← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 55

Sashe 44

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asad bai amsa ba daman yasan bazai amsa ba hakan ya saka yace, "deaf kana nufin kana son ta kenan?" Ya fad'a yana kallon fuskar sa. Ido Asad ya bud'e suka had'a ido yana kallon sa ya cize baki kafin ya girgiza kai alamun a'a, Hydar yace, "meye in ba so ba?." Asad ya d'age kafad'a alamun bai sani ba.

Hydar yazo kusa dashi ya dafa shi yace, "Deaf kana sonta na tabbatar tun a mafarkin ka ka fara sonta naga hakan a cikin idanun ka, lokacin da mahaifin ta yake gabatar mana da wannan mutumin I saw so many changes on your face, like kishin abinda akace nake hangowa a kan idanun ka a kwanshe, that's mean kana son ta Asad."

Zubawa Hydar ido yayi yana kallon sa har ya kai k'arshen maganar sa kafin yace, "A'a Hydar, hakan bazai yu ba."
"It can be deaf, kai mutum ne kana da zuciya kana kuma da feeling ko da yaushe zuciyar ka zata kamuwa da soyayyar wacce ta aminta da ita. Kana son ta Asad ka amince dani." Numfashi ya fesar ya bar wajan ya koma gefen gado ya zauna ya jawo drawer ya d'auko passport d'inta ya bud'e yana kallon hoton jiki.

Hydar ya murmusa ya k'araso gaban sa ya duk'a yace, "believe me your in love deaf, nasan tunanin ka ta ya zaka tunkari wannan yarinyar da batun love, ka bar min komai a hannu na zanyi komai."
"Nooo Hydar ban saka ka ba, ban amince kuma da abinda kace ba." Hydar ya murmusa baice komai ba yana kallon sa taurin kan Asad shine yake cutar sa wani lokacin. Fita Hydar yayi daga d'akin yana murmushi yana kuma neman hanyar da zai gabatar da yayan sa ga Rauda.

"How?" Ya furta bayan fitar Hydar ya kwanta a kan gado yana kallon sama yana jin zuciyar sa na bugawa da saurin gaske. Idanun sa ya kulle amma ita yake gani har lokacin ya bud'e ido sai yake jin sautin muryar ta a cikin kunnen sa hakan ya saka shi ya mik'e zunbur yana zaga d'akin. 'ta yaya zan fara son wacce aure na da ita bazai yu ba?, ta yaya zuciya ta zata so bayan Mama na raye?; oh my God ya zanyi?. firstly sai na cire ta a raina zan samu sauk'i, but itace take zuwa dreams d'ina bani na gayyace ta ba, meyasa take zuwa? Meyasa zuciyata take bugawa nake jinta a jikin ta?. oh my heart.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan ya dafe zuciyar sa da yake mugun gudu furta kalmaan da Hydar yayi ya saka zuciyar sa ta k'ara kaimi wajan gudu.

A daren ranar Asad ya tabbatar da son Rauda yake ba tausayin ta yake yi ba, ya tabbatar da maganar Hydar tun ganin da yake mata a farki Allah ya ajjiye soyayyar ta a cikin zuciyar sa, ya tabbatar da itace macen da ta samu nasarar d'aukar kambun soyayya a zuciyar sa. A cikin daren ya fara tunanin nemo hanyar da fidda ta daga zuciyar sa tun kafin dare yayi masa.

Washe gari.

Mama na zaune tana karyawa ita kad'ai a falon ta Aliyu ya shigo ya zauna kusa da ita ya jawo kayan breakfast na gaban ta ya fara sha shima, bata ce masa komai ba sai da ya had'a tea yasha kana ya kalle ta yace, "Mamana kin san me Asad yake shirin yi kuwa?." Ta kalle shi tace, "kamar ya kenan?."
"Mama ina wannan yarinyar da Hydar ya buge kika ce babu shi babu ita?."
"Ina jin ka."
"Itace dai yarinyar da ta kira ni da mahaukaci, at the end kuma kullum Asad sai yaje gidan su wajan ta, ya mata passport ita da iyayen ta zai kaita Egypt" ya fad'a yana kai grape bakin sa yana taunawa.

Mama ta ajjiye cup d'in hannun ta tace, "Me kake fad'a ne haka Aliyu?." Aliyu yace, "Abinda mahaifita taji shi nake fad'a, ina da tabbacin Mamana tasan bazan mata k'arya ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me ya had'a Asad da y'ar talakawa y'ar tallah har yake zuwa gidan su?."
Aliyu ya kalle ta yayi murmushi yace, "sabida yana sonta ne, yana kuma tunanin auren ta!."

"What? Aliyu kasan me kake cewa kuwa? Bana son shirme fa, wanne irin yana sonta Aliyu?." Aliyu ya mik'e tsaye yace, "Ba k'arya nake yiwa Mama ba, in kuma Mamana bata yadda ba zata iya sakawa a bincika zata gane maganar Aliyu gaskiya ce. but yana da kyau Mamana ta yiwa tufkar hanci tun kafin abun yayi nisa, mahaifita tasan in Abba yaji maganar nan babu abinda zai hana bai bashi ita ba. Faruwar hakan kuma daidai yake da Fulani mahaifita matar sarkin Katagum y'ar sarkin Kano jikar sarkin Kano zata zama inlaw d'in gurguwa, baka, kuma y'ar talakawa. At the end ita kuma zata zama matar sarki zata kasance a saman take Mamana, before Asad yayi sharawa da mahaifita sai ya fara da ita tunda itace sirrin sa!. Zata san abubuwa nasa da yawa kafin Mamana ta sani." Yana gama fad'ar hakan ya fita yana cize bakin sa alamun samun nasara dan yasan Mama ta cika tayi fammmm.

