← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 55

Sashe 29

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gashi kin cillar da katin maganin balle na fita naje wajan mai chemist d'in nan na baya naji ko za'a samu wasu daga ciki na karb'o miki. Kwalayen ma kin watsar balle naje dasu." Ita dai bata ce komai ba sai juya kanta da take yi kawai hankalin Umma yak'i kwanciya. Addu'a ta dinga yi mata a k'afar haka suka raba dare sai gabanin biyun dare sannan bacci ya d'auki Rauda sai a lokacin Umma ma ta runtsa.

         Da asuba Umma taso makara Allah ya taimaka ta tashi bayan ta idar da sallah Baba ya shigo take shiga d'akin sa tace, "Malam daman magana nazo muyi." Yace, "to ina jin ki."
"Akan k'afar Rauda ne jiya kusan kwana mukayi babu bacci tana ta kuka tana yi mata ciwo rashin shan maganin da bata yi ba kwana biyu,  shine nace zamu shiga gidan radio ko muje gidan sarki tunda yana taimakawa mu nemi taimakon kud'in maganin."
Baba yace, "gwara ma gidan sarkin yana taimakawa sosai da zarar maganar taje gaban sa, gidan radio sai aita yad'awa amma kaji shiru wani lokacin. zan tambaya anjima naji yana gari sai aje in sha Allah kuma zai taimaka."

"Allah ya sa" Umma ta furta jikin ta a sanyaye ta juya ta fita. Baba yana ganin ta fita ya k'arasa wajan ajiyar kud'in sa ya tsohuwar riga duk ta yage baza ka tab'a d'auka akwai kud'i a cikin ta ba ya fiddo da kud'in yana kalla, murmushi yayi yace, "da zan iya da an siyi maganin amma bazan iya cire kud'i masu yawa akan magani kawai ba gwara a fita neman taimakon shima riba ce" ya fad'a yana tattare kud'in ya mayar dasu ma'ajiyar su ya fito daga d'akin.

         Da gari yayi haske Rauda ta tashi babu laifi taji dad'in k'afar ta yi wanka ta karya tana zaune a kan farar kujerar da take zama sabida sauk'in tashi tsaye.
"Sallamu alaikum wai ana sallama da Rauda a waje." Yaro k'arami ya fad'a daga soron gidan.

Umma ta d'ago labule ta fito tana fad'in, "Sallama da Rauda kuma? In ji waye?."
"In ji Bala mai pharmacy" ya bata amsa yana kallon Umma. Umma tace, "to jeka kace gata nan." Yaron ya Juya ya fita Rauda ta kalli Umma tace, "Umma naje nayi masa me?."
"Jeki Rauda bamu sani ba ko hak'ura yayi ya kawo miki maganin."
"Ni dai Umma bazan je ba babu cin fuskar da bai min ba jiya."
"To ni bara na je" Umma ta fad'a tana niyar juyawa ta shiga d'aki ta d'auko mayafi.

      Mik'ewa Rauda tayi tace, "Zanje" ta fad'a tana d'aukar sandinan ta tana tafiya a hankali har ta fita soron gidan ta tarar dashi a tsaye da leda a hannun sa. Yana ganin ta yayi murmushi yace, "Rauda sannu, ya k'arfin jikin?."
"Da sauk'i, lafiya kake nema na?."
"Lafiya lau. Maganin na kawo miki nazo kuma na shaida miki duk bashin da yake kan ki an biya an kuma siya miki maganin da zaki ta sha har ki warke, dan haka daga wannan ya k'are azo a karb'a a waje na."

Kallon sa take tana kallon maganin da yake mik'o mata a leda kafin tace, "An siya min? Kuma an biya min bashi?, waye wanda ya siya har ya biya min bashi?." Bala ya gyara tsayuwa yace, "to wanda ya siya d'in aiko min akayi ba shi yazo da kansa ba, amma dai an siya miki."

"Waye wannan wanda zai siya min magani?" Ta fad'a a bayyane fuskar ta d'auke da zallar mamaki.

*Nima kaina abin ya bani mamaki waye ya siyawa Rauda magani kuma?.*⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️

*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*014.*

A sanyaye ta shiga gida hannun ta rik'e da leda ta zauna a inda ta saba zama Umma ta kalle ta tace, "Lafiya yake neman ki?." Ledar hannun ta ta nuna mata kana tace, "Wai cewa yayi nayi hak'uri da abinda ya faru jiya ga maganin wani ya siya min kuma ya biya bashin baya ya kuma bada kud'in wanda zan karb'a nan gaba."  Da mamaki Umma ta rik'e baki tace, "ikon Allah! Waye kuma ya biya?."

"Ban sani ba Umma, na tambaye shi yace shima turo wani aka yi amma wanda ya siya d'in bai zo da kansa ba."
"Wanne d'an albarkan ne da wannan aikin?."
"Nima kaina ya kulle Umma."
Umma ta nisa kafin tace, "to wama zai miki haka in ba Anas ba? Shi kad'ai ne saurayin da yake zuwa wajan ki yanzu shine zai shiga lamarin ki, Jikina yana bani shine ya siya miki."

Rauda tace, "Amma kuma Umma Anas baya garin nan tun ranar da muka had'u had'uwar k'arshe ya cewa Baba zaiyi tafiya ban kuma ganin sa ba, bai ma san halin da nake ciki ba a yanzu." Umma tace, "Ke kamar ba y'ar zamani ba Rauda? Kin manta yanzu waya tana isar da ko wanne irin sak'o a kuma duk inda kake a duniya?."
"Haka ne Umma, amma ina tantama gaskiya."
"To in ba shi ba waye Rauda?."
"Babu kowa" ta fad'a a sanyaye Umma tace, "to kin gani, amma Allah ya yi masa albarka ya raba shi da iyayen sa lafiya."

