← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 55

Sashe 13

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhaima tayi masa kallon up and down tace, "Kai meyasa baza ka bashi ba?, kamar kai ma ya amince da kai ko?."
"Eh ya amince dashi, amma kin fini kusa dashi kece zakiyi ba tare da kowa yasan hakan ba, sharaɗin maganin ba'a so wanda zai sha yasan an zuba. help us please in wani abu ya same shi dukkan mu ya sama." Numfashi ta fesar tana kallon sa a kaikaice zuciyar ta cike da tunani kala-kala.

"Please Suhaima" ya fad'a yana sake marairaicewa yana kallon ta.
"Sorry I can't" tana fad'ar hakan ta juya ta bar wajan ya bita da kallo yana cize bakin sa ji yake kamar ya jawo ta ya shak'e mata wuya yayi k'wafa ya juya ya bar wajan zuciyar sa cike da k'unar rashin samun nasara.

Direct apartment d'in su Asad Suhaima ta wuce tana zuwa ta tarar dashi a zaune shida Hafiz ta shiga da sallama ta kalle shi tace, "Yaya ka amince da Suhail or not?." Hafiz yace, "what happened?."
"He called me yanzu yana fad'a min akwai maganin da zai bani na bawa Bro deaf yasha wai zai protecting d'in sa daga abinda za'a aiko masa dashi, ban amince dashi ba gaskiya."

"U see na fad'awa Asad Suhail ba abin yadda bane amma always sai yace min shi ya amince dashi, yanzu kin karb'i maganin?."
"No, I'm not."
"Ki kira shi yanzu ki karb'a sai ki zubar dashi in ba haka ba tabbas zai bayar a zuba masa ne, daga yau ko me zai baki akan Asad ki karb'a."
Asad yace, "kar ki karb'a." Da mamaki ta kalle shi tace, "Why?." Idanun sa ya zuba mata akan fuskar ta yace, "abinda nace kenan" yana fad'a ya tashi ya shiga d'aki ta bishi da kallo.

Hafiz ya kalle ta yace, "ban san me yake damun Asad ba akan Suhail, ya kasa gane inda ya dosa har yanzu but muje mu sanar da Mama ita kad'ai ce zatayi maganin abin." Kai ta d'aga alamun haka ne suka fita a tare zuwa wajan Mama.

Asad lokacin da ya shiga d'aki zagaye kawai yake yi a cikin d'akin gabad'aya ya rasa tunanin me zaiyi cikin kwanakin mugayen mafarkai yake da mutane kala-kala suna k'ok'arin cutar dashi, dalilin da ya sanya gabad'aya baya sha'awar yin sarautar ko kad'an amma Mama ta dage shi bai ga abin so a cikin ta ba.

Kan gadon sa ya kallah a gyare yake tsaf dan Suhaima ce kad'ai take shiga d'akin sa ta gyara sai Mama bayan su wani dogari ko baiwa basa zuwa cikin d'akin dan umarnin Mama ne. Tunda ya kwanta jiya a kansa yake jin kansa yayi masa mugun nauyi ga wasu abu kamar allura da yake ji yana sukar sa gabad'aya kansa ya kulle ya ma rasa tunanin me zaiyi.
Ji yayi gidan gabad'aya yayi masa zafi ya d'auki makullin mota ya fita daga d'akin.

Washe gari.

Bayan gari yayi haske sosai Hydar ya d'auki mota ya tafi asibitin da Rauda take ya nufi office d'in Dr da sallama, yana ganin sa ya mik'e tsaye yana fad'in, "Barka da zuwa prince."
"Ya jikin ta?."
"Da sauk'i, mun samo dangin ta ma suna wajan ta a yanzu."
"Good a cigaba da kula da ita ayi mata komai, but bana so suna na ya fito a maganar ka samu wani sunan but banda nawa."

"Okay Prince in sha Allah."
"Let's go" tare suka fito suka shiga d'akin da take nan suka samu Mama da Baba da kuma Inna suna zaune a kusa da ita. Da sallama suka shiga suka amsa Hydar ya kalle su dukkan su kana ganin su kasan talakawa ne duk da duk wanda yake k'ark'arin masarauta talaka ne amma nasu talaucin ya fito yace, "Ya mai jikin?, nine wanda na buge."

Ganin babban mutum mai kalama da kwarjini kamar Hydar sai Baba aka gyara tsayuwa aka ce, "Jiki gashi nan dai har yanzu bata farka ba, sai dai fatan Allah ya bata lafiya." Kusa da gadon nata Hydar ya k'arasa yana kallon ta ya kalle su yace, "zata ji sauk'i, Dr zai mata komai babu damuwa."
"Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Umma ta fad'a tana kallon sa. Kai kawai ya d'aga baice komai ba ya fita daga d'akin daman burin sa a samo dangin ta.

Gida ya koma ya shirya zai tafi aiki kasnacewar Friday ce, bayan ya gama ya shiga wajan Mama ta kalle shi tun kafin yayi magana tace, "Ina kaje d'azu?." Da girmamawa yace, "naje wajan wacce na buge ne."
"Kaje kayi mata me? Ba ka bada komai Dr zai mata meye naka na zuwa inda take?." Shiru yayi Bai amsa mata ba tace, "Sunan ta Rauda iyayen ta talakawa ne suna zaune a unguwa Katsalle tana saida abinci a kasuwa meye naka da zaka dinga zuwa inda take?, wannan ba kalar wacce zaka je dubawa bace Hydar, zubar da kima ne a ganka a wajanta!, Tunda ka bar komai hannun Dr kar ka sake waiwayon ta kayi mata iya k'ok'arin ka."