#Vote
#Share
#Comments.

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*021.*

           Hankalin Mama in ya kai miliyan ya tashi jikinta har rawa yake sabida tashin hankali ta tashi ta bar wajan da sauri ta nufi ciki hankalin a tashe sosai. Bata tab'a jin abu mai munin abinda Aliyu ya fad'a mata ba gabad'aya ya gigitata ta rud'e jikin ta har rawa yake yi sabida rud'ani. Kallon agogo tayi taga k'arshe sha d'aya na safe ya kusa ta saka takalmi da sauri ta fita zuwa b'angaren y'ay'an nata dan tana so ta tabbatar da abinda akace mata. Gab da zata shiga falon taji sautin muryar Hydar yana cewa, "Deaf in love, ban tab'a amincewa zaka fara soyayya da wata mace ba duba da yanayin ka da yanayin maganar, sai gashi ka fad'a ba tare da ka shiryawa hakan ba, wannan soyayyar taku itace silar accident."

Asad dai baice komai ba Mama jin abinda ta jiyo ta sake firgicewa ta kuma tabbatar Aliyu bai mata k'arya ba abinda ya fad'a gaskiya ne tunda gashi har Hydar ya sani yana kuma kiran soyayyar da silar accident, har zata shiga falon sai kuma ta koma da baya da sauri ta koma b'angaren ta ta shiga cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya ta kira Mum. Buga biyu Mum ta d'auki wayar kafin tayi magana tace, "Sadiya in kina da time ki shigo yanzun nan." Daga can b'angaren Mum tace, "An gama ranki ya dad'e, bani mintina goma zan iso." Mama bata kuma jin me tace ba ta yanke wayar ta cillar kan gado tana zaga d'akin hankalin ta yayi mugun tashi.

        Zagaye take daga nan zuwa nan ta kasa zama abinda bata tab'a tunanin zai faru ba shine yake k'okarin faruwa jinin ta wanda ya fito daga jikin ta shine da son y'ar talaka, jinin talakawa kuma nakasashshiya. Jinin nata ma kuma Asad da ta k'wallafa rai a kansa ace shine yake son y'ar talaka gurguwa mummuna wannan ba k'aramin abun kunya bane a wajan ta. Shigowar Mum ya saka Mama ta juya Mum ta k'araso da sauri tana fad'in, "Ranki ya dad'e lafiya kuwa?."
"Ina fa lafiya; zauna mu tattara" Mama ta fad'a tana zama itama Mum d'in ta zauna.

"Me ya faru?."
"Meye ma bai faru ba Sadiya. Wani abu naji wanda yayi bazanar tarwatsa min zuciya ya jefa ni cikin wani hali wanda ban shirya tsintar kaina a cikin sa ba." Mum tace, "Ranki ya dad'e meye wannan d'in haka?."

Mama tace, "Ace wai jinina wanda na haifa da kaina ne zai so jinin talakawa, y'ar talakawar ma y'ar tallah a titi bak'a kuma gurguwa? Ta yaya hankali na bazai tashi ba?." Mum ta dafe k'irji ciki da firgici tace, "mun shiga uku, gaskiya dole hankalin ki ya tashi domin kuwa wannan babban cin mutunci ne da cin fuska a gare mu duka ba ke kad'ai ba."
"Bari kawai, yanzun nan naji maganar yanzun nan na tabbatar da ita amma zafi nake ji a k'irjina kamar ana tafasa min zuciya."

Mum tace, "Amma waye da wannan d'anyen aikin? Nadai san Aliyu bazai aikata hakan ba sai dai Hydar dan nasan shine zai iya b'allo mana wannan ruwan." Mama tayi murmushin takaici zuciyar ta na sake cika taf da k'una da b'acin rai tace, "Wanne Hydar ana zaune qalau...? inda Hydar ne ai hankali na bazai tashi haka ba. Babbar giwar fa Asad; wanda yake jiran kujerar masarautar nan wai shine yake soyayya da yarinya irin wannan." Gaban Mum yayi mugun fad'uwa jin wanda aka ambata ta dafe k'irji cikin tashin hankalin da ya bayyana akan fuskar ta itama ta zaro idanu tace, "Asad! Mun shiga uku."  Mama ta girgiza kai bata ce komai ba Mum tace, "Kuma kin tabbatar da maganar? In kika duba yanayin sa ranki ya dad'e sai naga kamar ba zai saurari irin su ba, Anya maganar nan daga majiya mai tushe take?."

         "Da Aliyu ya fad'a min ban amince sosai ba amma da naje na riska suna magana da abokin sirrin sa Hydar a sannan na tabbatar da Aliyu baiyi min k'arya ba. Sadiya jinina tafasa yake yi bazan lamunci wannan lamarin ba gabad'aya." Mum tace, "ni kaina jinin nawa tafasa yake ranki ya dad'e balle ke. Amma fa abinda mamaki anya kuwa ba asiri tayi masa ba? In ba asiri ba a yadda kika lissafo ta meye abin so a wajan ta har da yarima mai jiran gado guda zai d'aga kai ya kalle ta?."
"Babban tashin hankalina kenan Sadiya."
"To shi kin ji ta bakin sa?, ina nufin kun tattauna dashi akan lamarin?."
"Bai san ma na sani ba."
"Amma yana da kyau shima a tsawatar masa a kanta tunda yana jin maganar ki."
Chapter 44 · 0% Book details