Sashe 39
Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba yayi shiru da alama duk kwadayin sa shima maganar bata shige shi sosai ba yace, "To nema mata lafiya za'ayi ai, kamar kuma kin san abinda yace dan ya fad'a a bada babba guda d'aya ko mace ko namiji da za'a tafiyar tare kin ga kenan ya san abinda yake yi. Kuma kina kallon sa kin ga fuskar sarki Sa'ad yadda ya fad'a min sunan sa Asad yafi kowa hankali da ilimj a gidan sarki, kowa ya sanshi da a k'asar saudia yake da zama bai jima da dawowa ba shiyasa na amince da maganar sa tunda nema mata lafiya za'ayi kuma daman sune da hakkin hakan."
Umma dai bata kuma iya cewa komai ba ta ja bakin ta tayi shiru. Rauda kuwa sabon tunanin ta afka cikin mamaki da al'ajabi kenan daman yasan d'an uwan sane ya buge ta shiyasa yake k'okarin taimakon ta koda yaushe? Ya akayi yasan nice wacce d'an uwan sa ya buge? Ya akayi ya nemo ni yasan nice har ya san gidan nan?. Babu mai bata amsa sai ta ajjiye abincin dan ya fita daga kanta kuma ta tashi ta shiga d'aki tana shiga ana kawo wuta gidan ya haske d'akin nasu fanka ta fara kad'awa mai sanyi.
Duk watsewa akayi daga tsakar gidan Umma ta biyo bayan ta tace, "Rauda a ina kuka had'u dashi wannan d'in? Wanne taimako yayi miki yau?." Bata b'oyewa Umma ba ta fad'a mata komai har k'arshe Umma ta jinjina kai tace, "Ikon Allah! Kinga illar rashin kunyar ki da nake fad'a miki ko? Yanzu badan shi yazo ba da me kike tunanin zaiyi miki....?." Rauda ta sunkuyar da kanta k'asa Umma ta kuma cewa, "Ki dinga fad'a har da maza akan wani abu kalilan wanda bai kai ya kawo ba, meye dan ya mare ki a gidan sarki basai ki manta anyi hakan ba tunda kin san yafi k'arfin ki...?. Har da kuka kuma had'uwa wai sai kika ce masa mahaukaci da yake bakya gudun abinda zai je ya dawo. Yanzu me gari ya waya da ya saka karen ya yaga naman ki sun kuma yi miki fyad'e fa?."
Rauda a sanyaye tace, "Umma Allah ya rubuta faruwar hakan ne kawai." Umma tace, "Koma dai meye ke kika ja ai. kenan y'an ukun da ake zance akwai su a shigan sarki kin shiga rayuwar su dukka su ukun. to Allah ya kub'utar dake daga sharrin babban shi kuma wannan da ya taimake ki Allah ya saka masa da alkhairi, d'ayan kuma Allah ya bashi lafiya. Ke kuma nan gaba sai ki kama kanki." Da amin ta amsa a ciki ta shirya ta kwanta zuciyar ta cike da tunane-tunane.
*☆☆☆*
B'angaren Asad tunda ya bar k'ofar gidan su Rauda inda ake ajjiye karnukan ya kai Bobby ya ajjiye sannan ya nufi gida kamar koda yaushe. jin zuciyar sa yake da dad'i babu dad'i, in ya tuna yayi magana da iyayen Rauda akan ciwon ta sai taji dad'i a ransa, in kuma ya tuna da wani abun sai gaban sa ya fad'i a haka har ya k'arasa gida.
Yana shiga B'angaren su ya samu Aliyu a zaune yana wuci yana shiga ya mik'e ya tare masa hanya yace, "Waye ya baka ikon hana yiwa wacce na saka a yiwa hukunci?."
Asad ya kalle shi kamar zai magana sai kuma ya fasa ya rab'a ta d'aya gefen zai wuce Aliyu ya sake tare shi yace, "Magana nake maka Asad, me kake ji dashi har da zan yi hukunci ka saka a warware?." Asad ya kalle shi ido cikin ido yana juya nasa idanun yace, "Sabida baza'a yi d'in ba."
"Har kai ka isa!, me kake ji dashi da zaka hana ni abinda nayi niya?. Wacece ita a wajan ka da zaka hana ni d'aukar mataki?."
"Special one" ya bashi amsa a tak'aice yana wuce shi ya shiga d'aki ya bar shi a tsaye baki bud'e yana kallon sa.
"Special one? Me yake nufi?, kenan ta musamman ce a wajan sa?. In na fahimta daidai kamar wata ce a wajan sa ko wacce yake so?." Sai kuma ya dafe kansa yace, "A'a Aliyu this is not possible kawai akwai dalilin nasa nayi hakan, tunda har kuwa baya so koda nayi niyar na rabu da ita na fasa, yanzu na fara sakawa a hukunta ta indai hakan zai b'ata masa rai shine fatana" yana fad'a ya fita daga falon da sauri.
Asad kuwa wanka yayi ya saka kayan bacci ya fito zuwa falo, yunwa yake ji amma bazai iya cin abincin da ya gani a ajjiye ba haka kawai zuciyar sa bata yarda ba ya fita zuwa apartment d'in Mama. Bai same ta ba daman ba wajan ta yazo ba ya shiga ciki yaga abinci ya zuba yaci yarda yake so sannan ya tashi ya shiga ya duba Hydar ya koma.
