rover ash colour take yin slow daga gefen ta, wajan yake kalla yaga tabbas a nan suka had'u ya sake kallon gefe yaga kamar itace take so ta tashi kamar kuma ba itace ba, zuba mata ido yayi ta jikin glass d'in motar ganin fa da gaske ta kasa tashi ga kuma babu yawan mutane a wajan sai ya b'alle murfin motar ya fito duk da zuciyar sa na hana shi hakan amma gangar jikin sa tak'i karb'ar umarnin zuciyar tasa ya tsallako. Khamshin da taji a kanta ya saka ta d'ago kai ta kalle shi mamaki ya hana ta magana har ya kama kafad'ar ta kamar jiya ya tasar da ita tsaye bata san anyi ba.
Chapter 30 · 0% Book details