← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 55

Sashe 31

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lallai ma wannan mutumin yana raina mata hankali, shi kuwa fuskar ta yake kallo da babu niqab ko face mask zahirin tace a bayyane. d'auke idanu tayi dan yana yi mata kwarjini jin baice komai ba ya saka tace, "wai fuska biyu ce da kai wani lokacin kamar mutumin kirki wani lokacin mutumin banza ne kai, in zaka yiwa mutane fuska biyu banda ni domin na riga na gama gano kai d'in ba komai bane face mahaukaci wanda bai san darajar d'an adam ba. ban tab'a jin tsanar halitta kamar yadda nake jin tsanar ka ba. Na fad'i duk abinda yake bakina in ka dama ka saka a kashe ni a nan shine zaka nuna min lallai kana da k'arfin ikon mulki da sarauta. Ni kuma zan nuna maka k'arfin sarautar Allah domin ahi kad'ai nake jin tsoro a duniyar nan" ta fad'a tana d'ago ido ta zuba masa banzar harara mai d'auke da zallar tsana da k'yama.

Baice komai ba daman bazai ce ba dan ya gama fahimtar duk abinda take fad'a ba dashi take ba babban abinda yake d'aure masa kai a ina suke had'uwa da Aliyu?, "Lahh Yaya Aliyu!" Aka fad'a daga bayan sa cikin mamaki. Bai juya ba hakan ya saka Khairi k'arasowa da sauri ta tsaya kusa dashi tana dariya tace, "Ashe dai zan gane ka, ina wuni Yaya Aliyu?."
Kallon ta yake yana so ya tuna inda ya santa ganin hakan ya saka Khairi tace, "Wacce ka siyawa Yayar ta kayan fruits a k'ofar asibitiiiiii....?" Ta fad'a tana jan kalmar asibitin lallai sai ya gano.

Murmushi yayi kad'an alamun ya tuna ganin hakan ya saka tace, "Kaga yayar tawa nan ita ka siyawa. Anty Rauda ina lokacin da kina asibiti Baba ya bada d'ari biyu na siyo miki lemo a wajeeee.. Har Umma ta dinga min fad'aaaaaa? To kin ga wanda ya siya miki yace na kawo." Juyo da kallon ta tayi ga Asad tace, "Yaya Aliyu kaga Antyna ta koma mai yawo da sanda ko? Wanda ya buge ta ya daina zuwa inda take ance kuma sai an mata aiki zata warke mu kuma bamu da kud'in biyan kud'in, shikenan Antyna ta zama gurguwa" ta fad'a kamar zatayi kuka.

Takaici, bak'in ciki, b'acin rai suka tararwa Rauda lokaci d'aya bata san sanda ta tsinke Khairi da mari ba ta jawo ta kusa da ita ciki fad'a sosai ta zare mata idanu tace, "in baki min shiru ba sai na fasa miki baki, banza wacce bata iya shiru a rayuwar ta. Wa kika tab'a gani yana kula wanda basu san darajar mutane ba irin wand'an nan? Wa kike ganin yana kula masu shaye-shaye da neman mata eyeee?."

Khairi da take hawaye tace, "Wallahi yana da kirki Anty." Bai ji mai tace mata a gaba ba tafiya suke yi shi kuma ya juya zuwa cikin motar sa, duk da kalamai ta fad'a masu muni amma sam baiji komai a ransa ba dan maganar ta ta tabbatar masa da Aliyu yake bada shi ba.

A kan sitiyarin motar ya saukar da kansa yana furzar da iska a hankali yana jan numfashi yana saukewa, kallon inda suke yayi yana hango su da alama fad'a take yiwa Khairi dan yaga tana magana a fusace, duk taku d'aya da take yi tana nisa dashi ji yake kamar ana d'igo masa kewa wacce bai san dalilin ta ba a zuciyar sa tana yin gaba yana sake jin kewar na k'aruwa har ya daina hango su.

_Ya akayi ta san Aliyu?, a ina suke had'uwa haka?. Da gaske silar Hydar ta zama gurgurwa?._ tambayoyin da yake yiwa kansa a zuciyar sa kenan amma babu mai bashi amsa sai ita d'in. Sake kallon layin nasu yayi ya sauke numfashi sunan Rauda na yi masa amsa kuwa a cikin kunnuwan sa. "Inda Aliyu ta fad'awa hakan da me zai faru?" Ya furta a bayyane har lokacin yana kallon inda suka bi dan yasan tabbas sai dai wata ba ita ba, babu abinda zai saka Aliyu bai mata mummunan hukunci ba.

Yarinyar cikin mafarkin sa yake tuno fuskar ta idanun ta da goshin ta yake ganowa kamar ko yaushe, bud'e ido yayi ya tuno lokacin da Rauda ta bud'e idanun ta tana yiwa Khairi fad'a gabad'aya yanayin ta ya koma irin na yarinyar mafarkin sa. "Itace ko A'a" Ya tambaya yana dafe kansa da duka hannayen sa guda biyu jin bak'on abu wanda bai tab'a jin irin sa ba yana cigaba zuciyar sa da ko ina na jikin sa.

*KWANTAN ƁAUNA*

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*015*

Fuska a had'e Rauda ta shiga cikin gidan su Khairi na bayan ta tana gurshek'en kuka sai Khalil da yake biye dasu a baya. Ganin su haka ya saka Umma ta kalli Rauda tace, "Tun d'azu Rauda sai yanzu?." Zama Rauda tayi kafin tace, "Sai da naje titi." Umma tace, "Ke kuma Ummin ce ta dake ki kike kuka?."
Khairi tace, "Anty Rauda ce, dan kawai naga wanda ya siya mata fruits a asibiti na yi masa magana shine ta mare ni" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da kuka.