Rauda ta murmusa har cikin zuciyar ta take jin farin ciki tace, "Amin Umma Karon farko kenan a rayuwar ta da naji ya burge ni" ta fad'a farin ciki na shiga zuciyar ta sosai. Umma tace, "kin ga bara na kawo miki ruwa ki sha maganin nan jiya kin sha wahala" ta fad'a tana mik'ewa ta kawo mata ruwa a kofi ta sha maganin ta shafa na shafawa ta ajjiye ragowar.

Inna da take d'aki taji komai ta fito fuskar ba yabo babu fallasa ta wuce su bata ce komai ba daman Umma tasan baza ta ce ba dan idan magana ce akan Anas k'arara zata nuna miki tana bak'in ciki da ba Rahma yake so ba. Baba ne ya shigo a gigice fuskar sa taf fara'ar da basu tab'a ganin irin ta ba yana fad'in, "mutanen gidan nan kuna ina! Kuzo kuji abin arzuk'i da farin ciki" ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Umma tace, "Malam lafiya?."
"Bari kedai, ai babar ki ta iya haihuwa da ta haifo ki na aura kika haifo min Rauda. Bawan Allah shigo mana" ya fad'a yana kallon k'ofa.

Mutumin ya shigo sanye da k'ananu kaya hannun sa rik'e da leda ya durk'usa har k'asa ya gaishe su kafin yace, "An turo ni akan na kawowa Baba keke napep guda biyu, sannan ance na bawa mahaifiyar Rauda wannan kud'in" ya fad'a yana d'auko kud'in daga leda. Da hanzari Baba ya kaiwa kud'in cafka mutumin ya hana shi ya kalle shi yace, "Ita aka ce na bawa Baba." 

Yak'e Baba yayi yace, "Daman zan mik'a mata ne ai."
Mutumin ya k'arasa wajan Umma  ya ajjiye kud'in a gaban ta yace, "sannan yace a gaida wacce bata da lafiya shima baya jin dad'i ne da ya zarar ya samu lafiya zai baro inda yake yazo in sha Allah. Gashi yace a bata" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a rufe a takarda ya sake ajjiyewa Umma.

"Sannan akwai kayan abinci da yace a tawo dasu gasu can za'a shigo dasu yanzu." Umma da ta saki baki tana kallon mutumin tace, "bawan Allah waye ya turo ka da wad'an nan abubuwan haka?."
Kafin yayi magana Baba yace, "Anas mana, da shi mukayi maganar zai siya min abin hawan da zan dinga samun kud'i dashi, gashi kuma ya cika alqawari." Umma ta jinjina kai tana kallon mutumin tace, "Amma hidimar tayi yawa bai kamata mu karb'i abin hannun sa ba tunda babu wata magana mai k'arfi tsakanin sa da Rauda, gaskiya a mayar masa."

Baba yace, "ai na riga na ba shi auren ta, ko bana raye shine mijin Rauda tun ba yau ba na mallaka masa ita" ya fad'a hakora a bud'e dan kar ma a mayar da kud'in. Mutumin ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "Za'a shigo da kayan yanzu" ya fad'a yana fita jim kad'an aka fara shigo da kayan abinci babu abinda babu harda yankakkun kaji da d'anyen nama. Bayan an gama shigowa da su yace, "To Baba zan wuce ni." Umma tace, "Bawan Allah da gaske Anas d'in ne ya turo ka?." Zaiyi magana Baba yace, "Kina da matsala Binta, in ba shi ba waye zai aiko mana da wannan abin arzuk'in? Shine an fad'a miki sai faman maimaita magana d'aya kike yi."

Umma tayi Jimm sai tace, "mun gode bawan Allah kayi magana godiya dan Allah. bamu da bakin gode masa sai dai muce Allah ya biya masa dukkan buk'atun sa na alkhairi."
Ya amsa da amin Umma tace, "Tsaya bawan Allah a baka tukwici." Yayi dariya yace, "Haba hajiya ki bar shi na gode sosai. Sannan Baba yace a fad'a maka dan Allah kar kace zaka ja keken da kanka ka bayar a dinga yi maka ana kawo maka kud'i har gida."

Baba yace, "In sha Allah hakan ce zata kasance, Allah ya biya buk'atar duniya da lahira."
"Amin ya Allah. sai an jiman ku" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa.

Rauda dai ta kasa cewa komai bakin ta a bud'e tana kallon abincin da kuma kud'in dake kusa da Umma zuciyar ta na mugun bugawa da sauri-sauri bakin ta ya mutu murus ta rasa wacce irin kalma zata furta. Umma ta kalle ta tace, "Rauda baki ce komai ba bayan duk abinda ya faru ta silar ki ne." Kamar kuma an mata allura a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tace, "Umma na kasa magana ne gabad'aya ban san me zance ba."
"Haka zaki ce kuwa Rauda domin duk abinda aka bamu ta dalilin kine."
Kafin tayi magana Baba ya shigo fuska washe yana kallon kayan abincin yana fad'in, "yau ko fita kasuwar ma bazan ba a dafa mana kajin nan muci mu karya k'asusuwa."

Umma ta kalle shi bata ce komai ba ya kalli Rauda yace, "Allah ya yi miki albarka Rauda, ke farar haihuwa ce wallahi ko cikin y'ay'ana ke ta daban ce." Inna da take tsaye tace, "Su kuma bak'ak'en haihuwar sai a zubar dasu ace ba'a so" tana fad'a ta shiga d'aki ya bita da kallo baice komai ba ya cigaba da santin kayan abinci.
Chapter 29 · 0% Book details