Kallon mahaifiyar tasa yake da zallar mamaki jin har ta binciko komai a kanta daga jiya zuwa yau kuma wai ya daina zuwa inda take tsakani da Allah ai babu adalci a cikin abinda tace shi kuma bazai iya ba, baice komai ba sai daga baya yace, "In kin min izini zan fita." Ta kalle shi da hannu tayi masa alama haka ya fice taja dogon tsaki tana fad'in, "meye nasa na damuwa akan wata banza y'ar talakawa oho?, har na tsani yarinyar" ta fad'a tana yarfe hannun ta tana tab'e bakin ta.

*GRA.*

Su biyu ne kacal a zaune a falon Sadiya da y'ar ta Jidda suna zaune suna tattaunawa kamar koda yaushe Jidda tace, "Mum u mean zan mallaki Asad matsayin miji na?." Sadiya ta murmusa tace, "of course Jidda, nan kusa bada jimawa ba zaki zama mallakin sa."
"Wow!" ta furta tana juya idanun ta cikin jin dad'in abinda Mum d'in tace. Murmushi mahaifiyar tata tayi tana kallon ta tace, "Wannan kyauwu naki Jidda ai sai sarki, d'an sarki, jikin sarki ne zai d'auka."
"But Mum kina ganin zaiamince?, kin san halin sa fa kamar ba mutum ba."
"Babu abinda zai hana ya amince, yana jin maganar Maman sa fiye da tunanin ki, ko wuta ta nuna masa tace ya shiga zai iya shiga kuma ke kin san yadda take jin maganata ko ta iyayen ta bata ji, duk yadda zanyi sai nayi wajan ganin kin shiga cikin gidan nan matsayin matar sa. Wallahi zan iya k'arar da komai nawa wajan ganin hakan ya tabbata."

Jidda bata ce komai ba Mum ta kuma cewa, "da sannu zan kwace duk wani jin kai da take ji dashi ya dawo hannun ki, da idanun ta zata kasa sarrafa d'an ta sai abinda muka ce shi zaiyi, tana muryar d'an ta zai zama sarki ne ni kuma ina murnar zaki mallaki sarki, zata kasance mahaifiya a gare shi zaki kasance mata a gare shi, duk wani sirrkan sa zai dawo tafin hannun mu daga nan Rabi'atu ta gama yawo."

Murmushi Jidda tayi kyawun ta ya sake bayyana kana kallon ta kasan asalin iyayen ta ba hausawa bane tace, "Mum tana son Asad sosai fa, kina ganin zata bada wata dama kuwa?."
"Nice damar ai Jidda sai abinda nace mata ke kin sani, duk wannan zafin kan da take ji dashi sai na sauke mata. Kin san wahalar da nasha kafin na mallake ta kuwa...? Na kashe kud'i ban san adadin su ba wallahi. Akwai tarin abubuwan da tayi min a baya na tabbata ita ta manta amma ni ban manta ba, kwantan b'auna kawai nake mata so nake ki mallaki Asad a nan zata gane wacec Sadiya."
"Mum indai mallakar Asad ne lokaci ya kusa ai, ina so ma naje gidan na gaida ta."
"Hakan yana da kyau Jidda, kije gobe ki wuni a can ki samu ku keb'e keda Asad duk da baya magana kiyi k'ok'arin ganin kunyi magana dashi."

Shiru Jidda tayi Mum tace, "zan baki turare ki shafa a jikin ki duk wanda ya shak'i shi sai ya rikice Jidda." Dariya tayi tace, "da alama kin gama shirin ki Mum."
"Murucin kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya, lamarin Rabi'atu ba abu bane mai sauk'i ta wuce inda kike tunani. Kar take kallon kowa kanta na mugun ja sai da dabara da wayo zaka gano lagwon ta." Bata ce komai ba ta cigaba da danna wayar ta amma zuciyar ta cike take da farin cikin zata zama mata ga Asad kyakykyawa, mai aji, mai nutsuwa, mai kud'i, mai ilimi kuma sarki d'an sarki.

*◇◇◇*
K'asa-k'asa take magana kai da kaji kasan duk abinda ake fad'a babu gaskiya a cikin sa tana fad'in, "ka tabbatar Suhail ya saka layar a k'asan kafitar sa?." Daga can b'angaren yace, "na tabbatar domin inda bai saka ba Suhail bazai min k'arya ba."
"Amma kasan ni bana son long process nafi son ayi abu a gama kawai a wuce wajen."
"Ki kwantar da hankalin ki zancen da nake miki ma mai martaba ya jinkirta bayar da kujerar zuwa nan da wani lokaci."

"Kai kamar baka san halin sa ba?, kwantan b'auna zai mana lokaci d'aya sai dai mu wayi gari muji ana bugawa Asad tambari, nifa in ba gani nayi an kawar da Asad ba hankali na bazai kwanta ba."
"Ki kwantar da hankalin ki in abun bai yu ba a wannan karon zamu nemi master planer......."

"Master planer!? Wacece Master planer?" Ta fad'a da mamaki tana jiran amasa. Murmushi yayi mai sauti yace, "Zaki Santa in lokacin hakan yayi, ita take tsara komai kuma yake tafiya yadda ya kamata, in abu ya gagare ni ita nake nema, ta wuce duk tunanin ki ta dame ki ta shanye a hatsabibanci, ta wuce tunanin ki da hankalin ki, in kika ji shirin ta sai kin san naki ba komai bane ba."
Chapter 13 · 0% Book details