Umma ta kalli Rauda tace, "Akan me zaki mare ta Rauda bayan abin arzuk'i tayi? Ai ba laifi bane da taga wanda yayi mata alkhairi ta nuna ta san shi. Inda arzuk'i kema gaisawa ya kamata kuyi dan taimakon ki yayi." Rauda tace, "Umma bai cancanci a kula shi ba, bai san darajar d'an adam ba kwata-kwata." Da mamaki Umma tace, "Ke ya akayi kika sani?."
"Umma ina wannan d'an sarkin da muka had'u dashi a gidan sarki..? Wanda muka sake had'uwa dashi har Khalil yake cewa yace na shiga mota nak'i...?. dashi muka kuma had'uwa yau, shine fa wanda take cewa ya siyi kayan marmari dan tsabar k'arya."

"Wallahi ba k'arya nake ba shine Umma" Khairi ta fad'a tana kuka. Umma ta kalle ta zatayi magana Rauda tace, "Sai sake marin fuskar ki sannan zakiyi mana shiru naga alama. Bashi da kirki fa ko kad'an Umma yau ma baki ga kalar rashin mutuncin da yayi min ba."

Umma tace, "Kuma dai?." Rauda tace, "Kin san Khairi da shegen surutu ta dinga zuba a gaban sa maganar da ba'a tambaye ta ita take furtawa shiyasa na mare ta, wannan ai ba wanda za'a kula bane ba. Habiba tace min har neman mata yake yi garin haka in yayi mata wani abun fa tunda yasan babu abinda zamu iya?." Umma ta rik'e baki tana nuna Rauda da yatsa tace, "Ina raba ki Rauda da irin wad'annan zantuttukan wallahi, kinga ki kiyayi bakin ki kar ki jawo abinda zaki zo kina dana sani. Ina ruwan ki da sabgar sane wai? Ba abinda ya had'a ku ki dinga k'okarin gefa rayuwar ki a hatsari sabida tsiwa. Kuma kar na k'ara ji kince yana neman mata tunda kedai bai neme ki ba bai kuma nema a gaban idanun ki ba, ki kiyayi tsayuwa gaban Allah."

"Wallahi Allah na tsane shi tsana mai muni Umma, ban tab'a jin tsanar wata halitta a duniya kamar sa ba, bana son ganin koda fuskar sa ce." Umma bata ce komai ba ta wuce tana d'aura alawar magriba dan bata ga amfanin yi mata magana ba.

Bayan an idar da sallah suna zaune cikin k'aramin hasken fitilar tsakar gidan Baba ya shigo kamar an cillo shi har tuntub'e yake yi, "Ke Rauda maza jeki ga Anas can yana jiran ki." Abincin hannun ta ajjiye dan tasan ko bata ajjiye ba tunda yace ta tashi sai fa ta tashj tana k'okarin mik'ewa cikin fad'a yace, "ki k'arfafa jikin ki malama ki tashi." Babu wanda ya tanka ta tashi ta saka hijjabi ya d'auki kujerar da take zama da kansa yayi gaba tana bin sa baya.

Sanyin khamshi taji tunda ta shigo soron gidan nasu Baba ya ajjiye mata kujerarya kalli Anas da yake tsaye yace, "Gata ta fito maka da ita da kaina, zauna mana" ya fad'a yana kallon Rauda. Ba musu ta zauna Anas ya duk'a har k'asa yace, "Allah ya saka da alkhairi Baba." Baba ya amsa da amin ya fita.
Zama yayi kan irin tata kujerar yana kallon ta cikin hasken fitilar da aka ajjiye a soron ga hasken wayar sa da ya kunna gana waje wanda yake shigowa, bata d'ago ba shi kuma baiyi magana ba.

Jin shirun yayi yawa ya saka ta d'ago sai suka had'a ido karon farko tayi murmushi mai kyau tace, "Ina wuni." Jinjina da kujerar Anas yayi ji yayi in bai jingina ba iskar soyayya da take kad'a zata iya d'auke shi ta kai shi wani wajan shiyasa ya nemi mafita tun da wuri. Bai jima sosai ba ya kalle ta yace, "Dan Allah ki sake min murmushi da kika yi yanzu." Bata san lokacin da murmushin ya sub'uce mata ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na gode my love, Allah ya biya ki da aljanna."

"Baka amsa ba na gaishe ka" ta furta a hankali.
"I'm sorry My love, murmushin da kika yi min a karon farko a rayuwa ta ya saka na manta duk abinda kika ce. Lafiya lau ya jikin ki?."
"Da sauk'i."
"Allah ya k'ara lafiya. Kiyi hak'uri na nemi wayar Baba lokacin da abin ya faru ban same shi ba, ina can hankali na yana kan ki Rauda duk da tarin aiyukan da suka min yawa."

A sanyaye tace, "haka Allah ya k'addara, babu komai a hakan ma na gode sosai, mun ga abubuwan alkhairi Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata. Umma tace nayi maka godiya sosai." Murmushi yayi yace, "Babu komai Rauda kar ki damu."

Shiru ya sake biyo baya kafin yace, "Munyi magana da Baba akan aikin k'afar ki in sha Allah tafiyar ki zata dawo kamar dah indai ina da rai tunda aikin ba wani mai wahala bane indai aka bar nigeria, cikin satin nan in Allah ya amince za'a yi aikin." D'ago ido tayi suka had'a idanu yayi murmushi sai tace, "Na gode."
"Haba Rauda ni dake babu godiya wallahi, fatana ki amince da soyayya ta ki yadda dani har ta kai mu ga aure."
Murmushi tayi kad'an bata ce komai ba domin ita kam bata d'auka zai sake dawowa inda take ba sabida lalurar da ta same ta.
Chapter 31 · 0% Book details