Koda ya koma d'akin sa kalmar da ua fad'awa Aliyu ce ta fad'o masa zuciyar sa, ya tsaya a jikin madubi yana kallon kansa a bayyane yace, "Da gaske special one ce?." Sai kuma ya murmusa sosai har hak'oran sa suka bayyana ya shafa gemun sa ya zauna a gafen gadon yana jin muryar ta mai sanyi tana sake rantsa dodon kunnen sa. Ido ya lumshe tunawa da ta bashi hak'uri sai yaji zuciyar sa tayi fess ya dinga murmushi shi kad'ai a haka har ya kwanta yayi bacci.
Washe gari da misalin k'arfe goma na safe ake kwad'a sallama a k'ofar gidan su Rauda, Baba ya fita ba jimawa ya dawo ya kalli Rauda da take zaune tayi wanka yace, "gashi yarima ya turo zaku je, ki d'auko katin d'an k'asar ki kema ki d'auko naki kuje ke ya kamata ku tafi tare in tafiyar ce" ya fad'a yana Kallon Umma. Umma tace, "Ni da nace cikin yayen ta suje da guda d'aya."
Baba yace, "Duka su kad'ai ne wajan mazan su basa yi doguwar tafiya irin wannan ba. ke dan fa aikin jinya za'ayi da wallahi bazan neme ki ba ni zanje kodan na kashe kwarkwatar idanu na, to jinyar mace sai mace ki tashi ki d'auko ku tafi ana jiran ku."
Umma ba dan taso ba ta tashi ta saka mayafi ta d'auko katin d'an k'asar ta fito tana fad'in, "Amma malam kyau kaima kabi mu muje tare." Baba yace, "wannan a rubuce yake ai ba sai kin fad'a ba, d'an sarki fa da kansa wanda mai martaba yake ji dashi. na san abinda zai kunso muku ai gwraa naje nima." Umma ta kalle shi cikin takaici jin badan tsare lafiyar su zai je ba dan abinda za'a samo ne.
Inna da ta lek'o daga d'aki tana kallon su tace, "duk wanda ya hau motar kwadayi zata juye su a tashar wulaqanci, daga uwar har uban har y'ar." Ba wanda ya tanka mata suka fita. Suna hango su jiki na rawa suka bud'e musu mota su uku a baya aka ja suka tafi.
Da yake abu ne na manya an sanar da komai suna zuwa aka fara yi musu ashe Baba ma da nasa katin ya tawo wai bai san inda rana zata fad'i ba, kafin azahar an gama musu fasko an awa ashirin da hud'u zai fito da yake na manya ne babu b'ata lokaci. Suna baro wajan d'aya daga cikin dogaran ya kalle su yace, "Mai girma yarima Asad ya umarce mu da in mun gama mu kai ku inda zaku ci abinci sannan a mayar daku gida, yanzu zamu k'arasa wajan in zaku shiga ciki sai muje in zuwa za'ayi a kawo muku duk d'aya ne."
Kafin Baba yace wani abu Umma tace, "A'a ba sai muje ba mu wuce gida hakan ma mun gode."
"A'a ranki ya dad'e, yarima Asad bazai ji dad'i ba in muka ce masa bamu je ba, ku daure muje sai a kawo muku nan."
"Babu damuwa" Baba ys fad'a da sauri suka cigaba da tafiya. Gaban babban gidan abinci suka tsaya kafin na gaban yace, "ranku ya dad'e me za'a kawo muku?."
"Duk abinda ya samu" Umma ta fad'a kawai suka amsa da to suka fita.
Basu jima sosai ba suka dawo da ledoji manya suka shigo motar suka mik'a musu sai khamshi ne yake tashi sannan suka wuce gida, sai da suka har gida sun shiga sannan suka wuce.
*☆☆☆*
A zaune ya samu Mama kusa da godon Hydar ya shigo tana ganin sa tace, "Asad Hydar ya motsa yau da alama yana gab da farkawa" ta fad'a cikin nishad'i tana kallon sa. Murmusawa yayi kad'an ya k'arasa kusa da gadon yana kallon sa.
"Sadiya ta kira ni tace min kaje jiya naji dad'in hakan" ta furta a tak'aice tana kallon sa. Numfashi ya saukar a hankali yace, "kiyi hak'uri Mama, amma bata dace dani ba."
"Ta dace dakai Asad ita na zab'a maka ita nake so ka aura."
"Tohm Mama" Ya furta yana juyawa ya fita daga d'akin gabad'aya.
Yana fita mota ya d'auka ya fita daga gida.
Gidan da ya saba zuwa yaje ya zauna shi kad'ai yana tunanin da ya saba kansa a kulle kamar ko yaushe. idanun sa a kulle yana zaune ko motsin kirki bayayi babu abinda yake ji a zuciyar yake kuma gani sai Rauda ba tare da yasan dalilin hakan ba kawai ji yake zuciyar sa na motsawa a kan hakan. Ya sauke numfashi mai k'arfi ya tashi zaune sosai yana mutstsika idanun sa, jinin jikin sa yake ji tana shiga ko ina ya rasa gane tausayin ta yake ji sabida ta rasa k'afar ta ta dalilin Hydar ko kuma me? Bai sani ba bai san meyasa yake ganin ta always ba ko yaya ya kulle idanu ita yake gani; ya kasa banbance itace ta mafarkin sa ko ba ita bace?.